PAGE 1-2

176 18 1
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
               (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

INA MIKA GAISUWA TA MUSAMMAN GA DUKKAN MEMBERS DIN E. O. W,INA ALFAHARI DAKU. SAI YARAN ELEZABETH.

                  ***BOOK ONE***
                 *** FREE BOOK***

Ban rubuta littafin nan dan cin fuska ba ko kuma wani abu,duk wacce taga labarin nan yayi kamanceceniya da nata toh tayi hakuri,a rashin sani ne.

Ina godiya ga masoya na a duk inda suke.

BOOK 1: CHAPTER 1&2

________________________Hauwa'uuuu!,"Na'am Mama,cewar Hauwa'u dake shiri a daki",baza kiyi sauri ki fito ba lokaci na tafiya,ko so kike ki makara,daga farawa sai ki fara da latti,"fitowa tayi tana gyaran zaman hijabin ta tace na gama Mama".

Kwance habar zanin ta Mama tayi ta ciro dari biyu ta mika mata tace Allah ya kiyaye hanya,ki kula fahh! ban da kula samari,"da toh Mamana ta amsa ta fara tafiya",har ta kai bakin kofa taji Mama na fadin kiyi Addu'a kafin ki fita,"toh Mama,Addu'ar tayi ta fice daga gidan".

Tana fita ba jimawa ta samu mai adaidaita sahu ta shiga,cikin yan mintina da basu wuce sha biyar ba ta isa kofar gidan,tana sauka taba mai napep kudin shi ya bata chanji.

Babban gida ne na gani na fada kuma bene,dutse ta dauka tayi knocking gate din da shi,bayan kaman minti biyu mai gadin ya bude gate,"gaida shi Hauwa'u tayi da ladabi da biyayyah",lfy kalau,ykk,"Alhmd Baba,bayanin kanta ta mai",ohhhh! kece sabuwar mai aikin,"ehhh! nice Baba",matsa mata yayi yace shigo daga ciki,ga wuri ki zauna bari na musu magana,"toh Baba nagode".

Main parlor Gidan ya nufa ya danna door bell,ba jimawa mai aiki ta bude,"Baba ina wuni ya aikin",lfy lau diya ta ya naki aikin,fatan komi lafiya,dan Allah kiyiwa Hajiya sallama kice mata ga mai aikin ta karaso,"toh Baba,ban minti biyu",ba jimawa ta dawo tace Baba ta shigo",zo kuluwa,"tashi tayi ta karaso tana murmushi,dan taji dadin yanda Baba ya karbe ta",yauwa ki shiga ciki Allah bada sa'a,"Ameen-Ameen Baba,ina godiya da karamci",nuna mata kan kujera mai aikin tayi tace ga wuri ki zauna,Hajiya na nan saukowa,"Nagode sossai yar uwa".

Bayan kaman minti Ashirin Hajiya ta sauko,"tun kafin ta karaso cikin parlor Hauwa'u ta duka har kasa ta gaida ta",amsawa tayi ta zauna kan kujera tana mata sannu da zuwa,bayanin abubuwan da zata dinga yi a gidan tayi,sannan tace zan dinga biyan ki dubu hamsin duk wata idan yayi miki.

Godiya sossai Hauwa'u tayi tace"wlh Hajiya yayi nagode,Allah yasa musu Albarka",da Ameen-Ameen Hajiya ta amsa tace zaki fara aikin yau ne ko sai gobe,"zan fara yau idan babu damuwa",toh shikenan babu damuwa,kiran dayar mai aikin ta mai suna Zulai tayi ta bata umurnin nuna wa Hauwa'u duk wani kusurwar gidan".

A ranar ta fara aiki bayan an gama zaga gidan da ita. 
Aikin ta a gidan shine girkin safe,rana,dare,da gyaran dakin Hajiya dana danta,ita kuma dayar mai aikin a gidan take Zama,ita ke musu wanke-wanke,shara,mopping, goge-goge,saka tularan wuta a parlor,da sauran su.

A kwana a tashi babu wiya yanzu Hauwa'u tayi wata biyar da fara aiki,kullun in tazo sai ta ci abinci,ko da ace ta ci a gida,kuma bata tafiya gida sai da Abinci,wannan umurnin Hajiya juwairiyyah ne,sam bata barin ma'aikatan ta da yunwa,barin ma Hauwa'u,dan jin yarinyar take a ranta kaman yar data haifa,Hajiya Juwairiyyah kenan,mai kirki da sanin darajar mutane,talaka da mai kudi duk daya ta dauke su,bata da girman kai, gata faran-faran da ita,baka taba cewa tana da kudi.

Da misalin karfe shida da minti biyar '6:05' Hauwa'u ta fito daga gidan Hajiya Juwairiyyah,da yake layin ba'a samun abun hawa sai ka taka ka fita daga layin.

Tsaye take a bakin titi tana jiran abun hawa amman ko alamun su bata gani ba,gashi garin yayi baki sai chida ake,Allah-Allah take ta sami abun hawa ta karasa gida kafin ruwan nan ya sauka,dan idan ya sauka kam ba'a san ranar gamawan shi ba,tana nan tsaye wani mota yazo ya wuce,har ya wuce sai yayi reverse ya dawo,yayi parking a gaban ta,saukar da glass yayi yace malama dan Allah idan babu damuwa ki shigo na ajiye ki,dan naga alamun tun dazu kike tsaye a nan,"shiru Hauwa'u tayi ta kalli sama taga garin sai kara baki yake,gashi ko alamun abun hawa babu,kuma babu wurin buya idan an fara ruwa,ko kafin ta koma gidan Hajiya bayan an fara ruwan tasan taci na jaki,girgiza mishi kai tayi a hankali ganin babu option",bude mata wurin mai zaman banza yayi yace ta shiga,"zagayo wa tayi ta zauna zuciyar ta sai bugun tara-tara take",murmushi yayi yaja motar suka bar layin,"gaya mishi Address din gidan su tayi",har kofar gidan ya kaita ya sauke ta,"godiya sossai Hauwa'u ta mai ta juya ta shiga cikin gida",sai data shiga cikin gidan kafin yaja motor ya bar kofar gidan.

Tana shiga cikin daki aka kece da ruwa,"hamdala Hauwa'u tayi tace wai Mama ba karamin dadi naji ba da ruwan nan bai same ni a hanya ba,ajiye cooler dake hannun ta tayi ta zare hijabin jikin ta ta zauna kan kujeran dake parlor su tace washhh! Mamana na gaji sossai",murmushi Mama tayi tace na saka miki ruwan zafi a wuta,bari ruwan ya dan lafa sai kije ki watsa kohhh!,toh! Mamana bari nayi sallah,ta fada tana mikewa tsaye,"daukar butar dake bayan kofa tayi tace Mama ina yaya Asiya take"tana dakin ku,bai jima data fita ba,ina ga ruwan nan ne ya hana ta dawowa.

Bayan ta idar da sallah ta kwanta ta aza kan ta akan cinyar Mama tana bata labarin yanda su kayi da Hajiya,Murmushi Mama tayi har ranta taji dadi,tace iko mun gode da Abincin,Allah ya saka mata ya kare ta daga idan makiya ya bata abin da take naima,"da Ameeen Ameeen Hauwa'u ta amsa tace kin ga yanzu ba sai kin dinga girkin dare ba,kuma dole na fita da wuri Mama tunda har karin safe zan nayi,dan ma Allah yasa gidan ba nisa i da na raina kaina",dai-dai nan Asiya ta shigo dakin da gudu kaman an jeho ta..............................

Yawan comment da kuma yanda readers suka karbe shi shi zai determining yawan tsawon page da kuma posting a kan lokaci.

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now