Chapter 52

17 1 0
                                    

Daga haka ya mike ya koma gida ya iske Halimatu har ta yi Shirin kwanciya.

Qawwama kuma tayi bacci. Ya shigo ciki. ya zauna. Ta tambaye shi lfy na ga ran ka ya baci,

Ya ce "Daga wurin Asif na ke.'
Tayi karamar dariya ta ce "Ko da yake kun fi kusa ba zan shiga Tsakani ba."
Ya ce "Zo ki ban shawara."

Ta ce "Rufa min asiri in ba ka shawara a kan dan'uwanka washegari ku hadai kai. A'a ba da niba."

Ya ce "Dan Allah ki zo ki zauna mgnr serious ba ta wasa ba."

Ta zauna kusa da shi tana ce wa "Fadi min mtsl Allah sa na san maganin ta."

Ya ce "Na san ki da kishi kar na fara mgnr ki dauka da zafi. "
Ya ida yana jan kumatun ta.

Ta ce "Ni ka fada min in zan iya taimakawa toh in kuma bazan iya ba sai a san mafita ba ka tsaya kan ja na ba."

Ya ce "Toh fada min da wata igiya na ja ki?

Ta mike ya maida ta yana cewa "Tsaya ki ji bana."

Nima wasa nake maki. Mgn ce gamai da Asif da Nur.

Kin san auran su auran hadi ne toh mgnr da nake maki har sun far samun sabani jiya Umma ta kira ni ta ce min na ma shi mgn yau da na samai shi ya dinga min hauka kamar wani tababbai bayan ya koma daki ina bata hkr sai na tambaye ta in tana son shi ta ce min A'a, abinda ya fi ban haushi tana da wanda ta ke so, har ga Allah na tausaya mata dama Asif din na son ta da da sauki zai iya yaye mata wancen son ya sa na shi amma dukan su ba mai son juna, fada min ya zamu hada kan su.

Halimatu ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Chab aiki ja, gaskiya da tausayi musanman Nur ita mace ce shi kuma namiji ne zai iya kara auran wadda ya ke so amma ka san yanda za ka yi Asif ya fara son ta shi ne first ita na ta mai sauki ne domin mata muna da rauni.

Ya ce "Amma ta ya zan sa Asif ya fara son ta?

Ta ce "Ahh ba dan'uwnka bane ay kafi kowa sanin shi tin da komi naku daya ne ka ga feelings din ku zai iya zama daya."

Ya ce "Ba zaki ganai ba, Asif shegan taurin kai garai shi."

Yanzu dai ki fada min mi ita Nur din zata yi ta sa mashi son ta.

Ta ce "Abu ne mai wahala dama tana son shi da zai zo da sauki, shawara daya ce ko wanan su ya dau kaddarar sa su zauna su fara zaman auran su a hankali zasu fara son junan su amma mu ba abinda zamu iya face mu basu shawara su zauna su karanci halin junan su abinda daya baya so kar daya yayi ma daya haka ma abin da yake so sai ya ma daya.

Ya ce "Kin kawo shawara zan ma Nur din mgn ba ta da damuwa .

Ta ce "Ay ka sha fada ba sai ka fada min ba."

Ya ce "Toh yanzu minai abin kishi bayan ta auri twin brother na."

Ta ce "Sai kuma aka ce ma kishi nake."
Ya dubi Qawwama dake bacci ya rike kafar ta ya fara karkadawa.

Ta ce "Dan Allah kar ka tada min ita da kar na samu tayi bacci."

Ya ce "Ina ruwanki ki kwanta ki yi bacci."

Ya karasa mgr yana jawo Qawwama.
Ta ce "Da Allah na hada ka kar ka tada ta bacci take kai ka ji da ita tada ka kana bacci."

Ya ce "Kin ga ba ruwanki mu ba yanzu muke bacci ba ki kwanta ki yi bacci in ji da baby na."

Ta kwanta ta ce ka ji da ita. Ta bashi baya. Yayi dry. Ya mikar da Qawwama yana karkadamata kafa har sai da ta tashi.

Zata fara kuka yace "Look Abi ya dawo oyo oyo."

Ya rungumai ta. tayi shiru daga kuka sai murna.

Asim ya dubi halimatu yace "Kin ga ke ma ki tashi dan ni ban jin bacci Qawwama bata jin bacci ki tashi."

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now