Da cikin ta ya shiga watan haihuwa ta roke shi Asee ta zo ta dinga kama mata aiki, musanman yanzu da Qawwama ta shiga mkrt ga kuma kullun cikin ciwo ta ke. Ya ce mata sai yayi tunani.
Da jin haka ta yi shiru karshe ma komawa daki tayi. Takaicin komi ya ishe ta ko sau daya bata taba tunanin Asim zai yi fushi da ita irin haka zai rike ta a rai har na tsawon watanni. Kunsan duk dare sai tayi kukan dan sam bata jin dadin zaman su na yanzu ina ma ace bata yi planning din ba.
Bayan kwana biyu da ta mashi mgn ya je gidan su ya roki alfarmar a bashi Asee ta dinga taimakawa Halimatu musanman aikace aikace na azumi tin da ya gabato.
Malan ya kubu ya amince Asim ya mashi godiya.
Kafin ya dawo gida Asee har ta kira Halimatu ta bata lbrn. Halimatu ta ji dadin haka. Da Asim ya dawo ta mashi godiya.Washe gari Asee ta dawo gidan da zama na dan wani lokaci. Da zuwan Asee ta dan samu sauki da kuma jin dadi ganin Asim na sakan mata fuska ba kamar da ba.
Da safe Asee zata shirya Qawwama ita kuma ta masu brekasat bayan Asim da Qawwama sun fita Asee zata gyara gidan har ma tayi abincin rana.
Da shigowar ramadana, ku san Asee ke komi na gida. Ita kuma halimatu tin da tayi na farko da na biyu bata kara yi ba domin yana galabaitar da ita sai dai ta ciyar.
An dau azumi na sha shidda wadda ranar ta yi niyar azumi sai dai kuma Allah bai yi zata yi shi ba.
Lfyl ta gama safur tayi sallah ta dan kwanta kafin gari ya waye, kwanciyar nan da tayi nakuda ta taso mata, haka ta jure tin da ta san doguwar nakuda garai ta kuma ba haihuwar ce ba.
Har gari ya waye, Asim zai fita kasuwa ya kirata. Tana gudan dakin wanda yanzu ta ke kwana ita da Qawwama da Asee. Ta amsa sannan ta mike tana jin nauyin tafiyar ta fito ta iske Asee na share parlourn ta ce "Asee sannu da aiki."
Asee ta ce "Yauwa har kin tashi ya jikin na ki?
Halimatu ta amsa da sauki. Ta shiga dakin Asim, tana sallama.
Ya amsa.Ta karaso ta gaishe shi ya amsa sannan ta zauna saman gado dan ba zata juri tsayuba.
Duba da yanayin ta ya tambaye ta ya jikin naki?
Ta amsa da sauki.Ya ce "Ni zan wuce kasuwa akwai abin da kuke so ne?
Ta amsa da "Eh."Ya kalle ta ya tambaya "Anya kina lfy ko za ku je asibiti?
Ta ce "Ina tunanin kamar nakuda ce ban so kuma na je su ce ba ita ba ce."
Ya ce "Toh shi ke nan ki rubuto min abuwan da za a siya."
Ta amsa mashi da toh.Ya gyara hular shi yace na tafi.
Ta ce "Allah kiyaye a dawo lfy."
Ya amsa da Amin ya wuce.Ya na fita ta tsaya a dakin cikin ta na ta murdawa ganin ya na dadda ciwo ta kira shi wanda isar shi ke nan.
Ya na dauka ta ce "Habibi nakuda ta zo haihuwar ta zo dan Allah ka zo mu je asibiti."
Asim da jin haka hankalin shi ya tashi yace shi ke nan gani nan zuwa ku shirya. Ta amsa mashi da toh.
Ko zama bai yi ba ya tsaida adaidaita ya wuce ma'ikatar su Asif, akan hanya ya kira shi ya ce mashi zai zo ya ari motar shi ya kai Halimatu asibiti.
Ya na isa ko ciki bai shiga ba ya amshi key din motar a hannun shi daman ya fito waje yana jiran karasowar sa.
Ya mashi addu'ar Allah sauke ta lfy. Ya amsa da Amin.
Ya budai motar ya shiga ya koma gidan da sauri. Ya na isa ya fita da sauri ya budai gate din ya shigo da motar ya fita ya rufe gate din.
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomansaLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel