Bismillahir rahamanir Rahim_________9:45pm
“Ammi! Ammi! Ammi!Muryar yarinya yar shekara 8 da ke kiran mahaifiyarta daga waje har ta karaso ciki.
Ammi da ke parlour zaune saman carpet din parlour ita da Fatima mai shekara 4 ta na tayata homework ta dubai ta tare da tambayarta.
“Siyama lafiya ki ke kwala min kira tin daga waje?
Siyama ta zauna bisa carpet din ta na Hucin gudu ta ce “Abi ya ce mu shirya za mu fita, Ammi a dauko min kaya.”
Ammi ta ce “Ba kayan da za ki chanza.”
Siyama ta mike tare da cewa “Allah ni dai sai na chanza.” Ta wuce ciki.
Fatima da ke kwance saman carpet ta na wasa da pencil Ammi ta ce mata “Oya stand up let continue.”
Ta ce: “A’a sai mun dawo.”
Ammi ta ce: “Ki na so aunty ta duke ki, maza tashi kiyi.”
Kafar ta ta dora daya bisa daya ta ce: “Ammi da mun dawo zanyi.”
Fatima ba ta tashi ba har sai da Ammi ta ce za ta bata sweet sannan ta tashi suka cigaba da assignment.
Siyama dakin su ta shiga ta budai wardrobes din ta ta zubdo kayan ta duka sannan ta dauko olive gown. Ta aje bisa gadon ta sannan ta budai chest of drawer nan ma ta fiddo duka headband da hulunan da ke ciki ta na neman headband din ta ba ta gan shi ba. Ta koma wurin gadon su.
Gado biyu na yare ke jera a dakin kowan ne da side drawer. A dayan gado nan ma wata yarinya ce kwance ta na bacci sai dai ta dara siyama da shekara 5.
Siyama ta fara jijigata ta nace mata ta tashi. Bata ta shi ba har sai da ta ji Abi zai fita da su da sauri ta tashi zaune.
Siyama ta ce “Yaaya ina ki ka aje min headband di na?Qawwama ta ce "Ki du ba." Ta na karasa maganar idanuwanta suka fada kan kayan da siyama ta zubdo ta fara mata fada;
“Siyama wai ke miyasa ba ki abu cikin nitsuwa ji yan da ki ka zubda kayanki dazu na gama gyara dakin.”
Siyama bata damu ba ita dai ta headband din ta ta ke"Ni dai ina headband di na?
Qawwama ta ce: “Ya na bisa kai na zo ki dauka, mtssww.”
Ta mike za ta shiga toilet dan ta wanke fuskar ta Ammi ta shigo. Ta na shigowa qawwama ta ce: “Ammi ni nagaji ko 30 minute ba a yi ba da na gyara dakin nan wannan yarinyar ta zo ta zubar da kayan ta.”
Ammi ta dubi siyama fuskar ta ba yabo ba fallasa jira kawai take a fadi magana ta maida. Ammi ta ce: “Siyam wai miyasa ba ki jin Magana?
Ta ce: “Ammi headband di na fah na ke nema.”
Ammi ta ce: ‘Ba ki iya neman shi cikin nitsuwa ke ko mi sai kin yi na rishin hankali. Maza ki maida kayanki ki gyara dakin.”
Ta dubi qawwama ta ce mata “Za ku fita da Abi ki nemo kaya masu kauri ki sa wa Fatima.”
Qawwama ta amsa mata da toh ta shige toilet.
Ammi ta cewa siyama da ta gyara dakin. Ta wu ce. Ta na fita siyama ta cigaba da neman headband din ba yanda ta iya ta hukura da kayan ta dauko English skirt and blouse ta sa. Ko da qawwama ta fito ta mata Magana ta yi banza ta kyale ta.
Qawwma ta kyale ta ta shirya kanta da Fatima. Ta na gamawa ta dauki wayar ta ta kira Abi.
Abi na majalissa ya ga kiran ta ya daga. Yana dagawa ta ce; “Abi mun shirya.”
Abi ya ce: “I’m coming be ready.”
Ta ce: “We are.”
Ya ce: “Okay I will be there.” Ya yanke kiran ya mike yayiwa abonkan sa sallama ya shiga mota ya koma gida.
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel