A bangaren Halimatu ta na aje wayar ta ja tsaki.
Haidar da ke wurin ya tambaye ta "Lfy ki ke mana tsaki?
Ta Harare shi kafin ta ce "Ina ruwan ka."
Ya ce "Da ruwana kuwa da ga aje waya sai tsaki."Umma da ta karaso wurin su ta tambaye yi lfy.
Haidar yace "Umma daga ta gama waya ta wani ja tsaki."
Halimatu ta ce "Ba na san shiga tsarbu ba kare." Ta kara yin wani tsakin.
Huzaifah da ke cin fanke ya tsoma bakin sa, "Ai ne ya kira shine bayan sun gama ta yi tsaki."
Harara ta wullawa huzaifah daa yana kusa da ita da hannu zata kai mashi.
Umma ta zauna itama ta fara cin fanke nan ta.Haidar kuma yace "Dalla malama ki bari wanda ya bata maki rai ki mashi dacin rai ba mu ba, Allah sa kar Qawwama ta dauko wannan bakin halin na ki."
Umma ta kwabe Haidar "Kai Haidar ban sa haka, ina Ruwan ka da ita."
Ya ce "Umma gaskiya na ke fada mata."
Halimatu ta ce "Rike gaskiyar ta ka bana so."
Yayi dariya ya ce "Kar ki so sai na fadai ta."Umma ta dubai ta ta ce "Hala maganar tafiyar ta ki ce ta bata maki rai ko."
Halimatu da ita ma ke cin fanken ta aje shi sbd haushin da ya cika mata rai.Haidar ya ce "Gwara ma ki koma ko mun huta kin hana mu sakat a gidan nan."
Umma ta ce "Kai Haidar tashi ka fita ba ka gama Karin ba maza wuce ka bar gidan nan."
Ya mike yana dry yace "Allimoss! Kafin ki tafi ki kira ni na taya ki daukar kaya."
Duka wurin suka yi dry. Ita kuma ta hada gabas da yamma.
Karfe 2pm jirgin su ya sauka. Bubu ya zo ya dauke su yamaida su gida.
Direct part din Umma suka isa ta masu sannu da zuwa kafin ta tambayi su Nur, Asim Ya ari bakin Asif yace "Umma Nur bata da mtsl bata da damuwa, suma fa yi matching."
Asif ya kai mashi naush,
Asim ya ce auch kai haba daga na fadi gaksiya.Ya mike ya koma wurin umma ya cigaba da ce wa, "Umma kin san in fa tana wurin shi kasa cewa komi yake sai bayan ta tafi ya ishe ni da surutai, Umma ya dai fada sundum a soyyar ta."
Umma ba karamin dadin haka ta yi ba. Asif kuma ya bata rai fuskar nan daure.
Asim ya cigaba "Ay Umma Nur bata da mtsl, so kind.Asif yace "Dallah malan baka da aikin yi sai kuda ta bayan kana da mata."
Asim ya ce "No idan mutun na da halin kwarai dole a kudata ka ce kana kishi."
Asif yayi tsaki ya fita. Umma da Asim suka bishi da dariya.Har dare yayi Asim bai leka wurin su Halimatu ba wanda hakan ya kara bata mata rai tunanin ta ya ci galaba a kanta, da gaske ya samu watta wadda ta fi ta, daman ita ba tsarar shi ba ce yanzu kuma ya samu tsarshi wadda suke jinin sarauta tana da kudi.
A waya yace mata ta shirya da safe zai zo daukarta.
Ta amsa mashi da toh. Yau basu wani jima ko minti 5 ba su yi ba.
Ganin haka shima ya shiga damuwa mi ya samai ta ko bata da lfy walwalalta ba kamar jiya ba.
Haka dai su ka kwana kowa da irin tunanin da yake yi.Washe gari tin da Asuba da ta tashi bata koma bacci ba, ta hana Asee komawa dan ita ke taya ta shirya kayan ko a ce kun san ita ta shirya mata kayan dan tin da ta tashi bata jin dadin jikin ta.
Har gari ya ida waye wa Umma ta dora masu abinci safe dan bata so su makara daga su Halima har su huzaifah da za su je thafiz yau.
Asee na gama shirya masu kayan ta koma ta kwnata ba bacci take ba amma idanuwan ta a rufe suke.
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel