PAGE 45-46

46 11 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 45&46

_____________________________Tabe baki tayi ta tura kofar ta tace"za kaji da shi".

Sai bayan sallah la'asar Hauwa ta farka,mika tayi har sai da jikin ta ya bada karan kas bakin ta dauke da Addu'a.

Tana bude ido ta hada ido da Mami dake zaune kan darduma tana lazumi.

Murmushi Mami tayi tace"kin tashi daughter".

Murmushi Hauwa tayi tace"eh Mami ina wuni",ta fada tana sauka daga kan gadon,gyara gadon ta fara yi.

Ahh! daughter ki bar shi kije kiyi sallah  zan gyara yanzu.

Girgiza kai Hauwa tayi tace" nama gama Mami",bayi ta shiga ta dauro alwala,bayan ta fito ta hau kan darduman da Mami ta bari ta saka hijab ta tayar da sallah.

Jalal na shiga daki ya hau kan gado ya kwanta ya kulle ido tsawon mintina amman barci ya gagare shi,sai zabga uban murmushi yake kaman an bashi kyautar Makkah.

Wayar shi ya jawo ya saka Bluetooth a kunne ya fara kallan hotunan da yayi mata da videos,yana yi yana magana da murmushi shi kadai kaman wani zautattace,sai daya dau tsawon lokaci a haka kafin barci barawo yayi nasaran sace shi.

Uku da minti arba'in da uku Jameela ta farka daga barci bakin ta dauke da Addu'a,tana bude ido taga Jalal a kwance dan nesa da ita.

Bin shi tayi da kallon mamaki baki bude,"toh mai ya dawo da shi da wuri yau?,ganin shi rungume da waya yasa mamakin ta ya kara ninkuwa",a iya sanin ta da Jalal bai barci da waya balle bluetooth a kunne,anya lafiyan shi kuwaaaa?.

Hannu tasa ta taba goshin shi taji ba zafi,tagumi ta buga tace"ni yasu jikar mutun 4 bangare biyu,anya ba aljanu ya kama Jalal ba kuwa,anyaaaa!".

Rarrafawa tayi a hankali har ta karasa wurin shi,daukan wayar tayi daga jikin shi a hankali dan kar ta tada shi,kunna power button tayi taga wayar ya shiga key,juya wayar ta fara yi kamar mai neman wani abu a jikin shi,gwada bude wayar tayi har sau uku amman ta kasa,miyar da wayar tayi a hankali ta ajiye.

"Ni ko nace hmmmm da Jameela taga hoton nan yau da gidan nan ya kama da wuta".

Sauka tayi daga saman gadon ta duba agogo taga karfe hudu saura minti biyar.

Kallan Jalal tayi taga ko alamun tashi bai yi ba,zagayawa tayi ta bangaran da yake ta bubbuga pillow shi.

Bude idan shi yayi a hankali yace"what happen".

turo baki tayi tace"is time for prayer saura minti kadan a tayar".

Mikewa yayi da sauri ya diro daga kan gadon bakin shi dauke da Addu'an tashi daga barci ya nufi bayi,tsarki yayi ya daura da Alwala,yana fitowa daga bayi yaji an tada sallah,da sauri ya dauki takalmin shi da wayar shi ya fice daga dakin.

Bin shi da kallo Jameela tayi har ya fice daga dakin,tabe baki tayi ta shige bayi.

Bayan ta idar da sallah tayi azkar sannan ta mike ta linke darduman da hijabin ta ajiye,fita tayi ta nufi kitchen dan ta daura girkin dare.

Bayan an idar da sallah Jalal ya dawo,jin motsin mutun a kitchen yasa shi nufar kitchen yana tafiya a hankali kaman baza taka kasa ba.

Tura kofar kitchen din yayi ya shiga da sallama.

Juyowa Hauwa tayi ta kalle shi ta hade rai sannan ta amsa sallamar ciki-ciki.

Murmushi Jalal yayi yace"sannu da aiki".

Waiwayowa Hauwa tayi tana kallan shi da alamun mamaki ba tare da ta amsa ba.

Murmushi Jalal ya kuma yi yace"dan Allah ki dan hada min coffee".

Kallan shi tayi da alamun mamaki a zuciyar ta tace"dan Allah,dan Allah fahh!,Jalal ne ke hada mutun da Allah"ikon Allah baya karewa,su Jalal anyi hankali masha Allah.

Hada rai tayi kamar bata ji shi ba.

"Maimaita abinda yace yayi".

"Hada rai tayi ta dalla mai harara ta turo baki".

Murmushi yayi ya nade hannun rigan shi ya dau tukunya ya dauriye ya saka ruwa ya daura a gas ya kunna.

Bin shi da kallo Hauwa tayi tana mamakin shi,"toh kodai ba shi bane,anya Jalal ba rashin lafiya ya same shi ba".

Bayan ruwan ya tafasa ya hada coffee kofi biyu,bayan ya gama hada coffee ya daura shi kan try,miyar da tukunyar yayi ya ajiye.

Wani dan karamin plate ya dauka ya saka cup daya a ciki yace"ga na ki ya fada tare da ajiyewa a gefen ta".

Bin shi da kallon mamaki Hauwa tayi ta kasa magana.

Juyawa yayi ya fice daga kitchen din hannun shi rike da dan plate dauke da cup din coffee a ciki.

Bin shi da kallo tayi har ya fice daga kitchen din.

Jikin ta ne yayi sanyi sossai tana mamakin sauyin da taga tare da shi.

Jingina tayi da cupboard tana kallon kofar kitchen din.

Sossai jikin ta yayi sanyi da yanda Jalal yayi behaving.

Juyawa tayi ta cigaba da aikin ta jikin ta a sanyaye.

Bayan Jalal ya gama shan Coffee ya dawo ya ajiye cup din,daukan liquid soap yayi ya hada ruwan wanke-wanke ya wanke cup din sannan ya tattara kwanonin da Hauwa ta bata ya fara wanke su.

Barin abinda take tayi ta tsaya kallan shi tsawon mintina.

Juyowa yayi ya kashe mata ido daya yace"ya dai yarinyar Mami".

Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba,sossai yanda ya kira sunan ya bata dariya.

Murmushi tayi ta juyar da kanta gefe tace"hmmmmm!".

A tare suka karasa aikin,suna yi suna hira,shi ya fara janta da hira,tun tana shiru ta kyale shi har ta fara amsawa daga nan ta saki jiki ta biye mai su ka sha hira har da dariya.

In ka gansu baza ka taba cewa cat and rat din Mami bane.................................

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now