PAGE 73-74

43 12 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻

              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 73&74

_____________________________Bayan sallah Ia'asar su Mami suka shirya zuwa Asibiti.

Zaune Jameela take a parlor ta harde kafa daya kan daya tana cin chingum hannun ta rike da waya,tana zaune Mamma da Mami suka fice daga parlor.

Sossai Mamma ta kufula da ko in kulan da Jameela tai tayi,da kyar Mami ta lallashe ta,har suka isa asibiti Mamma bata yi magana ba.

Ko da suka isa Jalal bai farka ba,haka suka karaci zaman su suka tafi gida bayan sallah isha'i.

Sai da Jalal yayi kwana uku a Asibiti kafin Jameela ta sani.

Ko da wasa Mamma bata bari ta je Asibitin nan ba,sossai ran Mamma ya baci har tana ikirarin sai ya sake ta idan ya farfado,da kyar Mami ta taushi zuciyar ta har ta hakura.

     *****BAYAN SATI DAYA*****

Zaune Mami take a kan rubber chair ta zuba uban tagumi idan ta kuri a akan Jalal,sossai Mami ta rame kamar wata mai fama da ciwo.

Duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun ta yi taga uku da minti hamsin da biyar na rana,tashi Mami tayi bakin ta dauke da bismillah ta nufi bayi,alwala ta dauro ta dawo ta shinfida darduma ta tada sallah,bayan ta idar ta yi Addu'oin ta ta tashi ta linke darduman ta koma kan kujera ta zauna,dai-dai nan Mamma ta shigo hannun ta rike da basket.

Ajiyewa ta yi tace"Shalele har yanzu dan gida na bai tashi ba".

Girgiza kai Mami tayi idan ta cike da ruwan hawaye tace"Mamma har yanzu bai farka ba,ina tsoron na rasa shiiiiii!,ban San na rasa shi kaman yanda na rasa Abban shi"ta karasa maganar ta hawaye na zuba daga idan ta.

Rungume ta Mamma ta yi tana bubbuga bayan ta tana lallashin ta idan ta cike da hawaye,da kyar  Mamma ta samu tayi shiru.

Zaune su ke duk sun yi jugum-jugum ba Mai magana a cikin su.

Gyara zama Mamma ta yi tana kallan Jalal da kyau,salati Mamma ta yi tace"Shalele Jalal ya motsa",I da sauri Mami ta Mike Mamma ta rufa mata baya,iko tana Isa taji ya yi magana amman ba ta tantance abin da yace ba sabida muryar shi yayi kasa sossai.

Rike mishi hannu Mami ta yi ta fashe da kuka,da sauri Mamma ta fice daga dakin ta nufi kiran doctor,rufa mata baya yayi suka nufi dakin.

Duba shi yayi ya ga komai lafiya Lau amman ruwan da aka sa mai Bai kare ba,wani allura ya hada ya yi Mai sabida yayi barci.

Kallan Mami dake ta kuka yayi yace"yi hakuri  Hajiya insha Allah zai warke kar ki damu,an kusa cimma abin da ake so saura kadan,nan da kwana hudu zuwa biyar za'a sallame ku I jikin yayi kyau".

Share hawayen ta Mami tayi tace"toh shikenan Dr Allah ya sa".

Murmushi yayi yace"Ameen Ameeen Hajiya ki kwantar da hankalin ki"...............................

Comment
Vote
   &
Share

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now