Chapter 28

12 3 0
                                    

Washegari da safe ya tashi ya fito parlour ya iske ta tana shara. Ya amshi tsintsinyar a kan dole shi zai ida share ay ita ciki garai ta ba a so mai ciki tana stressing kan ta.

Ba yanda ta iya ta bashi tsinsiyar. Zata wuce kitchen ya tambaye ta ina zata.

Ta ce mashi zan hada Ruwan mopping
Ya ce "No ban yarda ba je ki zauna."

Cikin shagwaba ta ce "Hm hm."
Shima ya biye mata "Kin ga bake kadai ce ba ki je ki zauna ki wuta ni zan yi."

Ta ce "A’a sai dai mu raba."

Zai yi mgn ya kyale ya ce "Naji mu yi mu biyu."

Ta ja cheek din shi ta ce "Thank you." Ta wuce kitchen ta hada Ruwan mopping yayi shara tayi mopping sannan suka wuce kitchen daman ba yau ba sun saba dafa abinci tare sai dai in bai gidan ko kuma yana busy a kan kasuwancin sa.

Ya dafa masu indomine ta soya masu plantain dan shi da plantain akwai amana.

Bayan ya gama breakfast ta rako shi bakin gate ta mashi Allah kiyaye ya fita ta dawo ciki.

Har yanzu bai da mota bai da machine. Ko da Asif ya ce zai bashi motar shi ya ce A'a in ya bashi zata kara mashi nauyin zuba mai da gyaran ta.

Asif ya ce mashi zai ji da dawainiyar haka. Asim bai yardaba ya fiso ya naimi na kan shi har shi ma yayi kudin da zai siya mota.

Musanman yanzu da yake bakin kokarin shi wurin ganin shagon na shi ya habaka sai dai shagon ya ja baya sakamakon hidimar biki da yayi da kudin ga kuma ciyarwa da sauran daukan nauyin iyali.

Ranar da farinciki ya bar gidan, kasa wucewa kasuwa yayi sai da ya biya ta gidan su ya lbrt wa umma lbrn mai dadi in da ya kara jin dadi umma ce kadai a gidan duk sun fita.

Daga part din Umma ya wuce na su Asif ya iske shi a daki shima ya lbrt mashi duk da Umma ta kwabe shi a kan ba a badi sai dai ba zai iya boyewa dan’uwan shi kyakyawan lbr irin wannan ba.

Halimatu tun da ya fita ta zauna ta na tunanin yanda zata koyi snacks da desert.

Ta jawo wayar ta ta yi dailing number maryamah ba ta daga ba ta kara kira ba a daga ba.

Sai ta shiga youtube tayi searching yanda ake milk cake dan duk cikin desert ya fi son shi.

Ta ga vidoes din da yawa ta rasa wane za ta bi haka ta fara kallon su daya bayan daya.

Ta na cikin kallon na hudu kiran maryamah ya shigo da sauri ta daga ta kare wayar a kunnan ta ta mata sallama ta amsa bayan sun gaisa maryamah ta ce "Na ga kiran ki fatan lfy?

Ta ce "Lfyl aunty Maryam daman tambaya na ke son yi miki."

Maryamah ta ce "Fadi Allah sa na sani."
Ta ce "Kin ma san ta."

Maryamah ta ce "Fadi ina jin ki."
Ta ce "wannan kawar ta ki mai catering na ke so ki tambayar min ita ya ake milk cake."

Maryama tayi karamar dariya ta ce "Lailai kina ji da wannan mijin na ki yau kuma milk cake za a mashi."

Ta ce "Xake din jiya yayi dadi na ji dama ni na yi da kai na sai ya fi jin dadin haka."

Maryama ta ce "Hali manya toh ga shawara bana mi zai hana ki yi joining class din ta tin da ta na yin classes na koyan irin wa innan abubuwan."

Halimatu ta ce "Eh sai dai nawa ta ke yi?

Kwankin baya ta taba turo min flyer ta ta kamar 50k a wata uku

Halimatu ta zaro ido ta maimaita "Dubu 50 fah, a barshi ina naga 50 balle in ba wani ajiyar ta."

Maryamah ta ce "Ay da kin iya kin wuce wurin kuma na tabbata kina samun kudi daga wurin shi dan Asim ba irin mutane dake make hannu ba ne."

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now