Chapter 42

10 3 0
                                    

Bayan ya raka su ya rufe gidan sannan ya dawo ciki bai ganta a parlourn ba ya wuce daki ya iske ta ta na chanza kaya zuwa na bacci, ya karaso yana ce wa "Habibty mun zama iyaye."

Kalmal "Iyaye" da ya fadi ta boye bacin ranta a kan kin barin ta da yayi ta bi su.

Ta dubi babyn dake kwance saman gado tana bacci ta ce "Mun kara samun farin cikin rayuwa." Ta ida sa rigar baccin.

Ya dora hannun ta saman waist ya ce "Habibty yau kin kara bani farincikin rayuwa kin kara bani dalilin da zan rayu. A yau na kara san ki sama da san da na ke maki."

Ta sa hanun ta bisa fuskar shi ta ce "Ka manta kai ne farin ciki na kuma ta dalilin ka mu ka kara samun farin ciki a rayuwar mu, ka sa na zama uwa kuma muka zama iyaye."

Ya koma wurin babyn ya kwanta ya na kallon ta ya na mirmishi ya tambaye ta "Wa ya ma ta kiran sallah?

Halimatu ta karso ta ce "Na san Asif ya mata."

Ya ce "Da ni da Asif duk daya ne amma yanzu zan kara mata sai mu yi naiming din ta."

Ya karasa mgn ya na daukar ta ya mata kiran sallah a kunnan ta na dama sannan ya kara mata wani a na hagu sannan yace Allah ya raya min ke "Khadija."

Ta dubai shi da mamki ta ce "Khadija, sunnan umma ta??

Ya jinjina mata kai. Ta rungumai shi ta ce "I love you baby I love you qalbina."

Ya kai hannun shi bisa hannun ta yace "I have a gift to you."

Ta dawo gaban shi ta ce "A gitf??

Ya gyada mata kai ya ce "Been a mother, shiyasa na tanada mi ki shi yanda ba za ki taba mantawa da ranar da ki ka zama uwa ba."

Farin ciki shinfidai a zuciyar ta ta ce "Thank you Love."

Ya ce "Yanzu close your eye let me show you the surprised." Ta rufe idon ta.

Ya mike ya wuce wurin akwatin da ya dawo da shi ya daga ya dauko karamin gift box ya dawo saman gadon  ya ce "Open your eyes."

Tana budai idon ta ta ga box a hannun shi ya mika mata ta amsa cike da farin ciki. Farin ciki shinfidai a fuskar ta ta zare zaren sama ta dauki laminated papper da ke dauke da rubutu, ta karanta message din cikin ranta tana ta blushing;

"You have brought so much happiness into our lives. Thanks for giving me a baby gril. I love you."

Daga kasan kuma a kasa;

"What can be more beautiful than seeing my beloved wife bringing a new life from another dimension of life??

Bayan tagama karantawa ta sakan mashi kyawatnce murmishi ta ce "I love you too." Ya mata nuni da ta daga box din.

Ta daga, combo set ne na spa daga ciki akwai karamin box ta dauke shi ta budai shi, a ciki sarka ce da zube. Ta kalle shi sai blushing take ta kasa ce mashi komi farin cikin dake zuciyarta ya kasa barin tayi mgn.

Ya amshi box din ya dauki zoben sannan ya jawo yatsunta yayi kissing ya sa mata zoben sannan ya ce "Ina so zuben nan ta tsaya a hannun ki har abada, a duk lokacin da ki ka kalle ta zaki tuna ranar ko da kina bakin ciki da kin kalle ta za ta saki farin ciki."

Sannan ya dauki karamar Sarkar ya samata a wuya ya ce "Wannan kuma sarkace."

Nan take kwalal farin ciki ta zubo mata. ya ce "Ya kuma ki ke kuka?

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now