Halimatu da ta fuskan ci haka ta tambaye shi lfy kwana biyu ya dai na mata zancen yan gidan su haka na Umma.
Murmishi yayi mai ciwo ya ce "Sun ce ba su bukatata ba Ruwan su dani, kin san da ciwon na ke kwana na ke tashi kowa ya guje ni."
Ta dawo kusa da shi ta zauna ta dora kan shi saman kirjin ta ta ce "Ba wanda ya guje ka, muna son ka."
Ya ce "Ke kadai ki ke so na yanzu Umma ta dawo bayan su."
Gaban ta yayi mumunar dagawa jin Umma ta dawo rakiyar su Aunty Zulaiha abin da ta ke ji ma tsoro ke nan, fatan ta kar su ce za su rabata da shi dan a yanzu san da ta kewa mijin na ta ba ta iya misulta shi da komi. Tana cikin tunanin ya ce "Habibty ba zaki bar niba ko? Ba za ki guje ni ba?
Ta shafa sumar kan shi ta na ce wa "Ba zan gujeka ba kullun ina tare da kai, ina son ka kuma ina kaunar ka."
Shi kuma yace "Umma ba ta so na ta na fushi da ni na bata hkr ta kiya, duk ta dalin Aunty zulaiha da Safna a yanzu ba wanda na tsana irin su."
Haliamatu ta ce "Kar ka ce haka zata daina fushi da kai ka kara bata hkr."
Yayi shiru ya kara rungumaita yana sauke damuwar shi. Ita ma shiru tayi tana shafa sumar kanshi a hankali.
Bayan wasu dakika yace mata sanyi yake ji ta lullubai shi.
Ta amsa shi da "Toh" sanna ta kara da "Ko zaka koma daki?
Ya ce "A’a bar ni a nan."
Ta sauke kan shi a hankali ta maida shi saman kujera ta mike ta shiga daki ta dauko bedsheet, ta dawo ta zauna ta dora kan shi bisa cinyarta sannan ta lulubai shi.
Jin kadan jikin sa ya fara daukar zafi. Ta ce mashi bari ta dauko mashi magani.
Ya ce "A’a ki barshi zan samu sauki ni dai ki kara min abin rufa sanyi na ke ji sosai."
Ganin yanda jikin sa ya ke kara daukar zafi duk ta bi ta rikice. Bayan ta sauke kan shi daga cinyarta ta mike da sauri ta shiga ta kira Asif, gab da zata yanke ya daga ta mashi sallama yanayin yan da ya amsa ta san ba lfy ba."
Ta gaishe shi ya amsa. Jin yanayin mgnr shi ta fasa ce mashi Asim bai da lfy dan ko tantama babu shima Asif bai da lfy.
Asif ya tambaye ta fatan lfy?Ta ce "Eh daman sako ne zan baka sai kuma dan uwanka yace a barshi."
Daga haka ta katse kiran. Ta rasa wa zata kira ya zo a kai Asim asibiti.
Ta dauko another bedsheet ta fito ta kara lullubai shi. Zata koma daki ya ambaci sunan ta, ta dawo kusa da shi cikin radadin ciwo duk da har da raki yace "Habibty ban tunanin zan kai anjima ki kula min da kan ki da yar’ta."
Haliamtu da jin haka ta fashe da kuka ta nace wa "In sha Allah ba za ka mutu yanzu ba dan Allah ka jure bari na kira wani ya zo ya kai mu aisbiti."
Ya ce "A'a kar ki kira kowa kar ki basu wahala ni na san bazan rayuba, ciwon zuciyata ya tashi kuma zuciyata ta min nauyi."
Ta ce "Dan Allah ka dai na fadin haka."
Ya ce "Ki kula da kanki da Qawwama."
Ta ce "Dan Allah ka dai na ce wa haka."Ta mike ta wuce daki ta na kuka tana tunanin wa zata kira mai mota wanda zai kai su asibiti daman duk wani daukin ta Asif ne, shima bai lfy.
Tana cikin haka ta tuna da Aunty Salma da sauri ta fara naiman numberta ta yi dailing.
Aunty salma na daga wayar Halimatu ta yi kokarin kamai kukan ta amma ya gagara.
Aunty salam jin halimatu na kuka ta tambaye ta lfy mike faruwa mike damun ki?
Halimatu ta kokarata ta ce "Asim bai da lfy dan Allah ki zo su kai shi asibiti ciwon zuciyar sa ya tashi."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel