Ana sauran one week tafiyar su Dr sa'ada ta zo gidan Asim ta duba lfy Halimatu ta bada medical report akan zata iya hawan jirgi.
Ita dai Halimatu bata san ina za su ba jira ta ke bayan fitar Dr sa'adah ta tambaye shi.
Ta na tafiya ta tamabye shi, "Habibi ina zamu ne da doctor ta ke cewa zan iya hawan jirgi?
Yayi karamin murmishi yace "Mai martaba zai aurar da jikar shi so zaku je bikin."
Ta ce "Shine kuma sai mun je a jirgi."
Ya ce "Eh mana tafiyar da ni sa."
Ta ce "A'a ni dai ina jin tsoro."
Dariya ta kubce mashi. Ta bata rai. Ya ce "I'm sorry ke ce da abin dariya minen abin jin tsoro da hawan jirgi. Infact an riga da an saman maki viza so you should prefer.
Ta ce "Kana nufin ni kadai ban da kai."
Ya ce "Eh mana ay da su Umma za ku.'Jin ban da shi ta kara tsorata ba abin da ya fara fadomata a rai irin wulakcin da zata tarass a chan.
Ta ce "Ni dai ba zan je ba tsoro nake kawai hakan nan mu fado, gaskiya ban zan je ba kuma ban da kai."
Ya kara yin wata dariya ya ce "Amirori, mine abin tsoro dan Allah kar ki bada mu. Gobe za mu je a ida processing na tafiyar ku."
Ta yi shiru zuciyar ta na hararo abubuwa da yawa.
Ganin haka yace "Habibty wai mine na jin tsoro, in sha Allah ba abin da zai samai ku, zaku je lfy ku dawo lfy after all flight ya fi safe a kan mota. Ki kwantar da hankalin ki."
Ta sauke ajiyar zuciya tana jin jina masa but kasan zuciyarta tana hararo abubuwa da yawa.
Washe gari bayan sun dawo daga wurin passport ta roke shi a aje ta a gidan su ta kwana biyu ba ta je ta duba lfyr su Umma ba.
Ya aminta da haka a ka aje ta shi kuma ya wuce kasuwa.
Ta yi sallama ta shigo ciki ba kowa a falfajiyar gidan ta wuce dakin tana sallama. Ta iske Umma na sallah.
Ita ma ta aje jikar ta da mayafinta ta fita waje tayi alwalla ta zo ta kabbara sallah bayan sun gama suka gaisa.
Umma ta ce "Masha Allah kin mika."
Halimatu ta dubi cikin ta ta ce "Umma ana gane wa?
Umma tayi murmishi ta ce "In ban da abin ki kin taba ganin an boye ciki."
Ta sauke karamar ajiyar zuciya ta ce "Umma shawara ki na zo naima."
Umma ta gyara kafarta da ta mike su ta dora daya kan daya. Ta ce "Lfy, sabani ki ka samu da mijin naki?
Ta girgiza mata kai ta ce "Umma Asim bai da damuwa kin san in da mtskl ta ta ke."
Umma ta ce "Yanzu kuma mi su ka maki."
Ta ce "Umma basu min komi ba sai rai na yana bani akwai mtsl."
Umma ta ce "Ki min dalla dalla ki dai na kauna kauna."
Ta ce "Umma za su yi biki nan da kwana 6 kuma nan da kwan uku za a tafi Borno, yayan Umma sarkin borno shi ke auran da autar shi, dani kuma za su tafi, umma rai na na bani in na bi su hankali na ba zai taba kwanta ba dole sai sun takule ni sai sun wulakanta ni."
Umma ta ce "Toh ke ina Ruwan ki da su, ay sai an kula kashi yake tsami."
Ta ce "Umma ko ban kula su ba sai sun samu maganar da za su yarfa min, umma nan su uku kadai sun ta kura min ina ga inna shiga cikin dangin su ni wlh ban so haka ba."
Umma ta ce "Sai ki tashi cikin dare ki gayawa Allah, sannan duk abinda za su miki kar ki kula su kar ma ki tanka su, kar kiyi abinda za a zage mu a kan ba mu baki tarbiya ba, ki zauna da su da zuciya daya zaman amana."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel