Haka suka tsaya har sai da yamma sannan ya falka. Ko da ya falka ya iske su a dakin ba wanda ya tankamawa.
Umma ta dubai shi ta tambaye shi ya jikin na sa. Ta ido ya bata amsa sannan ta ce "Allah kara sauki."
Har dare bai tankawa kowa ba. Dan har yanzu da oxgen a hancin sa.Bayan dare ya ja Asif ya ce wa Umma ta koma gida zai kwana da shi.
Umma ta ce "A'a bari dai in tsaya."
Zai yi magana sai ya kyale chan kuma sai ta ce "Shi kenan kuna bukatar wani abu?Ya amsa da "A'a."
Umma ta ce "Okay, Aysha tashi mu tafi."Aysha ta mike suka masu sallama suka koma ita da Aysha da buba dan Abdullahi ya riga da ya koma gida.
Umma na tafiya da minti 10 Asim ya tambayi wayar sa.
Asif ya tambaye shi mi zai yi da ita kai da baka da lfy.
Asim yayi murmishi ya ce "Small headache ne."
Asif yace kuma ya kwatar da kai har da oxygen."
Asim ya ce "Ka miko min waya ta."
Asif ya ce "Wa za ka kira, kai da baka da lfy."Asim ya roke shi da Allah. Tuna da maganar Dr hakan ya sa ya mika mashi wayar ya na tambayar shi wa xa ka kira?
Asim ya amshi wayar yayi scrowling har wurin number Halimatu sannnan yayi dailing wayar a kashe. Ya kara kira wayar a kashe.
Asif ya tambaye shi "Wayar wa ce ce a kashe?
Asim ya aje wayar bai ce mashi komi ba ya lumshe idon sa ya budai sannan ya tambayi Asif mi Dr y ace.
Asif ya ce "You got heart attack na san kuma sbd waccen yarinyar ce ni har na fara jin haushin ta mtsww."
Asim ya dubai shi ya ce "Asif ke nan soyayar da ka ke yi ba soyayay ba ce face kanzan kuraige, ba kasan mi cece soyaya ba, ba kasan zafin ta ba balle dadin ta."
Asif yayi karamin tsaki ya ce "Zai fi ka ma baiwa zuciyar ka hakuri ka san abin da ba zaka samu ba ka wani dage sai ka sota. Dr nawfal cewa yayi dazun na da ba akawo ka da wuri ba da at any moment zuciyar ka zata iya bugawa, sai ka cigaba da son ta tin da daman baka damu da niba baka damu da Umma you only love her. Ko ajinkin ka ba ka damu da halin da zamu shiga ba ka cigaba har ta kai da sai ka rasa ranka. Ya ja tsaki ya kwanta saman kujer.
Asim bai ce mashi komi ba dan shi kan sa bai san wata irin soyayar da yake wa Halimatu ba gashi da ya tuno da abinda ta mashi jiya sai ya ji zuciyar sa ta kara raunana.
Allulan baccin da a ka mashi ita ta sa shi bacci da ba dan haka ba yau ma da ya kwanta ya na tunanin
A bangaren Halimatu da safe ta je gidan aikin ta ta dawo da yamma ta wuce islamiya.
Sai da ta dawo islamiya ta tuna abinda ta yi mashi jiya duk sai ta ji ba dadi musanman yanda ya tsaya jiran ta. Ta yi kudirta da ya zo yau zata bashi hakuri sai dai tin da ta gama sallah Magriba ta ke jiran shi amma yau shiru har a ka gama isha'I bai zo ba har su malan Yakubu suka dawo gida bai zo ba kuma bai naimai ta ba hakan nan ta ji gaban ta yana faduwa tabbass ta bata mashi rai abin da ta mashi bata kyauta ba. Ta kira shi ko kar ta kira haka ta tsaya tana contemplating har wayar ta mutu kasancewa tin jiya da dare da suka dauke huta ba su maido ba har dare. Haka ta kwanta da guiltiness.
Washe gari bayan ta gama abin da ta ke ta wuce gidan Mummy dan yi mata aiki.
Ta na cikin mopping parlourn. Mummy da ke zaune saman kujera Yasmin kuma na kwance saman kujera. Mummy ta ce "Yasmin kira min harira."
Yasmin ta kalli Mummy ta ce "Mummy Halimatu ta kirata ba na." Ta ida maganar ta na hararen halimatu.
Mummy ta ce "Bi ki ga aiki ta ke ba."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
Roman d'amourLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel