Chapter 48

9 2 0
                                    

Biyu na yi ta fara kuka tana ta kuka ya dora ta kan baby rocker vata yi shiru ba daman in tana kukan rufe idon ta ta ke bata ganin komi haka ma bakin nan na ta bai amsan nono balle a ce in ta fara sha ta yi shiru haka suka zuba ido suna kallon ta Asim kamar yay kuka ganin kukun da ta ke tamkar za a cire mata rai. Yauma bata dai na kukan ba sai 5. Tana yin bacci su kuma suka yi sallah su ka koma.

Haka duk dare Qawwama ke kuka tin yana damun Asim har ya zo ya dai na damun shi, da ta fara kukan zai dauke ta su fita parlour ya dora ta saman rocker ya mata addu’a ya tofe ta ya kwanta duk da da ya kwanta bai yi baccin minti 30 zai tashi ya kara kallon ta ya kara bata hkr tamakar mai jin abin da yake ce wa, sannan ya kara mata addu'a ya kwanta har asuba. Ya ma riga da ya saba.

A  bangaren su Asif an sa mashi aure shi da Nur duk da har a ka sa ranar bai naimai ta a waya ba ita ma bata naimai shi ba, kowa harkar gaban shi yake musanman Asif da bai damu da mgnr ba sai anyi yake tuna da zai yi aure ba kamar Nur wadda abin yana damun ta tayi tayi Mahaifinta ya janye mgnr auren ta da Asif amma ya kiya daman ba ma ta bi ta kan Mummy dan ta san ba zai yu ba.

Mahaifin nata shi ne mai daure mata gindin yin abubuwa shima a mgnr auren ta mimakon yayi backing din ta a’a shi ke supporting aure.

Qawwama na 6 month Asim da Asif sun je bikin Aminin su Ubaidu wadda za a yi a kaduna kasancewa matar da zai aura a kaduna ta ke za a yi event so tin kafin daren daurin auren su ka je kaduna za su yi kwana uku.

A ranar da ya tafi A ranar Aunty zulaih, safna, sadiya, da Yasmin suka zo gidan h
Halimatu.

Halimatu na zaune a parlour tana ba Qawwama fri so ta ji a na knocking ta  mike zata wuce Qawwama ta sa kuka ta dawo ta dauke ta ta fita ta budai gidan.

Tana budaiwa ganin su sai da gaban ta ya fadi.

Ta sakan masu fuska tare da ce wa su shigo.

Suka karaso ciki ta rufe gidan ta bi su a baya. Ta shigo ciki ta ce da su zauna.

Saukar mari ta ji a fuksar ta wanda ya gigitar da ita kasan ce wa unexpected ta ji shi a fuskar ta wadda zulaiha ta mata shi.

Halimatu ta dubai ta.
Safna ta ce "Ya dai mgn za ki yi ne?
Ta na ida wa ta kara sauke mata na ta.

Halimatu ta ce "Ban gane ba mi na maku da za ku zo har gida ku duke ni mi na maku?

Safna ta fashe da dariya ta ce "Au tambaya ma ki ke jikin ki ne zai gayama ki."

Ganin da gaske dukan ta za su yi ta sauke Qawwama ta aje ta saman kujera ta fara maida masu da martani duk da ta jibge su sai dai ina sarkin yawa ya fi sarkin karfi suka doke ta san ran su.
Sannan suka mata gargadi da ta rabu da Asim in har ba so ta ke ta bakunci lahira ba dan in har ta cigaba da zama za su cigaba da musguna mata har sai ta gwammace bata zo duniya ba. sanna kar ta kara shiga dangi ba su gayyatar ba sa gayyar kayan tsiya.

Nan suka bar ta tana kuka. Qawwama kuma sai kallon ta ta ke ta na wasa da abin hannun ta.

Haka ta tsaya ta ci kukan ta har ta gaji kafin ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskar ta tayi alwalla takai karan su wurin Allah.

Ko da Asim ya kira ta da dare bata nuna mashi komii ba har ya dawo.

Ganin tabo a gefen goshin ta ya tambaye ta mi ya samai ta.

Ta ce mashi bige wa tayi da bango. Dariyar keta ya mata dan a wurin qeta shi da Asif ba a san waya fi wani ba.

Sai da ya gama mata dariya yagama jan ta a kan sai ka ce karamar yarinya zata bige da bango. Sai da yagama zolayar ta sanna ya bata hkr.

Ya dawo da kwana biyu zai fita kasuwa maman sayyid ta tarbe shi, bayan sun gaisa ta fada mashi abin da ya faru wanda hakan ba karamin kona mashi rai yayi ba. Ya mata godiya ya koma gida ran shi bace.

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now