🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
BOOK 2 IS COMING SOON,IS PAID BOOK,FOR EARLY PAYMENT IS 300 LATE PAYMENT 500 COMPLETE NOVEL 1000.
TAKEN NA DABAN NE SAI WANDA YA KARANTA ZAI IYA BADA LABARI.
KU NAIMI NAKU,KARKU BARI A BARKU A BAYA"MATSALAR GIDAN MIJI (UWAR MIJI CE SILA) BOOK 2.
BOOK 1:CHAPTER 111-112
__________________________Tun da Hauwa taji an daura auren ta birkice,da kyar aka samu aka shawo kanta da taimakon Addu'a,bayan ta farfado Maman Fauzan ta taushe ta sannan tace"kin sanar da Mama?".
Girgiza Kai Hauwa tayi hawaye na zuba daga idan ta tace"bana san abinda zai tashi hankalin ta,ita kadai ta rage min a duniya",ta fada tare da fashewa da kuka.
Goge hawayen dake fuskar ta Maman Fauzan tayi tana fadin"ba abinda nake nufi ba Kennan,ina nufin ki sanar da ita mijin ki ya kara aure dan karta ji a gari,kinga idan hakan ta kasance babu dadi,ko yaya ne ki gaya mata amman ta hanyar da zaki kwantar mata da hankali ba ki tayar ba".
Girgiza kai Hauwa tayi alamun ta gamsu da abinda take fada,chan kuma tace"miko min wayar tawa na kira ta",ta karasa maganar ta wasu zafafan hawaye na kwaranya daga kwalwar idan ta.
Dan dariya Maman Fauzan tayi tace"haba ke kuwaaaaa!,so kike ki daurawa Mamar mu hawan jini kisa zuciyar ta ta buga,ke da nace miki za'a gaya mata ta yanda ba zata tashi hankalin ta ba shine kike fadin na miko miki waya kina kuka da hawaye shabe-shabe,kawai kice min asirin da kike boyewa kike son tonawa yau",ta fada tana murmushi ta kuma fadin"ki kwantar da hankalin ki Hauwa'u,wannan daga hankalin da kike ba mafita bane,kin fini sanin halin da kike ciki a gidan mijin ki,mai zai sa ki kunsawa kanki damuwa babu gaira babu dalili".….......
Murmushi Hauwa tayi ta katse mata hanzari da fadin"baza ki gane ba Anty,na san ina tsaka mai wiya a gidan mijina amman hakan ba zai hana ni kishin mijina ba,na san Allah ya halatta karin aure,hakan yasa bazan iya jayayya da hukuncin Allah ba,abinda ke damuna shine yanda ya wofintar da ni ya fita batu na,ko kallon banza bai hada mu balle maganar arziki,ni ba auren bane ke taba min rai,chanjawar da yayi ne rana tsaka ke taba min zuciya",ta karasa maganar ta tare da ajiyar zuciya hawayen dake makale a idan ta ya zubo.
"Anty bazan miki karya ba,ina masifar son mijina duk da abinda yake min,ban san wani irin so nake mishi ba,na san yana bata min amman hakan bai rage ko digo daga son da nake mishi ba,ban san mainene mafita ba,ji nake kaman a kullum son shi kara linkuwa yake a zuciya ta,ji nake kamar sai da na shiga wannan rikicin na gane girman son da nake mishiii"............... ta karasa maganar ta tana fashewa da kuka mai taba zuciyar duk wani mai imani.
Rungume ta Maman Fauzan tayi tana taya ta kuka,sun dau tsawon lokaci suna kuka kafin ta fara lallashin ta da ban baki tare da dabaru iri-iri da za tayi anfani da su wurin tafiyar da rayuwar auren ta.
Sossai ko kalaman ta yayi tasiri a zuciya da kwakwalwar ta wanda hakan ya samar da murmushin da anfi wata ba'a gan shi ba a fuskar ta.
Ganin kalaman ta yayi tasiri yasa ta kara bijiro da wasu tayi anfani da su ta wanke ta tsaf ta rage mata damuwar da take ciki,nan ta fara bata labarin tatsuniya,tuni Hauwa ta biye mata harda babbakar dariya.
Da ta tabbatar ta dan samu natsuwa sai tasa ta kira Mama ta gaya mata, faduwar gaba mai tsanani ne ya riske Mama,Kai tsaye tace"lafiyar ki kalau kuwaaaa?,ya naji muryar ki haka?",dariya Hauwa tayi tace"lafiya ta kalau Mama,mura nake fama da shi shiyasa inaga kika ji muryar haka,ya gida da Antyna,ina gaida ta kuma nayi kewar ku sossaiiiii".
Ba tare da Mama ta amsa ba tace"kin tabbatar lafiya lau kike kuwa?,karin auren da yayi bai zame miki damuwa ba?,nasan halin ki fa da zurfin cikin tsiya,dan Allah karki sa damuwa a ranki kin jiiii!ku kadai gare ni,bana san na rasa ko daya daga cikin ku,na fisan na tafi na bar".............
Katse ta Hauwa tayi tana kokarin danne kukan dake cinta tace"haba Mama taaaa!,ya kike fadin haka,ni babu komi a raina,ban sa komi a zuciya ta ba,jina nake fesss!kamar anmin albishir da kyautar makkah sunkutukum,damuwar ki ce kawai zai iya sani a wani hali,sabida haka ina san ki kwantar da hankalin ki Mamana,insha Allah ina cikin farin ciki,kawai ki rinka min Addu'a kamar yanda kika saba.
Murmushi Mama tayi tace"toh shikenan Kuluwa Allah ya tsare min ke, insha Allah zan aiko yayar ki wurin ki".
Toh shikenan Mama Allah ya anfana ya kara tsawon rai Ameeen,nagode sossai,bari na barki haka.
"Toh ki dai kula,banda wasa da azkar da karatun Al-Qur'ani".
Ya dan naki,shima ki rinka tofe shi da Addu'a safe da yamma.
"Lafiyan shi lau,ana yi Mama sai dai a kara kaimi",da haka suka yi sallama.
Iska mai zafi ta furzar bayan ta gama wayar tace"Allah ya taimake ni bata gano komi ba",toh kin gani ko,da yanzu kin nuna mata kina cikin damuwa da sai ta fiki shiga cikin ta.
Girgiza Kai Hauwa ta yi tace"haka ne Anty,tabbas naji kashi sittin cikin dari na damuwar da nake ciki ya kau,ina godiya sossai da kulawar ki a gare ni Anty,Allah ya bar zumunci ya bar mu tare".
A tare suka amsa da Ameen tare da rungumar juna.
Ana gabda kiran sallan magrib Maman Fauzan ta raka Hauwa har gida hannun ta rike da kula,hira suka dan taba kafin ta yi haramar tafiya.
Hauwa ta mike da niyyar rakata ta yi saurin dakatar da ita da fadin"ina zaki,zauna abin ki na hutarshe ki,kin dai ji abinda na gaya miki dai kohhhh!,in kuma akwai abinda ya shige miki duhu sai ki sanar da ni,a kwana lafiya",ta fada tare da ficewa daga dakin.
Tana fita Hauwa ta mike ta murza makulli.
Da misalin karfe tara da minti goma yan kawo amarya suka iso,sai shewa suke suna guda da bakaken maganganu.
Duk abinda suke Hauwa na jin su,ko da wasa bata yi gigin mikewa ba balle suyi tunanin fitowar ta,kara jan bargo tayi ta rufe su har kai tana karanto Adduo'in naiman tsari bayan ta kure gudun fankar dakin,da taimakon Allah barci mai nauyi yayi gaba da ita.
Ba ita ta farka ba sai bakwai na safe,da sauri ta mike tana karanto Addu'ar tashi daga barci,bayi ta shiga da sauri ta wanke bakin ta da fuskar ta sannan ta fice da sauri ta nufi kitchen,cikin minti talatin ta gama hada musu break dai-dai cikin su,bayan ta gama ta hada komai a tray ta ajiye a gefe ta gyara wurin,bayan ta gama ta dauki tray ta yi gaba abin ta,tana gabda shiga daki taji Sani yace"Ina namu abincin yake?".
Wata uwar harara ta wurga mai ba tare da ta amsa ba ta shige daki da sauri ta murza makulli ganin ya biyo ta.
Ajiyar zuciya mai karfi ta sauke tace"Allah ya taimake ni yau,in ba haka ba da na yabawa aya zakin ta".
Bayan sun kammala cin abinci ta tattara kwanonin gefe,tana san maida su kitchen amman tana tsoron gamon ta da shi........................................
COMMENT
VOTE
SHAREBY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Исторические романы"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...