Ta ce Kayi shiru kai na ke saurara.
Ya sauke ajiyar zuci ya ce "Umma na san ko na fada maki ita ba zaku yi amanna ba shi yasa kwara na cigaba da addu'a ke ma kin min duk da ina son yarinyar nan ina son ta da gaske kuma ina son in aure ta sai dai nasan ba zai yu ba.Umma ta sauko daga gadon ta koma wurin sa ta zauna ta nace wa wacece I want to know her?
Ta san kai dan waye da zata ki ka, ita wacece da zata ki amsar tayin soyayar ka?Kana dan Alhaji Inuwa wanda garin kano ke hannun su, ka na jikan tsohon sarkin Borno d'a ga current king, kuna da Kano kuna da Borno da Maiduguri, wa ta yarinya ce ta ke son sa maka dafin so ba ta isa ba. "
Ya yi murmishin ciwo ya ce "Umma ba iyar kowa ba ce, mtsl na daga wurin ku na san ba za ku bari na aure ta ba musanman Abba dan su din talakkawa ne, ba masu kudi bane, ba masu matsayi ba ne ba masu gata bane ba masu sarauta ne sai dai kuma suna da abin da suka fi mu duniya da lahira wato ilimin addini.
This is a bolt from blue, bata tsanmani haka ba. Ta ambaci sunan sa sau biyu cike da mamaki kafin ta ce "Kai ma ka san zancen nan ba dan’uwansa bane."
Ya marairaice ya na cewa "Umma shiyasa nace ki taya ni da addu'a dan wlh ta ma riga da ta sa min dafin son ta da har ina ji rayuwa ta ba cike ta ke ba in ban samaita ba."
Da farko Umma ba ta so ba ganin yanda yayi sanyi ya na Magana hakan ya sa ta tausa maganar ta. Ta ce "Fadi min ina kuka hadu? Har yanzu ba ka fadi min ba."
Yayi shiru yana fargaban abin da za ta ce.
Ta ce "Ba shiru za ka min ba mgn za ka yi kila in na gamsu in taimakeka wurin Abban ku."
Dafe goshin sa yayi yana kallen kasa yayi shiru. Tabbas Umma ta fuskanci damuwar sa hakan yasa ta kara tausasa lafazin ta "Ta ce Asim you should open it to me ba wai ka boye ba, ko da ya ke ban kai matsayin da zan ji ta cikin ka ba bari na kira Asif."
Da sauri ya dago kansa wanda umma tayi mamakin chanjin launin idon sa daga fari ya koma jaja-jaja. Ta ambaci sunan sa.
Ya ce "Umma ba zaku taba fahimtata ba musanmana Abba, dan Allah ki min addu'a, Allah ya cire min ita a zuciyata na san ba matsayi na ba ce amma zuciya bata da kashi ta rasa wadda zata so sai iya talakka, talakkan da bai aje ba sai yafita ya naimo, and the worst thing wai yar aiki a gidan kannen mahaifina wanna wata irin jarabawa ce Umma?
Ya rufe mata baki ba ta da ta ce wa jin mai aiki. Ya cigaba; "Umma kin tilasta sani na so a ce in kashe in birne in zan iya sai dai a bune mai wiya a wuri na, umma yarinyar nan ba kowa ba ce fa ce Halimatu mai aikin Mummy matar kawu mala.Saukar mari ya ji a kunchin sa. ya rike wurin ya sadda kai.
Rai bace ta ce "Ba ka isa ba gwara tin wuri ka ma cire ta a zuciyar ka dan kai ba tsaran ta ba ne. Mai aiki ina kai ina mai aiki. Zancen nan ba dan'uwansa ba ne gwara tin wuri ka cire ta a zuciyar ka dan abin da bazai yu ba ko ni ba zan aminta da haka ba balle mahaifin ku. Mtsww shasha-shasha.
Ta mike ta koma gado kafin ta ce "Kashe min fitila ka tafi.
Ya mike kwantakwata bai da kwari jikin sa ya kashe fitila ya koma dakin su.
Umma da fitar shi ta kasa gane haka, mai aiki da gaske dan ta yake so, sai kace a rubutun zubai.
Dole ta dagatar da shi dan wanan zubar da mutuncin su zai yi, mai aiki.. haka har ta yi bacci tana tunani.
Ya na shiga part din su, Ayan ya iske shi kadai a parlour ya mashi sallama ya wuce cikin dakin su.
Ba wanda ya tanka ma wa ya chanza kayan shi ya kwanta tare da juya masu baya.
Ya rufe idon sa yana jin zuciyarsa na masa nauyi ga zafin da ta dauka lokaci daya, Umma ce hope din sa idan ta yarda ya san za ta shawo kan Abba sai dai a wannan karon ita kanta bata goyi bayan shi ba.
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel