🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
INA MIKA GAISUWA TA GA
MARYUDAH
SHALELE (AMMIN LAYLAH)
LIL SIS
ABDOU MANZO MAIJIDDAH
FAREEY BBY
RASHIDAMDA SAURAN MASOYANA NA FACEBOOK DA WATTPAD.
BOOK 1: CHAPTER 89-90
__________________________Kallan shi take hawaye na zuba daga idan ta,bayan ya gama ci ta bashi ruwa ta wanke mai hannu da soso da sabulu dan kar ya sa hannu a ido,sam baya san tana bashi abinci ya fison yaci da kan shi.
Ruwan wanka ta hada ta mai wanka ta shirya shi ta fesa mai tulare,bayan ta gama ta dauke shi tana mai wasa suka fito waje,kujera ta ja ta zaunar da shi ta mika mishi wayar ta bayan ta kunna mai video Abcd,kitchen ta nufa ta kwaso wanke-wanke,tana cikin yi ta ji an turo kofar gida,da sauri ta dago ta kalli saitin kofar,ganin wacce ta shigo ne ya sata mikewa da sauri ta nufe ta da gudu ta rungume ta fuskar ta dauke da tsantsar farin ciki,sossai taji dadin zuwar yar uwar tata ba kadan ba.
Amin na ganin ta ya daga mata hannu yana wangale baki.
Da sauri Ummi ta nufe shi tana fadin oyoyo sweetheart,daukar shi tayi tana kissing din shi ta ko ina tace"sabida kaima nazo gidan nan my love,da ta Mamar ka ce da ba abinda zai kawo ni".
Dariya Hauwa tayi tace"ke dai fadi gaskiya,kice kawai kinyi missing dina shiyasa kika zo".
"Tabdi ba wani nan,Mama ce ta matsa min lanba,daga dawowa ta jiya ta sani a gaba da zance ki kuma ta ce nazo na gane mata ke,nace tazo muje tare amman taki".
Dariya Hauwa tayi tace"Allah sarki Mamata nayi missing dinta sossai".
Ba wani missing,i da kinyi da kinzo,ni fushi nake ma dake,yaushe rabon da ki je gida,ba kira ba komai,dalilin da yasa Mama ta turo ni kenan wai tana kiran number ki baya shiga.
Ayyyah ba haka bane wlh,baza ki gane ba.
Ba wani bazan gane ba sai dai in baki fada ba.
Shashantar da zanchan Hauwa tayi suka shiga daki,ruwa mai sanyi ta dauko a fridge ta tsiyaya mata a cup,bayan ta gama shan ruwa tace"akwai Kaya a waje fah na manta,ajiye Ameen tayi ta dau chocolate a Jakarta ta bude mai.
Bayan sun gama kwashe kayan abincin suka koma parlor suka bude sabon babin hira,Suna cikin hira Hauwa ta tashi taje ta zuba wake a wuta tasa kanwa,bayan ya nuna ta zuba shikafa,bayan ya nuna ta sauke ta soya mai sannan ta zuba musu a plate daya.
Sauko muci abinci,tun kafin ta rufe baki Ameen ya sauko zai saka hannu,da sauri Ummi ta rike hannun shi.
Bayan sun gama Ummi ta wanke kwanan.
Bayan sallan la'asar Ummi tayi shirin tafiya,har bakin titi Hauwa ta raka ta,bayan ta shiga ciki ta dunkule hannu ta mikawa Hauwa tace"kiyi manage".
Hawaye ne ya taru a idan Hauwa tace"ni fa ya kamata ba baki".
Murmushi Ummi tayi mata tace"kar ki damu,ki kula da kanki da sweetie na",ta fada tare da daga mata hannu,dai-dai nan mai keke ya fara tuki.
Hawayen dake makale a idan ta ne suka gangaro,saurin share su ta yi ta koma gida,duba kudin tayi taga dubu biyar ne cif.
Hannu ta daga sama tana godewa Allah daya rufa musu asiri,uwa Kennan,ta tabbata a cikin abincin gida Mama ta diban mata,Allah nagode maka da ka kawo min dauki.
Duba dayan laidan da aka ce kayan Al-Ameeen ne a ciki tayi,shake yake da kayan ciye-ciye kala-kala,ta tabbata wannan aikin Ummi ne,Ummi ba dai kwadayi ba,ba kalan kayan kwadayin da bata sani ba.
Bayan sallan Magarib Sani ya dawo hannun shi rike da laidan daya yi musu chefane,shinkafa loka daya,wake rabin loka,maggi,gishiri,man gyada da manga da sauran su.......haka ya harhada mata komai kadan kadan ya kawo,dayan laidan kuma gurasa ce da cheese sai sweet da bobo na Ameen.
Da murna Hauwa ta tare shi,sossai ta yaba kayan daya siya tare da mai godiya sossai.
Tausayin ta ya ji ya darsu a ran shi,ya tabbata da fitinanna ya aura daya gane kuran shi,ya Allah ka hore min na kula da iyali na Ameeen.
Bayan ya ci abinci yayi wanka Hauwa ta gaya mai zuwan Ummi da kuma aiken da Mama tayi musu.
Sossai ya nuna farincikin shi sannan ya ce"gobe insha Allah zai siyan mata kati ta kira Mama tayi mata godiya".da haka dai suka cigaba da hirar su.
Yanzu jameela ta fara aiki a company,ita ce accountant na company,tare suke fita da Jalal kuma su dawo tare.
Affan ya fara zuwa makaranta kullun driver ke kai shi ya dawo da shi..............................................
By Gimbiya Ayshu💞💞💞.
YOU ARE READING
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Ficción histórica"Labari ne akan budurwar da take tsananin nuna wa saurayin ta so har ta kai su ga Aure". "Tun kafin suyi Aure bai da karfi sossai,ta kasan ce tana aiki,tana kashe mishi kudi sossai,komi ya tanbaya tana bashi amman banda zubar da mutuncin ta,bata ta...