A fada kuma Umma bata san Halimatu ba a gida ta kwana ba dan fira ta yi fira har a ka fara kiran farko ba su san dare yayi ba, sai bayan sun yi sallah asuba su ka koma anan part din Ummi tayi bacci.
Salma kuma duk ta bi ta damu har sai da gari ya waye sannan zulaiha ta budai gidan.
Salma ta fito duba halimatu ba bu ita babu alamar ta cike da damuwa ta koma ciki tana cewa zulaiha, abinda ki ka yi jiya ba ki kyautaba bayan satar da ki ka dora mata zaki hana ta kwana ciki ko tausayin dan cikin ta ba ki yi ba, yanzu ba ta baranda.
Zulaiha ta ce "And so. Why should I worried, mtsww abeg get out of my sight."
Salma ta ce "Laifi na ne da tin jiya ban gayawa Umma ba."
Rai bace zulaiha ta jawo hannunta ta rike ta ce 'Ki fadawa umma."
Tayi murmishi ta ce "Yi maza ki je ki fada let paly the game, you know me, you know how I move." Ta yarfa hannun Salma.Salma ta Harare ta ta wuce, ta sa masu aikin naima Halimatu a duka part din mata.
A bangaren su Halimatu ba ta tashi ba sai wurin 11, ta falka ta gan ta a saman hanun shi, ta mai da kanta saman kirjin sa ta na mai kallon kyakyawan fuskar mijin ta cike da saukin mijin na ta. Ta na shafa kirjin sa a hankali, ta bace a tunanin sa har ya falka bata sani ba.
Har sai da ya mata mgn "Habibty” ta yanda ya mata mgn da bold voice din sa da muryar bacci. Ta dago ta kalle shi ta ce "How was your night is?
Yayi murmishi ya ce "In ce wani abu."
Ta gyada mashi kai yace "Kar fah ki ji haushi."
Ta ce "Mi zai sa in ji haushin Habibi na."
Ya ce "Kin yi kokari, nace ki zo in koya maki turanci, ban so a raina ki, irin wanna turancin da ki ka min."
Ta bata rai ta daga kanta daga kirjin ta zata mike ya maida ta ya ce "Yanzu fah ki ka ce ba zaki ji haunshin mijin ki ba."
Ta ce "Ay mistake ne kuma kowa na yi."
Ya ce "Eh kowa nayi amma ke kuma baki so a gyara maki gyaran ki."
Ta ce "Naji sai mi."Ya ce "Yanzu ce wa zaki yi how is your night my love hope is sweet."
Ta gatsine fuska kafin ta gyada kanta.
Ya ce "Ko da yake zan zo in daina ko ya maki ni ne ban da ma zuciya nace ki koya min larabci kin kiya nima daga yau ba zan kara maki gyara ba."Ta ce "Naji gwanda ni na iya kai kuma fa na’am da lalala kadai ka sani."
Ya ce "Toh, har da gori shike nan zan baki mamaki zaki zo wuri na ki roki na koya maki both English and Arabic."
Ta katse zance ta turo baki ta na ce mashi "Yunwa na ke ji."
Yayi murmishi ya maida ta kasa yace "Ni kuma yunwar ki nake ji how many days amma ba ki damu ba."
Ta ce "Wa ya ce ma, na fika damuwa, ta jawo shi ta hadai bakin su..
A fada kuwa Salma duk ta damu an duba ko ina ba a ga halimatu ba, ga wayar ta a daki balle a kira a ji ina ta ke.
Ta sa masu aikin suka tambayi fadawan dake gate su ma suka ce basu ganta ba. hankalin ta duk ya tashi.
Umma kuma har yanzu batan san halimatu bata nan ba, dan da ta tashi a part din Ummi tayi wanka ta ci abinci, kayan ta Salma ta kira ta ce ta fiddo mata kaya ta ba masu aiki su kawo mata.
Suna shiryawa suka tafi kai amarya tare da gyara ko sau daya ranta bai bata Halimatu ba ta gida.
Sai daya saura suka karya sannan ya fita ya siyo masu kaya a boutique ya kawo mata ta sa, wa inchan kuma aka sa su a cikin ledar boutique din suka fita. Tsanmanin ta za su je fada sai ta ga sun wuce tasha.
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel