Chapter 37

12 3 0
                                    

Su ka karasa ciki zulaiah ta sa mai aiki ta budai akwatin Halimatu, ana budai shi a ka ga sarka dan kunnen zobobe na gold, azurfa, pearls da sauran.

Cikin hakin kuka da muryarta har ta shake ta dubi Salma ta ce "Aunty Salma wlh bani na dauke su ban dauki komi ba sharri kawai ake..

Zulaiha ta mare ta a hassale kafin  ta ce "Ohh ni ke maki sharri ko Hindu ko kuma Adama ko Safinatu ko kuma Maryam?

Ehye wa ke maki sharri?

Ga kaya a akwatin ki ki ce sharri ake maki.

Salma ta zauna saman sofa ta kasa yarda Halimatu zata iya haka tabbass sharri a ka mata, ke nan tsarnar da zulaiha ta mata har ta kai da zata mata sharrin sata a idon jama’a.

Zulaiha ta dubi Salma ta ce "Mi zaki ce yarinyar da kike ta faman supporting?

Salma tayi shiru dan itama abin ya daure mata kai.

Kowa ya dau kayan shi kafin su tafi sai da kowa ya fadi albarkacin bakin sa.

A ka barta ita da Salma a dakin. Suna fita ta karaso wurin Aunty Salma tana kuka tana ranstewa akan ba ita ta sace su ba, imma sace su tayi mi zai sa ta aje su a inda za a gansu, ba ita ta sace su ba.

Aunty salma ta ce "Na sani Amira ba zaki iya haka ba ki yi shiru ki daina kuka kin ga ki na dauke da yaro a ciki, magriba tayi ki shiga ki alwalla."

Daga haka ta mike ta wuce ta bar ta a dakin ta na ta kuka ta na da na sanin zuw, ga Asim bai nan bai kusa da ita balle ya tsaye mata.

Kan ace mi magan ta zagaye gida har da masu yan k'ari, kai har Magana ta isa kunnan Asim wanda da jin haka ya mike ya dau hular sa ya rufe gidan ya fito, bai tsyaa a ko ina ba sai tashar mota.

Motar su ta tashi bayan sun yi sallah magriba 7:30pm.  Kafin su isa borno ya kira wayar ta ta ki dagawa karshe ma ta kashe wayar dan a tunanin ta lbrn bai kai kunnan sa ba ba zata iya daga kiran ba kar ya shiga damuwa jin ta na kuka.

Umma suna dawo wa a ka basu wannan lbrn ay sirikar ta barauniya ce, ita kanta abin nan ya bata mamaki bata ce masu komi ba, masu fadin Magana na fada, ga Karin yanzu kunsan kowa ya san cewa ita mai aikin gidan uncle din su ce ya aura.

Umma ba ta ji dadin haka ba ta kulu akan zulaiha dan ta jawa jannat kunne kar ta sake ta fadi wace Halimatu sanna ta san Salma da Asif ba za su taba fadin wace ce Halimatu ba.

Rai bace ta wuce part din ta tasa a a kira mata zulaiha. Zulaiaha bata part din su tana part din su Hindu.

Kafin mai aikin ta karaso ta shiga dakin ta iske Halimatu zaune a kasa ta hadai kanta da gwiwar ta.

Umma ta ambaci sunanta.
Da sauri Halimatu ta goge idanuwanta sannan ta dago kan ta batare da ta bari sun hada ido da Umma ba.

Umma ta karaso ta zauna saman gado ta ce "An kawo mumunar lbr sai dai ban gamsu ba kuma ban yardaba.

Halimatu da muryar ta har ta shake sbd kuka ta ce "Wlh wlh Umma ba ni na dauka ba ban dauke su ba ban sace suba."

Umma ta ce "Ya isa haka yanzu ki fadi min miyafaru tin daga farko har karshe."

Halimatu ta fada mata.
Umma dake sauraren ta ta na duban ta ta ce "Yanzu shatin marin dake jikin ki duk su su ka maki?

Ta gyada kanta.
Umma ta jinjina kai ta na ayyana fushin ta A kan zulaiha.

Zulaiha data karaso wurin Umma a dakin ta ce "Umma gani an ce kina kira na."

Umma ta ce amsa da "Eh."

Zulaiha ta ce "Lfy Umma, Ohh lbrn halinta ya zo kunnen ki, daman ni na sani tsintar tiyar mage bata mage."

"Zulaiha!
Umma ta kwabe ta kafin ta kara da "Watch your mouth."

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now