Haka yaran suka tubure su ba za su gidan aunty zulaiha ba duk da akwai jikoki sa’anin su, amma kaf cikin jikikoin ya’an Asif kadai suke shiri shima dan suna jikin gida daya makaranta daya both arabi da boko, sai yan' an Aunty salma wanda su xun girme su, apart from them ba mai yi da su daga masu jin haushin su sai masu masu hassada.
Bayan da Ammi ta iya ta sa ma su ido haka suka ki zuwa kamun
Abin haushin ba su je ba amma har an samu wani munafikin da ya fadiwa Abi ay matar shi ta na nisanta yaran shi wurin yanuwan su, bata so suna intraction da sauran yara gani ta ke yaran ta sun fi na su. Duk da ya gwale wanda ya kawo mashi labarin akan hakan nan ba za su ki zuwa ba, wani uzuri zai hana su zuwa.Hakan na bakan ta masu rai dan so da dama za su kawo mashi gulma ko makirci sai dai ya gwale wanda ya kawo mashi in kuma ya koma gida ya haw Ammi da fada ba ta ce mashi komi sai in ya sauko sai ta fadi mashi gaskiyar sai ya bata hakuri.
Haka ma yau sai dai yau yaran ne suka amsar wa mahiafiyar su.
Suna zaune bisa dining gaba ki daya suna cin abinci ya ce "Ammi na ji an ce ba ku je Kamu ba ko zan iya sannin dalili kin zuwan ku bayan kin san bikin huda a ke.Kafin Ammi tayi Magana siyama charab ta amsa tambayar "Mu muka ce ba mu zuwa."
"Siyama! Ammi Ta kwabe ta.
Qawwma ta ce "Abi ba fah laifin Ammi ba ne mu muka ce ba za mu ba."Ya aje spoon din hannun shi ya ce "Dalili?
Ammi ta ce "Abi kayi hakuri ba wai.."
Siyama ta katse ta "Abi gidan ba dadi duk ba su son mu."
Duban Ammi yayi cikin mamaki, ya san family din ba sa son ta amma miyasa zata nunawa ya’an shi haka, bai yi tsanmanin haka ba.
Za ta yi Magana ya dagatar da ita, "Kin yi daidai." Ya mike ya wuce ya bar dinning ya koma parlourn sa.
Rai ba ce Ammi ta ce "Ban hanaku tsoma bakin ku in muna Magana da Abi ba?Siyama fitsarara ta ce "Ammi we didn’t interrupt we just told the truth, kuma kin ce babu kyau karya." Ta ida maganar kamar ta na turke mahiafiyar ta. Qawmma dai shiru ta yi ba ta ce komai ba.
Ammi ta ce "Daga yau ina Magana da Abi wani ya sa min baki sai na fasa bakin." Daga haka ta mike ta wuce parlourn shi.
Syama ta ce "Chab a dake mu a hana mu kuka."
Qawwma bata ce ko mi ba dan tin ba yanzu ba ta ke monitoring din su, ta na bin su a jiki amma ko da yaushe family din basu da aikin yi sai zagin Ammi.
Ta isa parloun shi bai ciki sai ta wuce dakin sa bai na sai ta wuce balcony din dake dakin sa. Tsaye ta gan shi yana kallon ilahir unguwar. Da ga kofa ta ambaci sunan shi bai amsa ba ta kara kiran shi yayi shiru sai ta matso kusa da shi tare da hugging din sa ta baya. Ta dora fuskar sa saman bayan sa hannunwan sa saman kirjin sa cikin sanyi lafazi ta ambaci sunan sa "Darling ba wai haka nan muka ki zuwa.."
A fusace ya juyo ya ce "Ban damu da dalilin kin zuwan ku ba, habibty ban tsanmani haka daga wurin ki ba why will you tell the children the issues between you and my family, mi suka sa ni? Ina suka yi hankalin sanin dai dai da ba daidai ba?
Kwalar da ta dan sauko ta goge ta tare da yin murmishi mai ciwo ta ce "Yaran daa da yanzu ba daya suke ba, yanzu ba sai ka fadi wa yaro abin da ke wanzuwa ba zai gane, idan na fadi masu gakiya, mi zata kare ni da shi? Mi zata rage ni da shi? Kai karan kan ka ne a bayyane suke nuna min kiyaye da hassada mi zai sa yara ba za su fahimci haka ba, nayi imani ko rantsuwa zan yi bazan yi kaffara ba su Farhin su ma sun san da haka, amma ba komi, sun din yan’uwan ka ne kuma dole ka goyi bayan su.
Ta goge hawayen ta ta sauke ajiar zuci ta fashe da kuka. Ta juya zata wuce da sauri ya chafko ta ta fada saman kirjin sa, kukan ta ba karamin tada mashi hankali yake ba, ganin yanda yayi hugging din ta ta kara fashe wa da kuka, cikin kuka ta ce "Mi zai sa in fadi masu gaskiya bayan su da kan su suka gano haka?
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel