Chapter 60

12 3 1
                                    

A bangaren Asif da ya koma gida bayan ya sauka a parlourn shi ya tafi parlourn Nur, ya iske ta zaune ta na kallo.

Ta mashi sannu da zuwa ya amsa zai wuce ta ce "Nan ke nan zaka kwana da ka fadi da wuri anyi girki da kai."

Ya juyo yana ce wa "Ban gane ba?

Ta ce "Ina nufi you should have told me, ba wai in ga ka dawo ba bana san sha Ruwan tsuntsayen nan, ay na dauka  wurin amarya za ka dan ni nayi mamakin kwananka jiya har yau zaka yi na biyu.

Ya daure fuska tare da ce wa "Ban san shirman banza."
Daga haka ya wuce.

Ita kuma ta bishi da dariya dan Umma ta riga da ta sanar da ita Asif ya saki nihila yanzu damane da zata kwata incin ta ta koyawa Asif san ta."

Duk da bata san shi amma ya zata yi da kaddararta dole ta amshe ta hannu biyu.
Parlourn shi ya koma tare da tuna kayan haushin nihila dan tsakanin jiya da yau ta mashi kira ya kai 50 amma bai daga ko daya daga ciki ba. 

Yana zaune ya ji yunwar cikin sa ta ishe shi ya fito parlorun na ta bata nan ya wuce dakin ta. Ya iske har ta kwanta.

Ya juya ya fita ita kuma ta gan shi.

Kitchen ya nufa ya dafa indomine ya jira har sai da ta dahu sannan ya zuba ya wuce parlourn shi ya ci ya bar plate din a nan ya wuce dakin sa.

Washe gari da safe kafin ta fita ya tashi. Ta shirya zata fita ya dagatar da ita daga taka sannan ya ce ta shiko ciki.

Bata yi kardama ba ta shigo ciki. Ta zauna tana ce wa "Hope ba zaka dau lokaci ba dan zan je wurin aiki."

Ya ce "Dan zaki wurin aiki ba zaki fada min zaki fita ba."

Ta ce "Wait yaushe ka zauna a gidan da zan fadamaka kai fah bako ne, taya zan tada bako yana bacci."

Ya ce "Toh daga yanzu ni mijin ki ne."

Ta dubai shi ta danyi karamar dry tana ce wa "Daman kai miji nane kawai dai baka cika miji ba..  sai ta yi shiru.  Bayan wasu seconds ta mike yace "Ban gama ba koma ki zauna."

Ta zauna ta nace wa "Kayi sauri ina mkr."

Ya ce "Wai ke yaushe bakin ki ya budai har haka?

Ta ce "Please bana san tashin hanakli in baka da mahimmin abin ce wa zan tafi wurin aiki."

Ya ce "In na hana ki fah?
Ta ce "Shi ke nan sai na zauna hutu na ne."

Kallon ta yayi cike da mamaki ya dauka zata ce mashi A’a ko kuma ta fara sa’insa da shi ganin dai ta maida shi sakarai ba ma ta damu ba.

Yace "Daga yau ni ba bako bane mijin ki ne kuma mai gidan nan. Dan haka kafin ki tafi ki min breaksafast haka in dan kin dawo kafin na dawo a aje min lunch da kuma dinner."

Ta ce "Na kwana nawa?
Ya ce "Ban gane na kwana nawa ba."

Ta ce "Eh mana kwana nawa zaka yi kafin ka koma wurin ta yanda in san ranar girki na da na ta."

Ya dan yi shiru kafin  yace "Na sake ta."

Ta sani amma sai ta nuna kamar bata san da haka ba ta ce "Ka sake ta ikon Allah, ni da nake naiman saki ba ka sake niba sai ita."

Ya ce "Eh  ba zan sake ki ba. Na gama mgn kina iya tafiya."

Ta mike ta dau jikar ta ta wuce.

Bayan yayi wanka ya ci abinci ya wuce chan gidan nihla.

Bai yi mamakin ganin ta a gidan ba ya mata kashe di a kan ya bata kwana uku ta tattare komi na ta ta bar mai gida.

Sannan kada wanda ya kira shi biko ko kuma ya bashi hkr ya maida ta. Daga haka ya wuce wurin aiki.

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now