PAGE 77-78

45 10 0
                                    

🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU 💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚

BAN YARDA A SAUYA MIN LITTAFI TA KO WANI FUSKA BA.

WATTPAD: Aishamaaruf1
AREWABOOKS: gimbiyaayshu2503
TWITTER: Gimbiya Ayshu
TIKTOK:gimbiyaayshu2503

BOOK 1: CHAPTER 77&78

__________________________Tunda Jalal ya fice daga dakin Mami ya shige na shi bai fito ba sai da aka Kira la'asar,bayan an idar da sallah ya dawo ya shige daki abin shi ko abinci ya ki ci,tun tea da ya sha da safe ne kwai a cikin shi.

Mami na ta jiran saukowar shi bayan ya dawo sallah amman shiru,ta dai san Jalal bai jure yunwa hakan yasa bata takura wurin sashi dole ya ci ba,da dai Mami taga abin ba na karewa bane ta mike ta hada mai abinci da tea mai kauri ta daura a kan tray ta nufi dakin shi.

A kwance ta same shi yayi ruf da ciki idan shi a kulle kaman mai barci.

Ajiye tray Mami tayi ta zauna a bakin gado dai-dai saitin kan shi,shafa kan shi Mami tayi tace"ka bude idan ka na san ba barci kake ba,tashi ka ci abinci,na san ko na tanbayi damuwar ka ba fadamin za kayi ba amman dai ka ci abinci sai kaji dadin tunanin da kyau"ta fada tare da jan kumatun shi.

Murmushin daya bayyanar da fararan hakoran shi yayi ya mike ya jingina da bango gadon.

Tashi Mami tayi ta shiga bayi ta wanke hannu ta zo ta fara bashi tuwon a baki.

Dai-dai nan Jameela ta shigo hannun ta rike da gyale dayan hannun kuma rike da takalmi,sai wani taunar cingum take kamar wata tsohuwar yar tasha.

Dauke kai daga Jalal har Mami suka yi a tare kamar hadin baki.

Gaida Mami tayi Mami ta amsa ba tare da ta kalle ta ba.

"Sannu da jiki ya karfin jikin?".

"Ko kallan ta Jalal bai yi ba balle tayi tunanin zata samu amsa".

Sai da Mami ta tabbatar ya ci dayawa kafin ta bashi tea ya sha rabin cup yace"ya koshi".

Bayan sati daya da dawowar shi gida ya fara zuwa Aiki,idan Jalal ya fita tun safe ba shi ke dawowa ba sai magariba ko kuna bayan sallan isha'i,sossai wannan saban dabi'ar tashi ke damun Mami,sam Jalal bai iya zaman waje ba,amman ta kula yanzu abin da ya fi kauna kenan gantali,zuba mishi ido kawai tayi dan taga kaman ya dan rage tunanin da yake,a tunanin ta fitar da yake ne ya jawo hakan,dalilin da ya sa ta yin shiru kenan ta zuba mai ido.

A yanzu Hauwa na da wata biyu da sati uku a gidan miji.

Zaune take a kan kujera ta mike kafa da tray mai dan girma a kan cinyar ta wanda yake shake da kayan ciye-ciye kala-kala,in kaga kayan nan sai ka ji tsoro,amman haka Hauwa ta take shi tsaf,tana gama ci tayi gyatsa ta ajiye tray a kasa ta gyara zaman pillow ta jingina tana sauke ajiyar zuciya kaman wacce ta yi gudun kilometer dari.

Mamakin yanda take rizgan abinci kwana biyun nan take,ta tabbata idan wani yace za tayi irin wannan cin toh ba shakkah sai ta karyata shi,sai gashi kai duniya gaskiya da alamun tanbaya ko dai wata chuta ce ta kama ni,ko kuma tsusan ciki ke kwashe min abinci,gaskiya da sake Asibiti zani a duba ni abin yayi yawa sai kace wata runbu haba,dai-dai nan mijin ta ya shigo,kokarin mikewa take amman ta kasa,dariya yayi yace"koma abin ki na hutarshe ki na san halin kika yi".

Dariya Hauwa tayi ta rufe fuskarta da hannun ta tace"kai bby,nima abin na damu na wlh ko zamu je asibiti ne",ta fada tare da yin marmar da ido.

Dariya Sani yayi yace"toh yaushe za muje?".

Kokarin mikewa take tace"wlh ni kam ko a yanzu ma a shirye nake".

Dariya Sani ya kwashe da shi har da kwantawa a kan kushin yace"kin ga yanda kika koma kuwaaaaa!,kin yi wani himm kaman mutun uku aka hada",ya fada tare da rufe bakin shi yana dariya.

Bin kanta da kallo tayi tana tattaba jikin ta,a fili tace"mutun uku fahhhh!,uku fahhhh!dagowa tayi ta kalle shi ta kalli kan ta".

"ke dai wasa nake miki baki yi wani kiban kirki ba,bari na dauko miki hijabin ki".

Da toh kawai ta amsa fuskar ta ba walwala.

Bayan su je asibiti suka samu ganin likita Wanda yayi specialize akan mata.

Tun kafin ya duba ta ya gano bakin zaran.

Tarban su yayi da fara'a ya nuna musu kujera suka zauna.

Godiya Sani ya mai ya mika mai hannu suka yi musabaha,tun kafin yayi magana Dr yace"sunana Dr ishaq ina sauraran ku waye ba lafiya"ya fada fuskar shi dauke da murmushi.

Murmushi Sani yayi yace"ummnn Dr dama madam ce kwana biyun nan ban gane mata ba,ba ta da aiki sai ci,ga kasala,ga barci kaman".............

Murmushi kawai Dr yayi ya mika mata wani container yace"gashi ki yi fitsari a nan".

Amsa tayi ba musu ta shiga bayi,bayan kaman minti biyu ta fito tace"na gama Dr".

Danna wani bell yayi bayan minti daya wata nurse ta shigo ta risina tace"gani Dr".

Yauwa Nurse Habiba ki kai client din nan Lab a gwada min jinin ta da fitsarin ta,idan result ya fito sai ki kawo min.

Hakan ko aka yi bayan an dibi jinin ta ta koma dakin Dr.

Bayan minti goma sha biyar Nurse Habiba ta dawo hannun ta rike da paper a nade ta mikawa Dr ta wuce.

Warware Takardar yayi ya karan ta content din dake ciki yace..........................

Comment
Vote
   &
Share

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now