Da yamma Mummy ta kira Halima ta ce mata ta gayawa Nur komi.
Umma bata ji dadin haka ba ta tambaye ta dalili bayan sun ce ba za su fada mata ba.
Mummy ta fada mata abin da ya faru.
Umma ta ce "Raihana tinda bata san shi kar a takura mata a barta ta auri wanda ta ke so Allah kawo mata miji."Mummy ta ce "A’a Umma kin san tsorona kar mijin da zata aura ya wulakantan ta in yasan ba virgin bace.
Umma ta ce "Ay ba zai sani ba za a ce mashi tayi aure bazawara zai aura kin ga shi ke nan an kara rufe sirin Asif bai yi sex da ita balle ya san ita ba virgin ba ce haka ma wanda zai aure ta a ce mashi bazawara ce kin ga shi ke nan."
Mummy ta ja numfashi ta ce "Halima hankali na ba zai kwanta ba in har ba Asif ta aura ba ba zan taba samun nistuwa ba."
Zan kara shawo kan shi bana so Nur ta sha wahala yanda nake fuskancin qalubalai a nan, kin san nisantar ta da gidan nan shine farin cikin ta hutun ta amma shashar har yanzu ta kasa gane wa.
Umma ta ce "Toh nima zan kara mashi mgn kuma kar ki damu kafin watan ya kare zai maido matar shi."
Asim yayi salma Umma ta amsa sannan ta ce wa Raihana zan kira ki.
Asim ya zauna shi da Qawwama da ke hannun shi sanna ya gaishe da Umma.
Umma ta amsa tana tambayar shi Halimatu.Ya amsa da ta nan lfy.
Ta dubi Qwwama ta ce "Zo mu gaisa."
Asim ya sauke ta kasa yana cewa "Je ki gaisa da Umma."Ta girgiza mashi kai.
Umma ta ce "Zo mu tafi bye bye."
Ta kara girgiza kan ta.Asim ya ce "Je ku tafi bye bye za ta baki sweet."
Umma ta ce "Zo mu gaisa." Qawwama ta koma saman Asim.
Umma ta ce "Na san maganin ki. " Ta mike ta dauko biscuit a saman mudubi wanda mahir ya kawo mata ta dawo ta zauna tana ce mata zo ki amsa. Ta tsaya tana kallen ta,
Asim yace "Je ki amsa na budai maki."
Ya sauke ta. Qawwama ta fara takawa a hankali wadda yanzu kamanin mahaifin nata ya na dada bayyana a fuskarta.Umma ta ce "Zo bana yau kiwar a ke ji nan ay ba bakon ki bane."
Asim ya ce "Bacci ta ta shi ta fara rigima sai na fito da ita."
Umma ta ce "Zo ki amsa."
Qawwama ta karasa wurin ta, Umma ta dauke ta ta dora ta saman cinyar ta tana ce wa "Good girl, Na baki?
Qawwama ta daga mata kai.
Umma ta ce "Ok smile." Qawwama ta mata karamin murmishi. Umma ta mika mata biskuit. Tana amsa ta yi azamar sauka daga kan Umma.Umma ta ce "Ina zaki dawo."
Qawwama ta fara alamaun kuka. Umma ta sauke ta ta ce "Toh je ki mun bata."Asim yace "A’a Umma ba kun bata ba."
Qawwama ta karaso wurin Asim ta hau bisa shi.Umma ta ce "Ka ga yaran nan da wayo."
Asim yayi murmishi kafin yace "Umma naji kamar maganar dawowar Nur ku ke fatan zata dawo?Umma ta ce "Toh Asif din ne ya kaffe ba zai maidata ba ni ban ga dalilin kin yin haka ba."
Ya ce "Umma gaskiya ya maida ta hkr zai yi kuma ki mashi mgn abin da yayi bai kyauta ba."
Umma ta ce "Zan kara mashi mgn."
Ya ce "Umma ba wai shishigi nayi amma da zan shigo sai naji kamar kuna mgnr da Mummy gamaida Nur."
Umma sai da gaban ta ya fadi da sauri ta tambaye shi "A kan mi?
Sai yace "Na ji kuna cewa Nur ba vigin ba ce."
Umma ta ja numfashi kafain ta ce "Ban so ka ji wannan ba rufe min kofar."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel