PAGE 35-36

54 11 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 35&36

__________________________Tana shiga kitchen ta fara aikin ta da sauri sabida lokaci ya tafi.

Daura tukunya tayi a gas ta zuba ruwa ta kulle,tana kunna gas din taji ance"keh! village girl mai ya hana ki zuwa kwana biyu?".

Sossai Hauwa ta razana dan ba taji alamun tafiya ba muryar shi kawai taji,dakewa tayi tayi kaman ba taji shi ba ta cigaba da abinda take.

"Keh! ba dake nake ba,ina miki magana kin min shiru".

Dan juyowa tayi kadan tace"ni banga keh a nan wurin ba,dan Allah in ka ganta kace ina naiman ta".

Bin bayan ta da kallo yayi baki bude yace"keh ni sa'ar ki  ne da har zan miki magana ki dubi tsabar ido na ki gaya min nonsense".

"Shiru Hauwa tayi kaman ba taji shi ba amman harga Allah gaban ta bugun tara-tara yake".

"Shiga kitchen din yayi a zuciye ya janyota".

Juyowa tayi a razane zata kwala ihu ya rufe mata baki yasa hannun shi ya zagaye kugunta ya jawo ta jikin shi.

Zaro ido tayi tasa hannu biyu tana tura shi tare da dukan girjin shi amman yaki sakin ta.

Hade rai yayi yace"Ubanwa kika yiwa rashin kunya?".

Turo baki tayi tace"Ubanka ne",ta fada tana murguda mai baki.

Hannu yasa ya murda bakin da karfi har sai da Hauwa ta dan yi kara.

Yana sakin bakin tasa hannu biyu ta rufe shi sabida tsabar zafin da bakin ke mata.

"Gobe ma ki kara min rashin kunya ki gani sai na cire miki baki"

"Shiru Hauwa tayi ba tace komi ba".

"Oya yanzu ki bani hakuri".

Turo baki tayi tace"toh mai nama dazan baka hakuri".

"Dan murmushi Jalal yayi sabida yanda ta turo bakin ta mai kyau sossai".za kiyi koko sai na dau mataki.

"Mai nayi ma ni,babu abinda na maka fahhh!",ta karasa maganar a shagwabe.

"Zakiyi ko sai na murguda miki baki".

"Toh toh na yarda zanyi amman sai ka sake ni".ta fada tana ture hannun shi daga kugun ta.

Cire hannun shi yayi daga kugun ta yace"ina sauraran ki".

"Toh ka matsa baya kafin na fada".

"Na matsa baya kuma,kina da abinda kika shirya kenan".

"A'a fah babu abinda na shirya kawai dai kaje baya kadan sai na baka hakuri kaji".ta karasa maganar ta da lallashi.

"Murmushi yayi baice komi ba yaja baya".

"Da baya-baya ta fara tafiya tana kallon shi".

Sai data tabbatar ta jingina da kofar store sannan ta kalle shi tayi fari da ido tace"yauwa maima kace nayi ma?,ta fada tana gyara tsayuwa".

One step yayi,iko tana ganin haka ta bude kofar store ta shige ciki tasa sakata jikin ta na rawa,sai zare ido take kamar wacce tayiwa sarki karya.

"Murmushi yayi har wushiryar shi ya bayyan",juyawa yayi ya fita ya kullo kofar sabida ta tabbatar ya fita.

Abinci kala biyu Hauwa tayi masu saukin cin lokaci sabida time ya tafi,ko data duba agogo hudu da minti arba'in.

Shida da minti sha biyar ta gama shiri ta sallami Mami.

Tana fita wajen gate taga Jalal zaune a kan robber chair.

Ji tayi kamar za tayi fitsari a jiki,da sauri ta juya baya zata shiga cikin gida Jalal ya riko hijabin ta.

Salati Hauwa tayi tace"dan Allah,in kanawa Allah,dan darajar Mami,dan son da kakewa Mami kayi hakuri ka yafe min,wlh yanzu zan baka hakuri,ko da wasa bazan sake maka rashin kunya ba Allah",duk wannan surutun da take bata kalle shi ba tana rungume da gate.

Gintse dariyar dake cin shi yayi yace"ni ban tanbaye ki komi ba,ko kinji nayi miki magana ne,yanzu ki juyo ki kalle ni,kuma kika kuskura kika min musu sai naci miki mutunci".

"Tsit Hauwa tayi ta juyo hannun ta rungume a jikin ta kanta a kasa".

"Wato ke ba kida kunya koh,har ni zaki kallah ki mayarwa magana".

Saurin girgiza kai Hauwa tayi tace"na janye wlh kayi hakuri insha Allahu bazan kara ba".

"Sossai dariya ke cin shi sabida yanda tayi kamar kazar da aka saka cikin ruwan zafi".

"Dan Allah kayi hakuri ka barni na tafi dare nayi pls".

Harara ya dalla mata yace"in naki fah",mai zai faru".

"Girgiza mishi kai tayi alamun bakomi".

Da hannu ya nuna mata alamun ta shiga gaba.

"Ba musu tayi gaba ta juyo taga yana bayanta".

Sai daya rakata har bakin titi ya bari ta sami abun hawa ya biya sannan ya juyo ya dawo gida.

Washe gari tun shida da rabi Hauwa ta iso gidan ko data shigo babu kowa a parlor,kitchen ta nufa ta fara aikin ta kamar kullun,tana cikin girki taji kanshin tularan da ko barci take taji shi zata san mamallakin shi.

Bata koyi gigin juyowa ba sabida kar wani abu ya hada su,dan tabbas yayi mata ba shakka sai ta rama.

"Keh baki iya gaisuwa ba,ko za kice min ba kiji alamun shigowa ta ba".

"Shiru Hauwa tayi kamar bata san da zaman nutun ba".

Takowa yayi a hankali har zuwa inda take yace"yama kike da suna ma?".

"Shiru Hauwa tayi bata tanka mai ba".

Karasowa kusa da ita yayi a fusace zai jawo ta yaji an turo kofa,da sauri ya sauke hannun shi kasa yana kame-kame yace"ki tabbatar kin gama girki da wuri dan zan fita aiki".yana gama magana ta juyo yaga matar shi ce,kara hada rai yayi sabida karma tayi tunanin wani abu ya bi gefen ta ya fice.

"Keh meh ya hada ki da mijina?"

Juyowa Hauwa tayi tayi mata wani mugun kallo tace"abinda ya hada ki da shi shi ya hada ni da shi".

A harzuke Jameela ta shigo kitchen din tace"wlh karya kike,ko boka kike bi wlh baza ki taba samun Jalal ba,Jalal nawa ne ni kadai,duk wata mace data kuskura ta rabe shi sunan ta gawa".

Wuka Hauwa ta dauka tace"kika kuskura kika karaso nan sai na burma miki wukar nan,in yaso sai ki tafi ki barmu mu shana",ta fada tana kashe mata ido daya.

Jameela na ganin wuka bata ko kara minti biyu ba ta fice daga kitchen din tana fadin kinyi karya ki auri Jalal,wlh ba kalan ki bane,ke ina da yakinin Jalal bazai tab son ki ba,sabida haka ki daina batawa kanki lokaci yar matsiyata.

Murmushi Hauwa tayi tace"kanki ake ji"..................................

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now