Chapter 43

9 2 0
                                    

Bayan magriba Asim ya zo da mai hoto A ka mashi shi da ita, Asif ayyan da buba sai kuma yan gidan su Halimatu.

Bayan kowa ya watsai ta mashi mgnr tana so ta koma gida wanka, yayi kamar bai ji taba dan shi bai son ya nisanta da ita kuma in dai ta je wankan nan sai a ce sai tayi arba’in.

Ta ce "Habibi kayi shiru ba ka ce komi ba."

Ya ce "I think we have already talked about it."

Ta ce "Ni kuma na dauka sai anyi suna dan Allah ka barni na je."

Ya ce "Ki yi hkr amma ni tsrain zuwa wankan gida bai rai na."

Ta ce "Yanzu ke nan kullun Umma sai ta zo kuma ka san da nisa tsaknin nan da chan."

Ya ce "Ba damuwa I can afford the transport fee." Ta dai lura bai so sai ta kyale shi.

Bayan kwana biyar Hajiya Halima ta tamabye shi ina Halimatu da Khadija.
Ya ce mata su na gida.

Ta tambaye shi ba gidan su ta je ba
Ya ce "Eh umma."

Umma ran ta ya baci a akan haka ta mashi fada a kan bai kamata ya hana ta zuwa gida wanka ba musanman haihuwar fari mi ta sani dagana jikin ta sai ya saki.

Ya na komawa gida yace wa Halimatu ta shirya kayan ta da na baby gobe da yamma Asif zai so su kai ta gida.

Ba karamin dadi ta ji ba dan har ta cire rai da zuwa gida wanka. Ta mashi godiya.

Ya ce "Ban son godiyar ki tin da zaki tafi ki bar ni, tin da baby ta zo ki ka rage kulawa da ni." Ya dan chanza fuska.

Ta karasa kusa da shi in da yake zaune saman kujera ta zauna ta daga kanshi ta dora bisa kirjin ta ta na sha fa mashi gefen hannun shi ta ce "Ni na isa in dai na kulawa da kai, ay ko ya’ya nawa zan Haifa bazan daina kulawa da shagwababn masoyi na."

Ya dora hannun sa saman breast din ta ya ce "Daman jiya kin min rowar shi in bar wa baby, na bar mata shi da rana da dare sai ta bar min."

Yanda yake mgnr tamkar yaro dan shekara uku.

Tayi dariya ta ce "Shi ke nan yanzu ga ka ga shi. "

Zip din da ke gaban rigar ya zage ya fiddo su. Suna fira ya na wasa da su. Khadija kuma na gudan kujerar tana bacci.

Washe gari da safe tin da ta tashi ta ke farin ciki bayan sun gama breakfast ya wuce kasuwa ita kuma ta shirya masu kaya, tana son ta je gida kuma  ba ta so ta bar shi musanman jiya zuwa yau yanayin sa ya chanza.

Ta kira Umma ta fada mata za su wanka. Umma bata tsaya ta saurare ta ba ta fara mata fada akan sai da ta takura mashi ya kawo ta.

Ta ce "A’a umma shi da kansa ya ce in shirya."

Umma ta ce "Toh Allah sa dagaske ki ke sai kun zo."

Bayan magriba Asif ya zo daukar su, kayan ta a shirye suke ta mika mashi akwatin shi  kuma da ya fito ya ba Asif, Asif ya dauki akwatin ya kai mota shima Asim ya dauki baby shower set ya fita ita kuma ta dauki baby bag da Khadija suka fita.

Bayan an sa kayan a mota Asim ya rufe gidan ya shigo ciki.

Har suka isa bai ce mata komi ba sai fira suke da Asif.

Suna karasa lungun gidan na su. Asif yayi parking. Asim ya ce "Malan sai ka dan bamu wuri."

Asif ya juyo ya kalle shi ya ce "Tin dazu baku yi sallama ba kasan dai sauri nake."

Asim  yace "Toh kar ka fita idon ka ne zai makance." Ya ja tsaki.

Asif yayi karamar dariya ya ce "Ba da ni ba."  Ya budai motar ya fita.

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now