Washegari bayan sallah isha’I ya shiga part din hajiya shafa ya dau lubna ya fita da ita.
Ya fara mata siyaya dan gobe za a maida ta gida sannan yayiwa huzaifah wadda ta fi ta jiya ya wuce unguwar ta su. Da ya isa yayi parkin a gefen kaunar kamar kullun, ya dauko ledar huzaifah sannan ya dauki Lubna su ka karasa cikin layin.
Yau ma ya hadu da Nura sai dai yayi kamar bai san da su ba ya karasa kofar gidan yayi sallama.
Halimatu da Nura da kallo suka bishi. Nura ya tambaye ta daman yana da aure.
Ta amsa shi "A’a kila iyar yaya shi ce ko yan shi."
Nura ya ce "humm."
Ta dubai shi ya ce "Ba komi."A cikin gida huzaifah na jin sallamarsa ya mike da sauri Umma ta ce "Dawo ka zauna.
Ya marairaice ya ce "Umma yallabai Asim ne fah, kuma halima na wurin shi."
Yayar Halima da ta zo gidan yini kasancewa yau juma’a kafin mijin na ta ya zo daukar ta ta ce "Umma Halima ta yi hankali ke nan ta na kula samari yanzu."
Umma ta ce "Ay dolen ta ne ayi mutun shi kwatakwata bai san maganar aure."
Nusaiba ta ce "Haidar dai ya ce a mata rukiya."
Huzaifah ya faki idon Umma ya fice. Ya na sa kofar gidan ya rintsina ya gaishe shi Asim ya amsa sannan ya mika masa hannu suka yi musabaha.
Huzaifah ya dubi lubna da ke hannun shi ya tambaye shi "AI kanwar ka ce?
Asim yayi murmishi ya ce "A'a iyar yayata ce."
Huzaifah ya ce "Ya sunan ta?
Asim ya amsa shi "Lubna."Huzaifah ya ce "Chab sunan yan gayu."
Asim yayi karamar dariya ya ce 'Kai ma sunan ka na yan gayu ne."
Asim ya mika mashi ledar. Huzaifah ya sa hannun sa ya rufe bakin sa sannan ya waigi Halimatu.
Ya girgiza kai ya ce "A'a."
Asim ya ce "Ba ka ce mu abokai ne ba."
Huzaifah ya ce "Eh, Umma Baba da kowa ma fada za su min."
Asim ya ce "Ba za su ma ba kai dai ka amsa ka ji, be a good boy.
Huzaifah ya ce "A’a."
Asim ya roke shi amma huzaifah ya kiya. Ba yanda Asim ya iya ya ce toh saifullahi na nan.
Ya ce "A’a sai Haidar. Ya ce toh kira min shi. Ya juya ya koma ciki ya na tafiya a hankali dan ya san yayi laifi Umma ta ce kar ya fita ya fita. Ya karasa kusa da Haidar ya rada mashi yallabai Asim na kiran ka. Ya na fada mashi ya koma wurin kofar dakin malan Yakubu ya zauna.
Haidar ya mike Umma ta tambaye shi ina zuwa?
Ya ce "Zan je wai Asim ke kirana."
Umma ta ce "Mi a ka yi? Ba halimatu na chan ba."
Haidar ya ce "Umma kin san halin ta yanzu haka ko kula shi ba ta yi ba bari na je."
Ya ida mgnr yana fita waje. Ya mika mashi hannu suka yi musabaha sannan ya ce na kawo mashi snacks yace ba zai amsa ba jiya an mashi fada shi ne nace ya kira min kai, dan Allah kar ka ce ba za ka amsa ba."
Haidar ya ce "Toh tin da ka riga da ka kawo ba dadi a maida kyauta amma sun isa haka kuma mun godai."
Asim ya ji dadin haka ya mika mashi ledar.
Haidar ya tambaya ina halimatun?
Yayi murmishi ya ce "Da man wurin huzaifah na zo."
Haidar dai bai yarda ba ya ce "Toh shi ke nan sai anjima kuma ya godai."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomantizmLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel