Assalamu alaikum ina masu yin sana'ar hanu ta gida har ma da ta shago. Ina masu so su habaka kasuwan su daga karamin mataki zuwa babban mataki
Ina masu son sun samu customers, na gaske ba masu ce wa sai ba ji k.Kwantar da hankalin k nisa ta zo kusa kina daga gida za ki iya tallata kayan k wurare wurare da wayar hannun ki, ki na zaune batare da kin ba kan ki wahala ba zaki tallata kayan ki cikin sauki kuma za ki samu customers. Har ma ki samu masu wholeseler da kan k
Mun kirkiri class mai su na enterprenuashin sales bosters. Duk mai ra ayin shiga ko kuma son karin bayani k tuntubai su ta 09162382018
Ma su son a tallata masu kayan da su ke saidawa a media wato sponsor add su ma suna iya min mgn ta number ta 081070456601.
Washe gari bai je wurin ta ba sai dai da dare ya kira ta suka gaisa. Ba su wani jima ba.
Through out this week bai je gidan su ba sai dai a waya. Ranar Friday, da dare Abba ya tara su a parlour, yan’an sa da matan ya tambayi Asim ina kudin sadakin.
Kowannan su ya yi mamaki jin haka, Asim ya ce "Abba su nan."
Abba ya ce "Ka turo min su a account."
Ba bata lokaci ya dau wayar shi ya tura wa Abba 100k kamar yanda abba ya ce mashi.Kudin na shigowa Abba ya ce "Yauwa sadakin sun shigo kuma zancen da nake ma dazu bayan an sauko daga masallaci a ka daura auren ka da haulat yar gidan Ambassador Sadiq Ya’u.
Fara’ar da ke fuskar shi ta yaye nan ta ke zuciyar sa ta far bugawa da karfi.
Ambaton Allah ya fara yi yana kokarin daidaita lumfashin sa.
Umma daman ranta bai bata Abba zai aura mashi Halimatu ba.
Hajiya shafa da sauran mutane mamaki suke buba, Asif abin da suke tsoro kenan Ayan kuma ya san hakan za ta faru.
Asim ya dubi mahaifin na sa da raunanan idanu ya ce "Abba ka isa da ni kai mahaifi na ne bazan ki hukunci ka ba amma ka sani abin da ka ke ba daidai ba ne cutarwa da kake wa ya’an ka ba daidai ba ne, musanman mata, amma duniya ce gata ga ka."
Daga haka ya mike ya bar parlourn with so much hearted of his father, dama ya mutu ba tare da ya ga wannna bakin cikin ranar ba Ya wuce part din su.
Ya na mikewa Asif ma ya mike Abba ya kirashi ko tsayawa bai yi ba ya bi dan uwansa.
Ayan shima ya mike ya ce "Abba Allah ya wadata ka amma ba ka godaiba tsorona ka guji ranar da Allah zai amshe su ko dan hakkin ya’yan ka mata life is not trusted. Da haka ya wuce ya bi bayan su.
Ba wanda ya ce komi da daya da biyu da uku aka din ga fita har a ka bar hajiya shafa kadai ita ma ta ce "Alhaji ina jiye ma tsoran ranar da yarannan za su ju ya ma baya because of your selfies reason ka godaiwa Allah kaf din su ba mai saba maka amma kakiyayi ranar da za su juya ma baya.
Daga haka ita ma ta bi bayan su a ka bar shi.
Ko digon tausayi ko bakin cikin haka babu a zuciyarsa dan duniya ta riga da ta mashi daurin da ba ya jin kira sai dai a bishi da addu'a.
Asim ya na isa dakin su ya rufe da mukuli ya zauna kan gado zuciyarasa cike da bakin cikin mahaifin sa ina ma ace ya mutu kafin yau, ina ma ace Alhaji Inuwa bai zama mahaifin sa, yanzu shi ke nan yara bu da ita, ina, a’a hakan ba zai yu ba ay shi namiji ne zai iya auran mace sama da daya sai na aure ta sai dai yayi abin da zai yi ba dai ya auran min wata ba saboda selfishiness irin na sa, ya ji da shi amma Halimatu sai na aure ta.
Asif da ke waje ya roke shi da Allah da ya budai mashi kofa Asim ya kiya hatta Umma da ta zo bai budai kofar ba bai yi masu mgn ba.
Wayar shi ya jawo ya kira Halimatu bayan sun gaisa ya ce da ita ta fadi mai mi mutun ya kamata yayi in ya na cikin bakin ciki.
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel