Da dare bayan sun gama cin abinci suna fira ta mashi mgnr catering din ya ji dadi sosai da ta naimi in da zata iya abinci.
Ya tmby ta nawa ne kudin ta ce 55k ne.
Ya ce da wannan bana in sama ma maki chef bana.Da jin haka sai ta rasa mi zata ce
Ya ce "Ko baki so ne? Na ga zai fi sauki kullun ba sai kin dinga fita ba za a zo har gida a koya maki.
Kin san ban san kina fita hasken ranar yana dukan ki, kuma kin san i'm jealous of you.Ta sauke karamar ajiyar zuci ta ce "Habibi i'm sorry ka yi hkr bazan kara ba."
Ya ce "Ban gane ba mi ne ne?
Ta ce "Na yanke hukunci ba tare da na tuntubai ka ba har na biya kudin registration din."
Ya ce "Ikon Allah kin biya ko ki fada min."
Ta ce "Sai bayan na biya nayi tunanin haka first I want to surprise you every day with new dishes sai na ga bai da ce ina fita ba tare da na tambaya ka ba amma kayi hkr."
Ya ce "Ba komi but next time kar ki sake haka ba na so, Zan tura maki 55k din. "
Ta ce "Na riga da na tura mata fah."
Ya ce "Wanann hakki na ne sbd ni za aje a koyo dan haka ki rike kudin ki kin yi wata bukatar da su."
Ta ce "Nagodai my love."
Ya ja hancin ta ya ce "Ke ko baki da dama. Yazu dai ina wake da shinkafa na?
Ta ce "Chab ay na cinye shi dan shina ci da safe na ci da rana. " Ta ida maganar ta na dora kanta bisa cinyoyinsa.
Ya ce "Hajiyar wake da shikafa daga yau sunan ki ke nan…
___*A na ta laulayin ciki da shi yau dadi gobe ba dadi. Catering class din da ta shiga ba sosai ta ke zuwa ba sbd ciki.
Asim da san yara tin kafin cikin ta yayi 4 month yafara siyen kayan jarirai duk abin da ya gani physical ne ko a online ne sai ya siyo shi. Kuluwa kuwa ta na shanta.
Ranar friday ita da shi na kitchen, shi ya na tuka tuwo ita kuma ta na yanka alaiyahu. Huzaifah da ke parlour yana kallo jin a na knocking ya je ya bude.
Jannat da yar dattijuwa ummi babba iyar marigayi sarki haroon, former king of borno.
Ya durkusa ya gaishe su. Ummi ta amsa shi dauke da fara’a a fuskar ta Jannat kuma fuskarta ta daure. Su ka karaso ciki ya rufe gidan.
Sallama ummi ta rabka ta na karasowa ciki.
Asim dake tuka tuwo yace "Kamar muryar ummi."Halimatu ta mashi nuni da waccece ummi. Ya ce "Yayar Umma dake aure riyad.
Ta ce "Ohh kace babbar bakuwa mu kayi."
Asim ya amsa sallamar ummi ya mike ya na ce wa "Bari na je na tarbe ta kafin ta ce na mata rashin mutunci." Ya fice.
Ita ma ta wanke hannunta ta yarfe sannan ta bi bayan shi.
Asim ya fito dauke da fara’a a fuskar sa ya ce "Marhaban mutanen riyad."
Ummi ta ce "Ohh Allah my son."
Ya karaso ya ce "Ummi welcome." Ya zauna a gefan ta.
Halimatu ta karaso ta tuskunnan ta gaishe ta.
Ummi ta ce "Masha Allah wannan ce sirikar ta mu. Sannunki sannunki.
Halimatu ta sakan mata murmishi ta mike tana ce wa "Bari na kawo maku abin sha."
Jannat ta ce "Ba sai kin yi ba." T fadi ba tare da ta kalli in da suke ba.
Ummi ta ce "A’i kam a kawo min in ke ba zaki sha ba."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel