🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
BOOK 1:CHAPTER 103-104
____________________________Da kyar ta iya tashi tabar inda take zaune bayan awowin data shafe tana zaune tana karanta wasikar jaki.
Da safe duk sammakon ta sai da Sani ya rigata,murmushin da ya fi kuka ciwo tayi ta nufi dakin ta,Alwala tayi ta fara gabatar da sallar raka'atanul figir,bayan ta idar ta zauna tana Azkar kafin a tayar da sallar Asuba.
Kallo daya zaka yiwa fuskar ta ka gane tana da damuwa,har wani dan rama tayi a tsakanin yan kwanakin.
Tana gabda kammalawa aka tayar,a gurguje ta kammala tayi nata sallar,bayan ta kammala tayi karatun Al-Qur'ani na tsawon minti goma sha biyar,ajiye komai tayi a mazaunin su sannan ta nufi kitchen ta fara hada musu karin kumallo da abinda Ameen zai kai school.
Cikin minti talatin ta kammala komai tare da gyara wurin,a gurguje ta gyara parlor ta nufi daki ta tashi Ameen ta shirya shi yaci abinci suka bar gidan.
Zaune Mama take a tsakar gida ta rafka uban tagumi,haka kawai a yan kwanakin nan take yawan tunanin Hauwa kuma tayi mafarkin ta har sau biyu wanda mafarkin yake nuni da cewa tana cikin mawiyacin hali,ta kira ta har sau uku amman amsar daya ce"lafiya lau Mama Alhamdulillah".
Mama tayi kokarin yarda da kalaman ta amman abin ya citura,data zauna sai ta fado mata a rai,hakan yasa Mama kin yarda da kalaman ta sai dai ta dau alkawari taya ta da Addu'ar koma mai ke damun ta Allah ya yaye mata.
Tsanye Jameela take da doguwar rigar kanti a parlor tana koyawa Affan Assignment Jalal ya shigo,da gudu Affan ya mike ya rungume baban shi yana murna,Assignment din da ba'a karasa ba kenan.
*****BAYAN WATA DAYA*****
Rayuwa ta juyewa Hauwa,sam yanda take tunanin abin zai zo mata da sauki ba haka bane,abin sai kara tsanani yake.
Zaune Ameen yake a parlor yana cin taliyar daya ji manja,duk ya bata tiles din da farin rigar dake jikin shi.
A fusace Sani ya shigo gidan yana ta huci kaman wani zaki.
Bin shi da kallo Hauwa tayi tana salati,dan tasan ta kade daga ita har ganyan ta,wannan fushin daya shigo da shi tasan a kanta zai huce.
Bata gama zancen zuci ba taji ihun Ameen,a dari da saba'in ta shiga dakin,tana shiga ta iske yana dukan Ameen kaman wani sa'an shi,wani irin kukan kura tayi taja wiyar rigar shi ta baya,saurin sakin Ameen yayi ya fada kan hannun shi,juyowa yayi a fusace ya dauke ta da mari hagu da dama sannan ya hankada ta gefe,nan ya fara dukar ta kaman Allah ya aiko shi,sai daya gaji dan kan shi kafin ya barta a yashe ya shige daki.
Hawaye kawai ke ta kwarara ta gefen idan ta,nishin Ameen data ji ne yasa ta mikewa ba tare data shirya ba,da rarrafe ta isa wurin shi ta tallabo shi.
Wani irin kara Ameen ya saki da ta rike hannun daman shi.
Saurin sakin hannun tayi zuciyar ta na dukan tara-tara.
Kukan daya kuma fashewa da shi ne yasa ta maida hankalin ta a kan hannun data kula shi ke mai zafi,gani tayi hannun ya dan kumbura,idan ta na tsiyayar da ruwan hawaye ta dauke shi tana dingishi ta shiga dakin ta,ruwan wanka mai zafi ta hada ta mai wanka sannan ta ba shi magani,nan danan barci yayi awon gaba da shi.
Da kuka Ameen ya tashi sakamakon ciwon da hannun shi ke mishi,Hauwa na duba hannun taga ya kumbura yayi suntum sai nunfashi hannun yake,ba shiri ta dauke shi suka shiga gidan Maman Fauzan.
Salati Maman Fauzan tayi tace"garin ya haka ya faru".
Hmmm ke dai bari yana wasa ya fada kan hannun,abinka da ties.
Cikin hanzari Maman Fauzan ta shirya suka fice daga gidan.
Bayan Sati daya suka dawo aka kwace hannun kuma Alhamdulillah yayi kyau.
Yanzu ko kadan dukar ta da Sani yake baya damun ta domin ta saba,a sati bai fi a cire kwana biyu ba,kullun cikin duka take,ya maida ta kamar wata gangar sa da yake kima a duk lokacin da yaso.
Hauwa ta sallamawa farin ciki ta zubawa satautar Allah ido.
Washe gari sati Sani bai fita aiki da wuri ba har goma,kaman abin arziki yaci abinci kuma ya mata magana har da dan guntun hira kamar ba shi ba,suna cikin hira yace ta miko mishi ruwa,da murnar ta ta mike tana murmushi,tana dabda isa kusa da shi tsantsi ya jata ruwan ya bare a kan Sani.
A fusace ya mike yana fadin"ke mahaukaciyar wace gari ce,wannan wani kalar dabbanci ne".
Murya na rawa ta budi baki da niyyar ba shi hakuri ya nushi bakin ta,nan da nan jini ya balle ya bata har da farin yadin dake jikin shi.
Rintse ido yayi ya dunkule hannu yana huci, bata ankara ba taji saukar mari,kamin ta gama tantancewa ta kuma jin sukar wani,haka yai ta kifa mata mari har ya gaji dan kan shi,fuskar nan ya kumbura yayi jaaa! abinka da farin fata.
Daki ya shige ya chanja Kaya sannan ya fice,a kofar gida yaci karo da Maman Fauzan,ko ci kan ki bai ce mata ba ya fice daga gidan.
Bin shi da kallo tayi fuskar ta kunshe da mamaki.
Sallama tayi amman shiru ba'a amsa ba,hakan yasa ta shiga parlor kai tsaye.
Ganin babu kowa yasa ta nufar daya daga cikin kujerar dan ta zauna,jinin data gani ne yasa ta tokarewa a tsaye da alamun mamaki.
Dai-dai nan Hauwa ta dawo fuskar ta lullube da laiman ruwa,murmushin da bai kai zuci ba tayi tana fadin"lale marhaban Anty na,kece tafe banda labari,ga guri ki zau"......
Jinin data gani ne yasa ta yin shiru,murya na rawa ta fara kame-kame,murmushi Maman Fauzan tayi tace"mai ya Sami fuskar ki da bakin ki?,yatsun meh nake gani haka a fuskar ki?,jinin nan kuma na menene?".
Dariyar karfin hali Hauwa tayi tace"babu komai fa Anty babu abinda ya faru,ni babu komi a fuska ta kuma baki na inaga zazzabi ne ke son kamani".
Dariyar rainin hankali Maman Fauzan tayi tace"ki gama karairayin da za kiyi sai kizo ki gaya min gaskiyar zance".ta fada tare fa kishingida tace idan kin shirya sai ki fara bani labarin ainayin abinda ya faru.
Lubna ce zaune a gaban wani bakin mutun sanye da jan kaya fuskar shi da farin zane yace"meh matsalar ki bil'adama?,mai kike sooooo!?,mai za'a mikiiiiii!?",ya fada da karaji.
Baki na rawa tace"boka kwana biyu naga Sani baya kula ni kamar da,ban san mai nayi mai ba,da idan nace abu jiki na rawa zai yi,amman yanzu sai ya ja aji zai yi".
Dariyar yan iska boka yayi yace"kinyi babban kuskure bil'adama,nace karki bawa kowa labari akan aikin da aka miki amman baki ji ba,ke kika rage karfin aikin da kanki".
Murya na rawa tace"ayi hakuri dan All"........
A tsawace yace"kehh karki kuskura ki kara kira min wannan sunan".
Saurin girgiza kai Lubna tayi jikin ta na rawa.
Ki fadi abinda kike so ayi miki,murya a sanyaye tace"boka so nake ya aure ni nan da wata daya".
Wani irin dariya boka yayi yana kifta ido yace"angamaaaaaa!,kisa a ranki nan da wata daya kin zama matar shiiiiiiiiiiii!........... matukar kinyi abinda aka ceeeeee!.........kiyi da kyauuuuuuuu!.......,tashi ki tafi da baya baya",ya fada bayan ya bata maganin da za tayi anfani da shi...................................
COMMENT
VOTE
SHAREBY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Ficción histórica"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...