Asif ya koma gida ya fadawa Umman sa abin da ya faru ita ma bata ji dadi ba.
Abba ya aika a ka kirawo shi ya mashi tass a kan abinda yayi.
Asif ya bashi hakuri ya ce ba zai bari a dau hakkin wanda bai da laifi ba bayan shi Asim da kan sa ya tafi ba wanda ya tilasta mashi guduwa kuma ba sace shi ba aka yi.
Bayan ya shiga part din su ya kira wayar Asim bata shiga ba ya tura mashi text din abin da ya faru.
Asim na gani ran shi ya baci miyasa Abba yake son ya tozarta rayuwar sa miyasa bai kaunar sa bai kaunar farin cikin sa.
Wa shegari da safe kafin ta tafi aiki Asim ya kira ta ta ki dauka ta tura mashi message da ya dai na takura mata iyayen shi ba za su taba son ta ba ya hakura da ita.
Ya na ganin message din ya kara kira amma ba ta daga ba shima ya maida mata nashi;
"Wlh ba zan iya hakura da ke ba sai dai in Allah ya kaddara ke din ba tawa bace amma ba zan taba cire tsanmani ba."
Sati uku da tafiyar sa a ka kwantar da halimatu asibiti ba ta da lfy Asif yayi dawainiyar kudin asibiti da magungunar har da kudin cefane da yake basu ba tare da kowa ya sani ba hatta Umma bata san ya na taimakon su ba daga shi sai Asim sai kuma yan gidan su Halimatu.
A ka sallamai ta ranara da aka sallamai ta shi ya maido su gida a motar shi. Suka mashi godiya.
Bayan tafiyar sa nusaiba ke fadawa Umma ay dazu Asif ya kawo masu karamin buhun shinkafa, katan na taliya da macroni da karamar jarkar mai.
Umma ta ji dadin haka ta kira shi ta mashi godiya ya ce ba komi an zama daya ko da ba mu hada zuri’a da ku ba ba mun ki taimakon wanda basu da shi ba.
Umma ta mashi godiya. Bayan malan Yakubu ya dawo Umma ta bashi lbrn abin da Asif yayi shima ya kira shi ya godai mashi Asif ya ce Asim ya kamata ku godaimawa ni dan aike ne.
Malan Yakubu ya ce "Ka san in da yake?
Asif ya ce "Eh amma ba wanda na fada mawa kai ma dan Allah kar ka fadi wa kowa na san in da Asim yake ko Halimatu kar ka fada mata.."Malan Yakubu ya ce "Ba wanda zai fada mawa. Ya kara godai mashi.
Bayan kayan abincin a cikin ledar maganin halimatu ya sa envelop a cikin evelop din dubu 70 ce a ciki. Da wannan kayan abincin da dubu 70 din malan Yakubu ya hada a kayi hidimar bikin musa da na biyu ga mahifiyar halimatu sai nusaiba wadda ta ke iya ga mariganyiya wato tshohuwar matar malan Yakubu.
Yanzu mutun biyar ya rage a gaban sa saifullahi da Haidar suma ya'yan mariganya ce, sai Halimatu, Aseey da kuma Huzaifah.
Haka Asim ya shafe wata hudu ba wanda ya san in da yake sai dan uwansa. Halakar su da halimatu ta na ta kara karbi sai dai ita ta kasa kwanatar da hankalin ta a kan shi.
Lfyl ta ke aikin ta gidan Mummy. Mummy tsanmanin ta halimatu ta hakura da Asim musanman yanda ta tsorata a kan saruta da Mulki.
Nura kuma yana ta so ya turo amma Halimatu ta ki bashi dama.
Ana haka Asim ya tuna da baba lauwali kanen kakan sa wanda yake madobi a washe garin ranar ya shirya ya ta fi madobi ya samu kane kakan na sa bayan sun gaisa ya ce ya kawo masu zuyara.
Lawali ba karamin dadi ya ji ba ganin Asim ya kawo masu ziyara.
Tin da ga ranar da ya zo baba lauwali ya na ta jin dadin zuwan sa.
Bayan kwana uku ya fito ya fadawa baba lauwali abin da ke faruwa.
Baba lauwali bai ji dadin haka baya ce ya kwantar da hankalin shi in dai aure ne anyi an gama.
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel