Chapter 58

7 1 0
                                    

Nur ganin ta kusan kai wata guda a gidan Umma amma shiru ta ki daukar mataki, ta kira Mahaifin ta ta fada mashi duk abubuwan dake faruwa ta roke shi da ya turo mata kudin flight ta dawo gida ita ta gaji da cin kashin da ake mata.

Mai martaba bai ji dadin haka ba, ya bata hkr sannan yace mata shi da kan shi zai zo ya dauke ta su tafi. Ta ji dadin haka sosai ta godai ma shi.

Kwana biyu da yin waya da shi mai martaba da Raihana suka zo kano. Alhaji inuwa sanin zuwan su ya jinkirta fitar shi.

A parlourn Alhaji Inuwa a ka tarbe su, Nur da ke dakin Aisha ta sanar mata da su Mummy sun karaso.

Farin ciki ne ya gauraye jikin ta. ta sauka daga gadon da sauri ta sauka kasa Aisha na biye da ita a baya.

Bata tsaya ko ina ba sai parlourn Alhaji Inuwa.

Ta na isa tayi sallama tare da wuce wa wurin mahaifinta dan ba ta Mummy take ba.

Mai martaba ya budai mata hannu ta rungumai shi tana mai saukar da kukan farin ciki.

Ya rungumai ta sanna ya sake ta yana ce wa "Ya isa Nur."

Nur ta sake shi. Kukan da ta ke yi ya hana ta yin mgn.

Mummy ta ce "Nur kukan ya isa."
Mai marataba ya kara da "Ya isa haka Nur."

Nur ta goge hawayen ta.
Alhaji inuwa yace "Samu wuri ki zauna kafin Asif ya karaso."

Nur ta zauna a gefen kafar mahaifin ta,
Kafin zuwa Asif Alhaji Inuwa ya bukaci  Nur da ta kara fada mashi abin da ke tsakanin ta da Asif.

Nan ta fada masu duk abin da yake mata.

Mai martaba yace "Alhaji Inuwa wannan karon shine sulhu na karshe dan haka da yaron nan ya karaso ka sa shi ya sake ta."

Raihana ta ce "Mai martaba abi a sannu".

Inuwa yace "Haka ne mu jira Asif din shima mu ji ta bakin sa."

Bayan wasu mintuna da ba su wuce 5 zuwan 7 Asif ya karaso.

Da zuwan sa ya durkusa ya gaishe su sannan shima ya zaunaa.

Mai martaba ya ce "Asif mun zo nan dan naiman sulhu in kuma ba zai yu ba sai ka sake ta dan haka yanzu ka fa da min mi Nur ta ke ma wanda bakya so da kake kuntata mata rayuwa."

Asif ya dubi Umma ya dubi Mummy, tabbass dama ce ya samu da zai sake ta amma kuma ya san sakin Nur baccin ran mahaifyar sa ne zai hau kan shi.
Nan fah ya shirya mata karya da gaskiya.

Nur tin da ya fara take kuka tana karyatawa.

Raihan ta kwabe ta a kan tayi shiru.
Amma Nur bata yi shiru ba karshe ta kasa kama bakin ta da duk maganar da ta fito daga bakin ta fadi take sbd fushi har ta kai da tayi fucin da ba wanda ya ji dadin sa.

"Sbd ba ke ki ka haifeni ba na san da mahaifiyata na raye ba zata tillatsa min auren azzalumin mutun kamar shi."

Saukar mari ta ji a fuskar ta wadda Umma ta mata shi sannan ta mike ta ja ta gudan parlourn Abba ta zaunar da ita kan kujera.

Nur ta cigaba da kuka Umma ta zauna a kusa da ita cike da tsananin tausayin ta. kafin ta ce "Shiyasa ban so Raihana ta fada miki gaskiyar nan ba."

Nur in har ki ka mata haka da kin kasance butulu mai manta alkahairi,  Raihana ta dauke ki tamkar yar'ta, ta rainai ki ta baki soyayar da bata ba sauran yan'ya ta ba, haka mai martaba ya rainai ki ya dauke ki tamkar iyar shi ko sau daya basu taba gazawa a kan ki ba ba su taba nuna cewa ke ba iyar su ba ce ba su taba nuna banbanci ba tsakanin ki da sauran ya’yan su miyasa zaki ce haka.

In ma mahaifiyar ta ki na raye ba laille ne ta baki so da kaunar da Raihana ta baki ba. sannan raihana ta na son ki, ke karan kanki kin san yanda kuke fama da surraya ke shaida ce a kan makirar matar nan, matar da bata san mahaifiyar ki zata so ki amatsayin sirika?

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now