Tin da ya dawo at around 12:00pm bai fita daga gidan ba, sai bayan yayi sallah magriba ya shirya dan zuwa ganin masoyiyarsa da yake daukin gani.Leda biyu da ke saman mirrow ya dauki karamar ya bar babba sannan ya fito. Hamza ya iske da abokansa suna biga PS, suka gaishe shi ya amsa cikin sauri ya wuce.
Da isar shi gidan su Halimatu yau layin na su babu giccin yaro, ya zaro wayar shi daga aljihun gaban rigar shi yayi dailing number ta.
A cikin gidan Umma na zaune saman sallaya kamar kullun sai Nusaiba da Asee da ke karatu Huzaifah kuma na cin abinci, Halimatu kuma ta na ciki ta na guga.
Her phone’s rang, the chiming of the phone made her pause. Ta aje iron din ta jawo wayar ta, ganin shi ne ke kiranta ran ta ya bata yana kofar gidan su. Ta dau kiran tare da mashi sallama.
Ya amsa. Ta gaishe shi ya amsa, sannan ya ce mata ta fito yana kofar gida. Ta amsa shi da ya bata 5 to 10 minute. Ya amsa mata da toh. Ta aje wayar ta kashe iron din ta fito waje. Ta ce "Umma ga Asim ya zo kuma yau ya ce "Zai shigo gaishe ki.
Umma ta dago ta kalle ta bata bata amsa ba.
Halimtu ta dubi si Asee ta ce "Asee dan Allah ku koma ciki kai ma Huzaifah koma ciki ka ida cin abincin.
Nusaiba ta ce "Mu ina Ruwan mu da shi ba Umma zai gaida ba."
Halimatu ta ce "Da Allah na hada ku, kuma in ya shigo bisa tabarmar ku zai zauna."
Umma da ta yanke wudrin ta ce "Nusaiba ku koma daki bana in ya tafi sai ku dawo."
Huzaifah da ya mike yana cin tuwon sa ya ce "Halima yauma su biyu suka zo?
Halimatu ta ce "Ban san ni ba tambayo da kai."
Huzaifah ya aje kwanan twon ya juya ya nufi hanyar waje ya na tsidai hannunsa, tin da ta ki ba shi amsar tambayar sa zai je ya gani da kansa.
Ta kira shi da ya dagata amma ina ko dagata wa bai yi ba. Yana fita ta dau kwanan tuwon ta maida shi kitchen ta rufe shi ta koma daki ta sa hijab din ta sannan ta yi waje.
Huzaifah kuma na isa wurin Asim ya rintsina ya gaishe shi.
Asim ya amsa shi. Huzaifah ya tambaye shi ina da’uwansa.
Asim yayi murmishi ya ce "Ya na gida."
Huzaifah ya ce "Ka gaishe min shi."Asim ya ce "Zai ji." Sannan ya mika masa ledar hannun sa.
Huzaifah yayi tsaye yana kallon ledar tare da jin tsoran amsa.
Asim ya ce "Amsa bana."
A lokacin Halimatu ta fito ta na mashi sallama. Da sauri huzaifah ya jiyo yana girgiza kan sa, Ya wuce ciki da sauri.
Asim ya bi shi da kallo. Bayan ya wuce ya dubai ta ya ce "Kin kyauta."
Ta mashi alamar tambaya ya ce "Kin hana shi amsa ba na."Ta ce "A'a ni ba ni na hana shi ba."
Ya ce "Toh gashi ki kai mai tinda ke kin ce kin girma da tsaraba.Har ya mika mata kafin ta amsa ya ce "Na ma fasa da kai na zan bashi daman mun yi dake yau zan gaishe da Umma, fatan kin fadi mata."
Ta gyada mashi kai, ta ce "Bismillah." Ta juya ya bita a baya suka shiga ciki.
Yayi sallama Umma ta amsa shi. Suka karaso ya tsugunna ta gefenta tare da saddar da kansa. Ya gaishe ta ta amsa sannan ta mashi ban gajiyar hanya.
Bayan sun gaisa ya aje ledar a wurin ta yana ce wa "Umma ga tsarabar hanya a ba Huzaifah."
Umma ta ce "Har da diwaniya."
Ya ce "Ba komi."Umma ta ce "Huzaifah kam ya godai." Ta kira huzaifah. "
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel