Suka koma gida Asif ya fada mashi abinda ya faru shima yaji dadin haka dan ba wanda zai ki tayi daga gidan Alhaji Inuwa.
Malan Yakubu suna tafiya shima ya je gidan yayan mahaifin ta ya bashi kyakyawan labarin nan wanda shima ya yi murnar haka kuma ya aminta
Halimatu ma tana komawa gida Umma ta bata wannan albishirin.Jalimatu ta rasa mi za ta ji murna zata yi ko bakin cikin haka.
Ta zauna ta yi tagumi Umma ta tambaye ta baki farin ciki da haka.
Ta ce "Umma ni ma ban sa ni ba, murna zan yi ko takaici, Umma yanzu zuri’ar da basu mutunta mutane, basu daukar talakka abin komi cikin su zan shiga Umma?
Umma kin san wacece mahaifiyar shi? Umma ita din fah yar ce ga tsohon sarkin Borno sannan kanwa ga sarkin yanzu, Umma ina ni ina su, mahaifin sa yana daya daga cikin masu fada aji a garin nan umma ina ni ina su. Umma ya fi karfi na, Umma kwanciyar hankali, farin ciki da walwala na ke so ba tarukan dukiyar da babu farinciki babu walwala balle nitsuwar da za aji dadin ta.
Umma ta ce "Na sa ni amma shi ay yana son ki.'
Ta ce "Umma yau da gobe sai Allah, ko ba dan ba dadai wata rana za su min gori gamaida dukiya, Mulki ko saurata."
Umma ta ce "Ki na nufin ba zaki aure shi ba? shi ke nan ba ri baban naku ya dawo in ce ya kira su ya ce baki amince da tayin su ba.
Bayan malan Yakubu ya dawo ya zaunar da ita ya tambaye ta in ta na son shi, kar ta dubi halin gidan su, halin Asim za ta duba da shi zata zauna ba da su ba dan haka ta fadi mashi in tana san shi in kuma bata san shi yanzu ya kira su ya ce ya fasa ba da yar shi.
Tayi shiru ta rasa wata kalal amsa za ta bada.
Ya ce "Kinyi shiru ke na ke sauraro kina son shi ko a’a.
Ta gyada kai.
Malan Yakubu ya ce ba gyada min kai zaki yi ba amsa zaki bani kina san shi.
Ta ce "Baba zabin ka shi ne nawa."Malan Yakubu yace "A karon karshe Halima kina son shi?
Ta ce "Baba duk hukunci da ka yanke shi zan bi."
Malan Yakubu ya ce "Shi ke nan tin da haka ki ka ce ko gobe kiyama na fita tin da har sau uku na tambaye ki ki ka ban wuka da nama, gobe za su zo za su kawo kudin naiman auran ki za a sa rana. Kin iya tashi.
Ta tashi ta koma ciki ta na tunani kala kala a zuciyar ta kiran Asim ya shigo. Ta na dauka ya ce "My would be wife.'
Ta gaishe shi ya amsa sannan ta ce "Miyasa ka min haka, ka dawo baka fada min ba sannan ka aiko iyayen ka gidan mu, Miyasa kayi hk?
Yayi karamar dariya ya ce "I'm sorry yourhighess I just want to give you surprise, fada min baki farin ciki ne?¿
Ta ce "Eh bana yi."Ya ce "Huzaifah dai ya ce mai karya dan huta."
Ta ce "Au karya ma nake ma."
Ya ce "No no no, ni na isa, kin ga daga gobe na san ke din ta wace."
Ta ce "Har yanzu da sauran ka wa ma yace ma zan aure ka."
Ya ce "Ay Magana ta kare dan zuwa yanzu na gama sanin ki so stop pretending na san ki na so na."
Ta ce "Aure fah ba abin wasa bane miyasa zaka turo gidan mu?
Ya ce "Sbd ina son ki kuma kina so na."
Ta yi shiru. Ya ce "Amira miyasa baki so na toh, miyasa baki son aure na didn’t I deserver you or what?
Ta sauke karamar ajiyar zuci ta ce "Ba wai kai ne bana so ba ina tsoran..
Ya yanke ta "Khalas.. Na ji abin da nake son ji."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel