Chapter 62

3 0 0
                                    

Halimatu ta dubai shi da mamaki dan ko sau daya bata yi tunanin zai sa sunana ta ba ko da yake sunanna ta sunnan mahaifiyar shi.

Ta ambaci sunan sa. Ya kalle ta. Ta rike kunnen ta tana ce wa "Da fatan na wanke laifi na, zaka dai na fushi da ni."

Murmishi yayi kafin yace "Sai jiya na gane dalilin ki na yin haka, haihuwa ta isa kadai ta kara wa mutun Imani, Allah biya ku da gidan Aljanna. Allah ya sama ku juriyar da mu ba mu da ita."

Ta rungumai shi ta nace wa "Habibi ina son ka dan Allah ko sau daya kar ka rage son da ka ke min dan Allah kar ka ra fushi da ni musanmana irin wannan."

Ya rungumai ta ya na ce wa "Bazan kara ba kiyi hkr."

Ta dago ta nace wa "Sunnan ta Halimatu toh wani sunan za a ce mata?

Ya dubi jaririyar yace suna mai dadi mai ma’ana domin ta na dauke da sunan ki da kuma na Umma.

Fatan na ta dauko kyawawan halin ki da na Umma amma banda sanyin ki dan na ga alamun Qawwama ta dauko shi." Ya ida cikin wasa.

Ta ce "A kirata da sadiyar ta."
Ya ce "No ban da sadiya wani suna dai."
Ta ce "Toh Sawwama."

Ya maimaita "Sawwama kuma, a'a sunan bai yi dadi ba."

Ta yi murmishi ta ce "Amma sunan na da ma’ana mai yawan azumi kuma ka ga cikin azumi na haifeta."

Ya ce "A’a bai yi ba."
Ta ce "Toh siyama?

Ya dan yi shiru kafin yace "Da sauki amma zan naima mata suna mai dadi mai ma’ana."

Ta kalli zoben da ya bata da haihuwar Qawwama ta ce "Ka ga abinda ya bani juriya da hkr lokutan da ka chanza min."

Ya dubi hannun ta tana jujjuya zoben.
Ya ce "Shiyasa nace kar ki cire shi duk lokacin da ki ke bakin ciki za ki samu farin ciki bayan kin tuna da ranar da ki ka fara zama uwa."

Ta ce "Shiyasa a kullun da ka bata min rai da na kali zoben sai na ji baccin ran ya tafi."

Ya ja hanncin ta kafin  ya ce "Yau ma na kawo miki kyauta amma ba zobe ba ce."

Cikin murna ta tambaye shi minene.
Ya ce "Bai karaso ba."

Qawwama ta shigo tare da ambatan sunan sa.

Asim ya dubai ta ya ce "Princess."

Ta karaso tana ce wa "Abi bacci zan yi. ina zan kwanta ina baby zata kwanta?

Asim yace "Sai kin fadi."

Ta ce "Toh ni da kai da baby a nan, Ammi da Aunty Asiya a chan."

Asim yayi karamar dariya ya ce "Haka za a yi."

Ta hau gadon tana ce wa "Ammi sai da safe."

Ammi ta dubai ta ta ce a "Chan zaki kwana."

Ta ce "A’a ni a nan zan kwana da Abi na da kuma baby na."

Asim ya dubi Halimatu ya ce "Kinga ki bar mu mu kwana a nan ki je ki kwana da Aunty Asiya".

Ta mike zata dau ki jaririyar, Qawwama ta saki ihu tana ce wa "Abi zata daukar mana baby."

Asim ya amshe ta yace "Kin ga ki bar mana kayan mu ki je ku kwanta mu ma mu kwanta."

Halimatu ta ce "Da kan ka zaka maido min ita." Ta wuce.

Qawwama ta ce" Abi bacci zan yi karr ka bari Ammi ta dauke ni ta mai da ni chan."

Asim ya ce "Ba za ta yi ba."

Ta kwantar da kanta saman pillow. Ya ce "Baki yi addu’a ba.'

Ta tashi zaune ta na ce wa ya ma. Ya tuna mata tayi ta shafe jikin ta sanann ta kwanta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: a day ago ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now