Suna cikin jiran halimatu ta haihu kubra ta karaso. Bayan sun gaishe ta ta tambaye su har yanzu bata haihu ba.
Maman sayyid ta ce "Eh Umma sister ta ce tana da doguwar nakuda."
Umma ta ce "Allah sarki Halimatu Allah sauke ki lfy."
Suka amsa da "Amin."
A bangaren Halimatu tin kafin haihuwar ta zo ta sadakas a kan ita mutuwa zata yi su kira mata Umma da Asim tanai mi yafiyar su musanman Umma ita dai ba za ta rayuba mutuwa zata yi haka ta ke abu daya har aka yi magriba kan baby bai fito ba da nakudar ta zo sai ta koma. Har a kay isha’I shiru babu komi.
Jin shiru yayi yawa Asif ya tilasta Dr Nawfal ya zo duk da ba bangaren shi bane hakanan ya zo shi da abokin sa suka duba ta, kamar yanda sisiter Hauwa ta ce bata bukatar Cs zata iya haihuwa da kanta tin da ko bleeding ba ta fara ba doguwar nakuda ce kawai.
Bayan sallah isha’I Umma ta shigo labour room din ta karaso wurin ta.
Halimatu na ganin ta ta fashe da kuka tana ce wa "Umma ki yi hkr amma mutuwa zan yi wlh ba zan iya ba ki yafe min."
Umma ta ce "Haba halima ki jajirce bana da kin haihu duk wata wahala ta kare, ki kara hkr."
Ta na kuka tana ce wa "Ba zan iya ba. ni amin Cs, dan Allah ki ce masu su farka cikin, umma mutuwa zan yi dan Allah ku taimaka min."
Umma ta ce "Toh ki kara hkr bari na je nace wa Dr a shirya tiyatar."
Ta juya za ta fita ta ce "Umma a kira min Asim mu yi bankwana."
Batare da umma ta juyo ba ta amsa mata da "Toh" ta wuce ta bar ciki ba ta kara dawo wa ba.
Da Asif, Maman Sayyid da Umma haka suka tsaya suna jiran halimatu ta haihu.
Umma kuma bata san abin da ke faruwa ba ganin Asif yayi dare bai dawo ba ta tambayi bubu.Bubu yace mata shi ma bai san in da ya je ba.
Ta dauki waya ta kira shi. Gab da zata yanke ya dau kiran.
Yana daukan kiran Umma ta ce "Asif ka san bana son daren nan duk in da ka ke ka dawo."
Asif ya ce "Umma na manta ban gaya maki ba tin dazu muna asibiti mun kawo Amira zata haihu."
Umma ta ce "Shi ne ba ka fada min ba."
Ya ce "Umma Asim ne ya azzalzale ni da na tawo."Umma ta ce "Ta haihu ne?
Ya ce "A’a Umma wai sun ce doguwar nakuda garai ta har yanzu bata haihu ba."Umma ta ce "Allah sauke ta lfy da ka fada min da wuri da na zo na samai ka amma yanzu ba yanda za a yi na fito karfe 12 saura."
Ya ce "Umma ba damuwa umman su ma na nan."
Umma ta ce "Toh shike nan Allah sauke ta lfy."
Ya amsa da Amin. Ya yanke kiran.
Dukakan su kwanan tsaye su kayi tin da suka zo sister hauwa taga bata isa haihuwa ba ta ce masu su koma Asif ya ki yarda haka suka kwana a asibitin bata haihu ba ko da a ka yi asuba ta yi sallah Asuba dan nakudar ta je ta dawo ta ke mata.
Bata haihu ba sai 7:25am ta haifi baby girl.
Sister hauwa ta goge yarinyar sannan ta mikawa halimtu ita ta rungumai yarinyarta ta lumshe ido, tana jin saukar farinciki a ranta mara misultuwa. Daga bisani ta tambayi umman ta.
Sister hauwa ta sa Nurse badiya ta kira Umma.
Nurse din ta fita ta ma su albishir da ta sauka lfy an samu baby girl.
Suka amsa da "Masha Allah Allah raya."
Nurse din ta dubi Umma ta ce "Tana kiranki." Umma ta mike ta bi ta suka shiga.Umma na shiga Halimatu ta fa she da kukan farin ciki ta na ce wa "Umma na haihu na zama uwa nima, umma daman haka ake ji Umma kin yi kokari ni daga wannan na gama ba zan iya Haifa dayawa ba wannan kadai ta ishe ni."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel