Chapter 26

16 3 0
                                    

A ka gama bud  kan wurin 9 Asif da ubaidu yamai da su gida.

Ta yi wanka tayi sallah isha’I ta ci abinci sannan ta chanza kaya shigar atanfa riga da zane sanna alkyaba da ta sa bamai ce wa ita din ba jinin sarauta ba ce dan alkabba ba karamin hawa tayi da fuskarta ba.

A ka shiga da ita dakin malan Yakubu, malan Yakubu, malan kabiru umma da hadiza su ka mata nasiha sannan a ka fito da ita, haka amaryar ta taka har babban layi inda mota zata iya shiga dan layin su mota ba ta shiga.

Ita da hadiza da malan yakubu a motar Asif sai kuma motar ubaidu Nawfal da ta Ayan a ka kawashi suran mutane. A ka yi comboy a ka kaita gidan ta.

Masha Allah karamin gida ne saidai an kyawata shi.

Gida ne mai two bedroom single parlour kitchen da kuma store all the bedroom there's tolet inside.

Ginin dai zamani kuma ya sha furniture daidai da zamani.

Ko wannan su santin gidan Halimatu yake.

Yaran zamani da basu kuka ko dikon kwala babu a idon halimatu fuskar ta wanshar dan har da ita ake raha.

Wurin 11 saura Asif ya masu sallama ya shigo dakin ya isar masu da sakon ango zai shigo yace a bar mai matar shi.(a bar mai kayantsaa😂)

Nusaiba tayi darya ta ce "Muma yanzu za mu tafi wane mu mu tsaya."

Shatu ta ce "Halima yi na yi nayi bari na bari."

Harraa ta wulla wa shatu a sirran ce. Su ka mike suka bar dakin, na parlour ma su ka fita kowa ya shiga mota.
Asim kuma ya masu godiya sanna ya masu sallama dan shi ba wani siyan baki.  Suna wuce wa ya shigo ciki ya rufe gate din sannan ya karaso ciki ya mata sallama.
Ta amsa.

Ya karaso saman gadon ya na cewa a budai min fuskar bana.

Ta girgiza kan ta.

Ya ce "Toh ko nan ma sai na siye ta irin na dazu."

Ta budai fuskarta ta na sakan mashi kyawatancen murmishi.

Ya ce "Masha Allah wifey si dai fah kin ban mamaki."

Ta mashi alamar tanbaya
Ya ce "Na dauka zan zo in iske ki kina kuka."

Ta dan Harare shi kafin ta ce "Kukan mi zan yi??

Ya ce "Ahh unblieable ko da yake kin sha kukan ki ranar da a ka daura yanzu kam ba sai kin yi ba."

Ta sa tafukan hannun ta wanda suke dauke da jan lalle bayan hannun ta kuma yana dauke da bakin lale ta rufe da fuskarta ta fara kukan karya.

Yayi karamar dariya ya ce "Ke koh you can pretend. Yanzu stand up let pry and thank to Allah.

Zai mike ta rike hannun shi ya dubi hannun ta da mamaki.

Ta ce "Ba ka yi addu'ar da miji ya kamata yayiwa matar shi ba."

Ya ce "Ni ban san ta ba koya min sai na yi."

Ta ce "Za ka rike goshi na sai ka fada;

Allaahuma innee as’aluka khayrahaa wa khayra ma jabaltahaa alayh, wa a’oodhu bika min sharriha wa sharri ma jabaltahaa alayh."

Ta na idawa ya ce "Ni da ba balarabai ba ta ya zan iya fadin haka."

Tayi murmishi ta ce "Ay ba wahala."

Ya ce "A'a yanzu dai zaki fadi na fadi."

Ya ida maganar yana kai hannun shi bisa goshin ta. Ta fara karanta mashi adduar yana fadi har ta kamma. Sanna ya ce barakallahu fiki. Malama ta what next.

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now