Chapter 45

15 3 0
                                    

Washe gari da safe bayan sun tashi dogarai suka kawo masu breakfast su ka ci sai su ka fito dogaran su ka raka su fadar mai martaba.

Da isar su suka zauna a kujerar suna jiran fitowar sarki. Bayan minti 5 zuwa 8 sarki ya fito a na fara masa kirari suka mike har sai da sarkin ya zauna sannan suka zauna.

Bayan an gama masa kirari suka sauka daga kujerar suka gaishe shi ya amsa sannan ya ce da su koma su zauna. Bayan sun zauna.

Mai martaba ya ce "Kun sa kaya daya taya zan iya banbance sirikin nawa.'
Asim ya dan yi murmishi ya ce "Ga shi nan." Ya nuna Asif.

Sarki ya ce "Masha Allah Asif, ay gimbiya Raihana ta na ban lbr ka da yanayin halin ka da nistuwar ka, kuma tayan da ta ke yabo da tarbiyar ka na san hankali na zai kwanta idan yar’ta Nur ta aure ka, ina fatan ba za ka ba mu kunya ba yanda ko wa ke yabon kyawun halayen ka.

Asif yace "In sha Allah."

Sarki yace "Yauwa, daman kafin ka zo mun yi mgn da mahaifin na ku mun fidda ranar da za a sa auran sai muka ce kafin a sa za ka zo ku kara fahimtar juna tin da daman kun san junan ku kuma ya’uwa ne. Toh ina maku fatan alkahairi.

Asim ya amsa da "Amin."
Sarki ya ce "Kuna iya tafiya."
Asim yace "Mun godai."

Suka mike suka wuce, suna fita Asim ya ce "Dude lamarin ka mamaki yake bani, sai ka gama cewa ba ka son aure da an zo wurin manya sai ka chanza mgn."

Asif ya harare shi kafin ya ce "In kai baka jin nauyin idon manya ni ina ji."
Asim yace "Kai ka sani."

Suka wuce part din Mummy zuwa parlourn ta suka jira ta fito su ka gaishe ta sannan ta aika a kira Nur.

Nur da ke kwance a daki mai aiki ta shigo tare da yin sallama.

Nur ta amsa sallamar ba tare da ta dago ta kalle ta ba.

Mai aikin ta rintsuna ta ce "Ranki ya dadai gimbiya na kira.. "

Da hannu ta ma nuni da ta tafi. Mai aiki ta juya ta fita. Ita kuma ta mike ta fita ta wuce parlourn Mummy daga ita sai rigar bacci jikin ta ko hula babu dan bata jima da tashi ba ta dau wayar ta ta fara amfani da ita.

Ta na shigowa ta yi sallama. Asim ya amsa sallamar ta.

Ganin su Asim na parlourn da sauri ta juya ta fita bata tsaya ko ina ba sai dakin ta tana jin haushi shigarta kamar  mahaukaciya ga gashin ta da ya cukukiye.

Ta shigo dakin tana ta karamin hauka sbd takai cin haka.

Bayan fitar ta Mummy ta bi ta da "Allah shirya."

Asim yayi karamin murmishi. Mummy ta aika mai aikin da ce wa Nur in ta shirya ta zo tana kiran ta.

Nai aikin ta juya ta wuce dakin Nur ta yi sallama ta shigo daki. A hassale nur ta ce "Ke mi a ka yi??

Mai aikin ta rintsuna tana bada hkr sannan ta ce "Sarauniya ta ce idan kin shirya tana kiran ki."

Nur ta ce "Na ji wuce ban wuri." Mai aikin ta juya ta  fita.

Nur tayi tsakin takaici duk ya ishe ta da ta tuna yanda Asim ya ganta a daukar ta Asif ne dan Asif ko kallo bata ishe shi ba.
Ta shiga toilet ta yi wanka ta fito ta shirya ta kimtsa kanta da fitowar ta ta sa mai aiki ta hada mata breakfast.
Mufida ta karaso tare da ce wa "Ke na zo kira Mummy na naiman ki.."

Nur ta juya kwayar idonuwan ta ta ce "Su Asif ne fah, ni fah I don’t like him, he is.. in fact I hate him."

Su ka fara tafiya mufida ta ce "Ni a tunani na bai da mtsl."

Nur ta ce "Sis mgn a ke ta aure, my all life."

Su ka yi sallama suka shigo.

Suna shigo wa mummy ta ce "Nur dan kin rai na mutane za ki bar baki suna jiran ki wai ke yaushe za ki yi hankali?
Nur ta karaso ta zauna ta na cewa "Mummy I just wake up when you sent to call me, don’t you see how I came in.'

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now