M&N perfume:
Black humra
White humra
Her majesty
Dilka mix
Dilka oil
Dilka soap
Kabbasa spray
Kajiji
Sandal wood
Sandal flask
Farce
Kalacha
And mores
Suna kuma koyar da turarukan huta na sudan yamel senegal da sauran sirikam turarukan huta da gyaran jikiContact them 09162382018
Suna zaune suna fira kiran Asim ya shigo wayar ta ta dauki wayar ganin shi ne ta mike ta wuce daki tana amsa kiran. Tana shiga ta ce "Mun ga sako mun godai Allah kara arziki."
Ya ce "Amin ya Allah, kin san ba zan iya kwana cikin fan ba ke da baby na ku kwana a cikin zafi."
Tayi dan murmishi ta ce "Yanzu dai ka ci abinci?
Ya ce "Na ci sai dai ban ko shi ba."
Ta ce "Ay sai dana ma tayin abinci kaki ci, gashi nan yanzu gana jin yunwa."Ya ce "No ba yunwa ba na ke ji ba kawai dai ban koshi ba dan ba girkin ki ba na ci."
Kamar kullun fira suke yi tamkar sarauyi da budurwa dan wani lokacin sai kowa ya kwanta ita take kwanciya.
20 days da zuwan ta gida Asim da Asif su ka kwanta Asibiti rishin lfy ta kwana uku har a ka sallamai su Halimatu ba ta san an kwantar da shi ba kuma ba ta san bai da lfy ba ko da ta tambaye shi sai ya wayin ce mata da lfyr shi lau har sai da ya warke bayan kwana hudu za su je Adamawa shi da Asif ya zo gidan su.
Bayan sun gaisa da Umma, Umma ta shiga daki ita da Asee da Huzaifa ta bar su a nan waje kasancewa yau da akwai hutar nepa.
Yana rike da Qawwama, yatsar shi ta tsakiya ta na cikin hannun Qawwama yana mata wasa ya ce "Gobe fah zamu Adamawa ni da Asif zan raka shi wurin Nur."
Ta ce "Ya yarda ke nan?
Ya girgiza kai ya ce "A’a a cewar sa bai son ta amma hkr zai yi."Ta tambaya "Amma ita na son shi?
Ya ce "Ban san wannan ba shima bai sa ni ba sai dai mun je gobe."Ta ce "Toh Allah kai ku lfy ya maido da ku lfy."
Ya amsa da "Amin" sannan ya ce "Mi kuke bukata ke da baby."
Ta ce "Ba mu bukatar komi sai dawowar ka lfy."
Ya yi dan murmishi ya ce "Zan turo ma ki kudi kafin gobe, kin san ban so a dorawa su baba nauyi, ke ma ina so fah ki dinga cin mai kyau kina shan mai kyau yanda Qawwama zata yi kiba."
Ta dubi Qawwama dake wasa da kafafun ta ta ce "Duk kibar ta a haka so kake ta kara kiba."
Ya ce "Eh mana yanda duk wanda ya ganta ya san ana ba ta kulawa."
Ta ce "Ba ita kai dai ba ni kai na duk wanda ya ganni ya san habibin masoyiya na kulawa da ni..."
Yau da ya dawo daga gidan su Halimatu gidan su ya wuce ba gidan shi ba domin da safe za su tafi adamawa by flight, Abba ya biya mashi kudin zuwa da dawowa shi kuma Asif ya biyawa dan’uwan sa dan ba zai iya zuwa shi kadai ba Asim shi ne kashin bayyan sa.
A daren sai da Asif ya nunawa Umma bai son auren amma ina bakin alqalami ya bushe tinda har uban yarinyar ibrahim Khalil ya yarda mgn ta kare.
Haka ya kwana da takaicin haka tare da qudirin sa yarinyar ta janye.Washe gari da safe suka shirya buba ya kai su airport, tafiyar hour su ka yi kafin jirgin ya sauka a airport, suna fita driver ya zo ya dauke su dan Mummy ta tura driver tin kafin su zo.
Da isar su a ka wuce da su shashen ta a ka aje su a masauki na musanman na baki.
Suna jran fitowar Nur Asim ya tabo shi. Asif ya hadai gabas da yamma. Asim yayi murmishi ya ce "Put on smile, haka ka ke so ta zo ta gan ka sai ka bata tsoro."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel