Chapter 53

25 4 0
                                    

Maganar sakin Nur har ta budai fada kowa ya san da haka. A bangaren Asif shima fada ya sha shi wurin Umma Abba da kuma Asim  har ma da sauran yan’uwansa sai dai kuma ya kafe a kan ba zai maidata.

Bayan kwana biyu mai martaba Ibrahim ya kara tuntubar Nur ya ji shiru ba ta kawo mashi maniamin na ta ba.

Mummy da ke zaune a kan kujera kusa da mai martaba, a cikin parlourn shi, ta dubi Nur ta ce "Ke nan sbd da shi ki ka kashe auran na ki."

Mai martaba yace "Dagata Raihana, kar ki takura mata ki barta ta yankewa kanta rayuwar ta na gaba sannan shi Asif ya bani kunya ban zata zai wulkanta min ya’ ba."

Raihana ta ce "Mai martaba hkr zata yi ta koma."

Mai martaba yace "A’a ba zata koma ba wannen shine hukunci na."

Ya dubi Nur ya ce "Fada min waye yaron da ki ke so dan gida waye?

Nur da idon ta har sun cika da kwala.
Ya tambaye ta lfy mi ya samu idon ki.

Ta ce "Daddy Mummy ku yi hkr amma dan Allah kar ku ce na koma wurin shi."

Mai martaba ya ce "Ya salam, Nur ay na gama mgn ki kwantar da hankali ba zaki koma mashi ba".

Ta girgiza kan ta, ta fara kuka a hankali.
Mai martaba yace "Haba mana ki yi shiru minene abin kuka ba mun gama mgn ba."

Cikin kuka ta ce "Fatah bai so na ya yaudare ni yayi auran shi."

Mummy ta ce "Waye shi?

Ohh yanzu kin kashe auran ki sbd da shi shi kuma yayi auran shi sai ki cigaba da zama a karamar bazawa mtsww.

Ta mike ta fita. Mai martaba ya bita da kallo kafin ya mai da kallon shi kan Nur da ta ke kuka. Ya ambaci sunan ta.
Ta kalle shi.

Ya ce "Tin da ki ka ga ya yi aure toh ba alkahairi ba ne, abin da nake so da ke ki kwantar da hankalin ki ki dai na kuka.

Cikin kukan ta ce "Daddy dan Allah kar ka ce za ka aura min wani."

Daddy yace "A.ma ba kin zauna ba aure ba"

Ta ce "Amma Dady I’m still young, elders sisters di na ba su yi ba."

Daddy ya ce "Eh amma su mania min ne bai zo ba sannan ba ke ce farko ba kuma ban so ki zama karshe in akwai wadda zata zama karshe to auta ce. Na baki lokaci ki nitsu ki naimawa kan ki abokin rayuwa, safuwan da habib  basu maki ba koh?

Ta daga mashi kai ya ce "Toh shike nan kiyi shiru ki dai na kuka. Goge hawayen ki. Ta goge yace yauwa yanzu ki je ki kwanta ki huta.

Ta mike yace ta goge hawayen ta. Ta kara goge wa ya ce yauwa yar albarka.
Ta ce sai da safe.
Ya ce Allah kai mu.

Ta fice, dakin ta ta nufa ta fada saman gado ta cigaba da kuka har bacci ya dauke ta.

Bayan wata daya da faruwar haka, da dare kowa ya kwanta, Mummy na kwance saman gadon ta na alfarma tana ta sake a zuciyarta gamaida yar’ta da manaiman ta wadda duk cikin su ba ta iya ba ko daya.

Ta mike ta fita daga dakin ta ta shiga dakin Nur.

Lamp din da suke side drawer ta kunnan daya sannan ta zauna a kusa da kafarta tana kallen yar’ta ta cikin tausayi, mi za tayi ta fada mata ko ta kyale, ta dauki tsawon mintuna ta na zaune kusa da ita tana tuna rayuwar baya.

Chan ta yanke hukuncin tada ta. Ta daddaba ta tare da kiran sunan ta.
Cikin bacci ta amsa ta.

Mummy ta kara ambatan sunanan ta.
Nur ta budai idon ta, ganin Mummy ta kori baccin da ke idon ta. Ta tashi zaune ta nace wa Mummy

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now