PAGE 41-42

55 10 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)  

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BOOK 1:CHAPTER 41&42

___________________________Bin shi da kallo Jameela tayi tana mamakin abinda yace.

A fili tace"mai hakan ke nufi,tunanin meh Jalal yayi da har ya yi wannan ihun".

Wani bangare na zuciyar ta yace"kodai tunanin wannan yarinyar yayi".

Da karfi tace"ina baze yiwu ba,mai zai yi da wannan tsaburarran yarinyar mtssww".

Allah ya isa zuciya ta,kina chutar da ni,mai yasa kike min haka,mai yasa kike son hada ni da wannan yarinyar mai kama da Aljanar dare.......bude kofar da Jalal yayi ne yasa ta yin mukus tana zare ido.

Fitowa Jalal yayi daure da bathrobe fari kal-kal.

Hada ido su kayi ya hada rai yace"mai yasa kike kallo na".

Kai tsaye tace"kai da wani ido ka ganni".

Murmushin gefen baki yayi yana shafa kanshi ya nufi drawer.

wandan pj.max ya dauko kalan baki ya saka ba tare da ya saka riga ba ya nufi dressing mirror ya dau tulare yayi wanka da shi,fita yayi daga dakin ya nufi kitchen,Coffee ya hada ya dawo parlor ya zauna ya kunna Tv yana kallan Ball.

Sai wurin sha biyu ya kashe Tv ya nufi dakin su,ko daya shiga dakin bulb a kashe yake alamun tayi barci kenan.

Tabe baki yayi yace"fitinanna",bayi ya shiga ya dauro Alawala.

Jallabiyar shi dake rataye ya dauka ya saka ya shinfida darduma ya fara nafila,sai da yayi raka'a goma sha daya har da shafa'i da wuturi,a raka'an shi na karshe wato wutiri ya ringa surfa Addu'oi,"ni dai banji mai yace ba balle na dauko muku rahoto,sai dai ina fatan Allah ya amsa Adduo'in shi".

Wasa-wasa shakuwa mai karfi ya fara shiga tsakanin Hauwa da Sani,kullum sai yazo wurin ta zance ba fashi,gashi in yazo ya rinka kashe ta da kalamai masu dadi masu narkar mata da zuciya,sossai kalaman shi ke shigar ta har zuciya wanda hakan yasa ta fara fadawa gogin son shi.

A bangaran oga Jalal kuma abu yayi tsamari domin yanzu ya tabbatar wa kanshi cewa ya fada so sabida duk abinda yake ita yake tunani,ko barci yayi sai yayi mafarkin ta.

Zaune Jameela take a parlor ta daura kafa daya kan daya tana latsa waya,sai wani cin chewing gum take tana kas kas kas da shi kamar mutanan chan.

Hauwa dake aiki a kitchen duk karan chewing gum din ya dame ta,tayi tsaki yafi sau ashirin.

Tana cikin aikin ta taji alamun takun sahu,ko kafun mai tafiyar ta karaso tasan wacece sabida sam Mami bata saka takalmi masu kara,kuma ba tama cika saka takalmin ba sai chan ba'a rasa ba.

Gyara tsayuwar ta tayi da kyau ta kara hada fuska dan kar ta kawo mata wargi.

A nan bakin kofa Jameela ta tokare ta saka hannu daya a kugu dayar kuma ta rike kofa da shi tace"keh husband  snatcher".

Ko tari Hauwa bata yiba balle tayi tunanin samun amsa.

Sossai shirun data mata ya bata mata rai hakan yasa cikin jin haushi tace"keh yar iska".

Murmushin takaici Hauwa tayi ta juyo ta jingina da drawer kitchen tace"i inkin ce yar iska kadan kenan kin rage mata karfi da quality,da kamar yar goguwa kika ce ko yar kwararo-kwararo lungu-lungu yauwa da a nan sai na baki amsa amman kam yanzu ni kinga aiki nake ba nida lokaci,in kuma taya ni kikazo yi kuma toh bismillah.

Sossai ran Jameela ya baci,taso ta kuntsa mata bakin ciki ne sai ga shi ita aka kuntsowa.

Shiga kitchen din Jameela tayi dan ta jibgeta iya son rai tunda mai ceton ta bai nan.

Hauwa na ganin haka tayi tsaurin daukar wuka domin shi kadai ne abin da zai cece ta,jikin ta na dan rawa tace"wlh kika kuskura kika matso sai na soka miki wukar nan kin mutu in yaso sai mijin ki ya auro wata,kai kai kai na manta ba sai anje nesa ba gani,kinga kina mutuwa sai a daura da ni,ta fada tana dage mata gira fuskar ta dauke da murmushin mugunta".

Hannu Jameela tasa ta toshe kunnan ta tayi ihu ta nufi Hauwa.

Hauwa na ganin ta nufo ta tace"ohhhh!    wato kina san abin ya tabbata kenan toh bismillah".

Kamewa jameela tayi ta Fashe da kuka sabida tsabar takaici da bakin ciki,tunda take duniya babu wanda ya taba mata irin abubuwan da Hauwa ke mata.

Babu abinda yafi sata takaici da bakin ciki kamar taji tana hada kanta da mijin ta,wannan abin shi yafi komai kona mata rai da sata bakin ciki.

"Murmushin mugunta Hauwa tayi dan ganin taci nasarar dasa tsoro a cikin ziciyar Jameela".

Abinda ke bata dariya da ita shine sam kuka bai bata wahala,abu kadan zata bare baki tana kuka kamar wata karamar yarinya,ga shegen tsoro kamar farar kura.

Fita tayi daga kitchen din sum-sum tana hawaye,abu daya yasa ta kuka wai in ta mutu zata aure mata miji,wasu hawaye masu zafi suka gangaro mata tace"amman Allah ya isa tsakani dake,wlh kin cuce ni,kin zalunce ni,ban yafe ba",wai mijina,mijina fahhh!,Allah ya isa insha Allah ke da shi sai dai kallo amman ba aure ba,mayyah kawai mai son mijin mutane,mtswwwwww..............................

By Gimbiya Ayshi💞💞💞.

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now