PAGE 91-92

38 8 0
                                    

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
              (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚

BOOK 1:CHAPTER 91-92

__________________________Mintina sun shude,ranaku sun shude,watanni sun shude.

An shafe wata uku amman har lokacin Sani bai sami kwakwaran aiki ba,dan abin da yake samu dama ya gagara,rayuwa ta juye musu ta musu daurin has.

Ba karamin tattali da manegi Hauwa tayi ba da har abincin ya kai su wannan lokacin.

Zaune take akan kujera ta rafka uban tagumi tana tunani.

Maman Fauzan tafi minti biyar tana sallama amman shiru,jin ba alamun za'a amsa yasa ta shiga bakin ta dauke da sallama,sakin baki tayi sakamakon ganin ta da tayi zaune a parlor.

Tafi minti uku a tsaye tsabar mamaki,a hankali ta daga kafar ta ta karasa inda take zaune ta dafa ta.

Razana tayi tana gyara daurin dankwalin ta tace"sannu da zuwa harka.........maganar ce ta makale a makoshin ta sakamakon wacce ta gani".

Ahhh Maman Fauzan kece?,shine baki yi sallama ba....

Ajiyar zuciya Maman Fauzan tayi tace"hmmmmm nafi karfin minti goma a gidan nan,nayi sallama a waje har na gode Allah,nafi minti hudu a parlor nan duk baki sani ba,mai ya faru?,mainene matsalar ki?,tunanin me kike haka da har za'a shigo parlor ki baki sani ba?".

Dabas ta zauna a kan kujera ta rike kanta da hannu biyu tana salati a zuciyar ta.

Zama Maman Fauzan tayi kusa da ita ta dafa ta tace"na tabbata kina cikin damuwa,ga alamu nan sun bayyana kan su,dan Allah ki gaya min matsalar ki kar kice a'a".

Murmushi daya fi kuka ciwo Hauwa tayi tace"babu komai wlh,kawai abubuwa da suka faru a baya nake tunowa,amman bancin shi babu komai   insha Allah",ta karasa maganar ta fuskar ta kunshe da murmushin daya bayyanar da dimples din ta.

Girgiza kai kawai Maman Fauzan tayi ba dan ta yarda ba.

Janta da hira Hauwa tayi dan kar ta zargi komai.

Bayan kaman minti ashirin ta mike tace"ni kam bari na koma gida Fauzan ya kusa dawowa makaranta,ina Babana ban gan shi ba?".

Murmushi Hauwa tayi tace"wlh yana daki yana barci abin shi,na San ma ya kusa tashi tunda ya jima yana barci".

Ayyah idan ya tashi a shafa min kan shi.

"Toh insha Allah za'ayi haka".

Har bakin kofa ta raka ta,da zata tafi tace"yi hakuri Maman Fauzan na manta ban tanbaye ki ba,dan Allah taimako nake san kimin".

Da murmushi a fuskar ta tace"Ayyyyahhh i babu haka a tsakanin mu,ke dai kawai ki fadi abin da kike bukata matukar baifi karfina ba zan miki shi".

Iska mai zafi ta furzar daga bakin ta tace"dan Allah kudi nake san ki ara min zan je gida,na ce ya bani amman ya ki wai baza ni ba amman idan ina da kudin toh na tafi sai na dawo,ni kuma ba ni da shi gashi ina san zuwa ganin gida dan na kwana biyu banje ba".

Dan jimmm tayi sannan tace"kamar nawa kike bukata".

Karyar da kai gefe tayi tace"dubu biyar ma kawai ya isa,insha Allah gobe dana dawo zan baki".

Ehhh! toh baza'a rasa ba bari naje na duba,Allah yasa kudin ya kai.

"Ameeeeen ya Allah"

Batafi minti biyar da fita ba ta dawo ta kawo mata kudin.

Bayan Sani ya dawo Hauwa ta sanar mishi da kudurin ta na zuwa gida.

Shiru yayi daga bisani yace"ba nida kudin da zan baki na mota,shikenan kudin dana samu yau kuma na mana chefane da shi".

Murmushi tayi tace"karka damu ka kwantar da hankalin ka ba sai ka bani wani abu ba,na san ba kada shi kuma bazan taba daura maka nauyi da yafi karfin ka ba,ni dai fatana shine Allah ya kawo mana karshen wannan rashi da gaggawa Ameeen".

"Ameeeeen ya Allah,Allah ya tsare ya kaiku lafiya kuma ya dawo da ku lfy Ameeen,in kinje ki gaishe da Mama da Anty Ummi".

"Insha Allahu duk za su ji".

Haka su ka ci gaba da hirar su har zuwa lokacin kwanciya suka nufi makwancin su.

Washe gari da misalin karfe takwas ta bar gida,bayan ta gama aikace-aikacen ta.

A gareji tayiwa su Mama siyayya sossai.

Tafiyar minti Arba'in suka yi kafin suka shigo cikin garin kaduna,adaidaita ta samu ya kaita har kofar gida ta biya shi .

Da sallamar ta ta shiga cikin gidan.

Saurin dagowa Mama tayi dan ta tabbatar da muryar data ji,in ko ba gizo idan ta ke mata ba kaman Kulu take gani a gaban ta,dai-dai nan Ummi ta fito,maganar da take ne ya makale mata tace"wa nake gani haka,anya ba batar hanya kika yi ba,tun muna tsanmanin zuwan ki har mun cire rai".

Murmushi Hauwa tayi ta ajiye laidan hannun ta ta sauke Ameen ta nufi wurin Mama ta rungume ta tace"kiyi hakuri Mamana ba share ku nayivba kuma ban manta ku ba,kuna raina, kullum da ku nake kwana nake tashi".

Uffan Mama bata ce mata ba har ta gama zanchan ta tayi shiru.

Ganin Mama taki kula ta ne ya sata fashewa da kuka tace"kiyi hakuri Mama,ba mantawa nayi daku ba,yanayin halin rayuwa ne amman...................rufe mata baki Mama tayi da hannun ta tace"ya isa ban tanbayi wani abu ba,ya mai gidan naki?,ina fatan komai lafiya babu wata matsala".

Daga mata kai Hauwa tayi tace"babu komai Mama".

Hauwa na sauke shi ya nufi gurin Ummi da gudu ya dane jikin ta yana mata gaurancin su na yara.

Cire hijabin ta tayi ta taya Mama aiki bayan ta gama taci abinci,dama ko kari bata yi ba gashi har goma ta gota.

Wuraran karfe biyu suka gama shirin su na zuwa gidan Mami.

"Laida Mama ta naima ta raba kayan da Hauwa ta kawo ta ce ta kaiwa Mami".

Tafiyar minti Ashirin suka yi sabida chikoson abin hawa.

Danna door bell Ummi tayi,bayan minti biyu Zulai mai aiki ta bude kofar,ware idan ta tayi tace"ahhhhh!yau babbar bakuwa muka yi,aiko kinci sa'a shigowar Hajiya gidan kenan.

Wuri ta nuna musu suka zauna sannan ta nufi kitchen ta hado musu kayan kwalama dana sha,tana ajiye trayn Ameen ya saka hannu,bige hannun Hauwa tayi ya ko bare baki ya hau kuka.

Rama mishi Ummi tayi tace"bana san mugunta wlh ki kiyaye ni,akan yaran nan zan iya ci miki mutunci,dama da aka aje ba ci za'a yi ba,ko dan ya riga ki sa hannu,toh ki kiyaye ni wlh",ta fada tare da daukar laidan cake ta bude ta fara ba shi.

Wlh duk ke kika lalata min yaron nan,kin maida shi wani dan  kwarya-kwaryan kwadayi.

"Hajiya na zuwa",ta fada tare da shigewa kitchen.

Mami bata san ko suwa ke naiman ta ba,sai data sauko tayi ido hudu da Hauwa.

Zaunar da Affan tayi a kan kujera ta ware mata hannun ta.

A kunyace Hauwa ta mike ta nufe ta tana gaishe ta ta fada jikin ta,ba tare da Mami ta amsa ba ta rungume ta tace"i ni fushi nake dake kwana biyu baki kira ni ba kuma idan na kira baya shiga".

Dan Allah Mamina kiyi hakuri halin rayuwa ne amman insha Allah zan gyara.

Gaida Mami Ummi tayi tana kokarin daukar Affan.

"Amsawa Mami tayi tare da tanbayar lafiyar Mama".

Sossai suka sha hira da Mami sannan aka yi hotuna,sam Hauwa bata yarda ta yi hoto ko daya ba,Ameen dai ya sha hoto kala-kala da Affan da uwar gayya Maman yara.

Da zasu tafi Mami ta cika su da goma ta arziki tare da makudan kudi da basu san adadin shi ba.................................

By Gimbiya Ayshu💞💞💞

🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.Where stories live. Discover now