Chapter 55

13 3 0
                                    

Sai da gari ya ida waye wa bayan ya yi breakfast, kafin ya tafi kasuwa ya biya gidan su.

Yana shiga yayi katobara da mahaifin sa. Ya rinstuna ya gaishe shi. Mimakon Alhaji inuwa ya amsa sai dai yace "Kai daga yau kar ka kara kawo iyar ka da matsayinta mutanen gida na kar in sake ganin su ko kofar gidana."

Asim ya dubi mahaifin na sa cikin rashin fahimta.

Alhaji inuwa ya katse shi "Ka ji na gaya ma kar su sake zo min gida in ba haka ba daga kai har su na kore ku, kana cin albarkacin mahaifiyarka na inuwa ta in ba dan haka ba mi zanyi da kai, shashasha wuce ka ban wuri."

Ya wuce part din Umma tin daga kofa yake kiran sunan ta.
Umma da ke sama a parlourn ta ta ce "Asif ya fiye fittina" kafin ta xe
"Lfy ka ke kira na haka? Ta amsa shi da ga sama.

Ya karaso ciki Umma ta ce "Ohh daman kai ne ay na dauka Asif ne."

Ya karaso ya zauan tare da gaishe ta.
Ta amsa ta na tambayar shi lfy.

Ya ce "Umma ay na dauka sbd kukan ta ki ka maido ta ashe sbd wancen tsohon ne daman ay nima ba dan shi nake zuwa mashi gida in ba ki na gidan nan ko kallo ma ya ishe ni."

Umma ta kwabe shi "Kull kar in sake ji ka fadi haka shi din mahaifin ka ne."

Ya ce "Amma Umma dan yana mahaifina shi ke nan sai ya dinga ci min fuska bayan Amira har da karamar yarinya da bata san komi ba, shi ke nan gidan na sa bazan kara zuwa ba su ma ba za su kara zuwa ba in an hadu a waje an gaisa tin da haka yake."

Umma ta ce "A’a sbd da shi ba kun ki zuwa wuri na."

Safna da karasowar ta ce "Wan da bai ji Bari ba yaji hoho. Har gobe yarinyar nan ba zata chanza akan yanda ta ke ba matsiyaciya yar tallaka."

"Safna!
Umma ta daga mata tsawa. Kafin ta kara da "Wuce ki bamu wuri."

Ta ce "Umma ki cigaba da goya mashi baya muna nan zata raba ki da shi."
Daga haka ta koma dakin su.

Ya ce "Umma ba za su kara zuwa gidan nan ba dan na lura har abada ba za su taba son matata ba gashi kirkiriri sun shafawa Qawwama karar tsana ita mi ta masu."

Umma ta ce "Dan wa kake zuwa gidan nan?
Ba dan ni ka ke zuwa dan haka yanzu ma haka zaka cigaba da zuwa dan ni sannan shi mahaifin na ka ka cigaba da bashi girman shi ka kyale shi da kudin shi balle ma Allah ya rufa ma asiri ka na dogara da kanka ba tare da support din shi ay ka fi su hashim daman an ce ka ki danka duniya ta so shi ka so shi duniya ta ki ka.
Dan haka ka cigaba da naiman na kanka watara na sai lbr, kuma arzikin nan kai ma zaka yi shi wanda ya fi nashi kuma in sha Allah arzikin da Allah zai baka za ka taimaki talakkawa da su, Allah maku albarka gaba ki dayan ku.

Ya amsa da "Amin."
Umma ta ce "Ka ma saki ran ka."

Ya ce "Toh, Umma ni zan wuce kasuwa." Ya mike.

Umma ta ce "Allah ya kiyaye." Ya amsa da amin ya wuce.

A adamwa Mummy ganin shiru yayi yawa gamai da Nur ta samaita a dakin ta ta na kwance da wayar ta a hannun ta.

Shigowar Mummy ya sa ta ta tashi zaune tana ambata sunan Mummy.
Mummy ta karaso ta zauna kusa da ita tana ce wa "Nur kina lfy, yana ga kwana biyu na ji ki shiru, ba walwala a tare da ke ko parlou baki fitowa balle waje?

Nur ta ce "Mummy tin da ki ka ban lbrn nan na kasa yarda da kai na, na kasa yarda da abinda ki ka fada min gani na ke tamkar a mafalki ne ba gaskiya ba ne, na kasa yarda ke da Daddy ba iyaye na bane. kun nuna miin soyyar da ba kowane yaro zai samu gata a wurin aynayin iyayen sa.

Mummy ta ce "Kull Nur, kar in sake jin mgnr nan a bakin ki yanda muka tona muka rufe haka ke ma dole ki tona ki rufe ta kar ma ki bari ta fita, a da kullun ina yiwa mahaifiyar ki addu’a yanzu ke ma zaki taya ni yi mata addu’ar nan. Dan haka kar ma ki sa wa ranki damuwa har wani yazo ya san gaskiyar.
Ta gyada mata kai.

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now