3:45pm
Asif ya dawo daga aiki Umma ta ce da shi na yi wa Abban ku mgnr ka da Nur kuma ya amince.
Asif da yake cin Abinci har sai da ya kwarai. Umma ta ce "Subhannalah, sannu."
Ya aje plate din da ke hannun sa ya kalli Umma.
Umma ta cigaba "Ka na da number ta in kuma ba ka da number ta sai a baka sannan ka fidda ranar da za ka je ku gaisa."
Ya ce "Umma miyasa za a min haka?
Umma ta ce "Ban gane ba."Ya ce "Umma ni fa ba son ta na ke ba."
Umma ta ce "Ban ga ne ba kya son ta ba, Raihana ta ce min ta ma mgn kuma ka amince."
Ya ce "Umma na amince a lokacin dan ina jin nauyin idon ta amma Umma mi zan yi da wata Nur fi sabililahi."
Umma ta kame baki tana kallon shi. Kafin ta ce "Kana nufin kafi karfin ta kenan, ko kai ma zaka samo talakka irin dan uwan na ka ku bar ni da masifar Abban ku."
Ya ce "A’a Umma, yanzu duk matan dake gida a ce Nur za a hada ni da ita yarinyar da idon ta ke bisa kai."
Umma ta ce "Kana nufin bata da taribiya kanwata ta sangartar da ita ba ta bata tarbiya ba."
Ya ce "A’a Umma amma kin san rawar kan yarinyar nan dan Allah Umma ki ma Mummy mgn."
Umma ta ce "Ba wata mgn da za a kara yi dan hatta Ummi ta san da maganar haka ma mai martaba dan haka zai fi ma in ka sa a ranka auran ka da Nur babu fashi."
Ya mike yana gunguni ya fita. Ta yi tsaki.
A bangaren Asim da ya dawo ya iske ta tana baci sai bai tada ta ba ya wuce kitchen ya duba abinci babu.
Ya dawo parlour ya kunna Tv ya fara kallon kwallo har sai da aka kira magriba ya shiga dakin ya tada ta. Tana kwance ta ce "Habibi har ka dawo."
Ya ce "Na jima da dawo na iske kina bacci. Fatan kina lfy?
Ta ce "Lfy ta lau."
Ya ce "Ni na dauka baki lfy na dawo na gan ki kwance kuma ba abinci."
Sai a loakcin ta tuna bata dafa abinci ba ta ce "Sorry, yau ban jin yunwa sai na manta ban dafa ma abinci ba amma bari nayi sallah sai na dora ma."
Ya ce "No ki barshi in na dawo daga masallaci sai mu fita mu ci."
Ta ce 'Thank you mi love."
Ya sakan mata murmishi ya wuce.
Bayan fitar shi ta gyara kwanciyar ta tana so ta koma baccin sai dai kuma bata yi sallah ba, ta kori baccin dake idon ta ta tashi zaune ta mike ta wuce toilet tayi alwalla ta fito tayi sallah bayan ta gama ta shinke dai a jikin gadon ta na wudri. Yayi salma ya shigo ciki.Ta amsa shi sanna ta tashi zaune.
Ya ce "Ni fah wannan kwanciyar ban yarda da itaba, tashi muje asibiti."Ta ce "Shi ke nan ba daman mutun ya kwanta sai a ce bai da lfy."
Ya ce "Eh mana sbd na damu da ke yanzu dai sa mahaifin ki mu fita."
Ta ce "A’a da hijab din za fita."
Ya ce "Toh malama musilimatun qanitatun."Ta mike tsaye. Ya ce "Na kagagara ki sauka lfy. Ta amsa da Amin.
Ya rike mata hannu suka fita ya rufe gidan suka taka suka hau baban titi ya tsaida adaidaita. Ya kai su nearest eatry suka ci abinci a nan sannan suka dawo.
Suna shigowa a ka kira shi a waya. Ya rufe gidan sanan ya karaso ciki ya dau kiran.Asif muryar a shake ya ambaci sunan Asim.
Asim da jin muryar sa a shake cike da damuwa ya tambaye shi Asif kana lfy mike damun ka?
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomansaLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel