chapter 34

8 3 0
                                    

Bayan Aunty Salma ta fito ta tambaye ta ina Amira.

Ko kallo bata samu ba balle amsa.
Aunty salma ta ce "Aunty zulaiha baki kyautawa abinda ki ke yi ita ma fah mutun ce irin mu."

Aunty zulaiha ta daga mata tsawa  "Yi min shiru."

Aunty salma ta ja bakin ta tayi shiru. Ta sa kayan bacci sanan ta fita parloun ta iske halima na waya ko tantama bata yi ba ta san da Asim ta ke waya.

Ta fita babban parloun ganin mutane a parlourn ya sa ta juyo wa ta dawo wurin halimatu ta na ce wa Asim, "Kai Asim ka kyale mana yar’uwa bacci ma ba za ka bar ta tayi ba."

Asim yayi murmishi yace wa Halimatu "Aunty salma ce."

Halimatu ba ta ce mashi komi sai dai mamakin da aunty salam ta bata ganin ta san da Asim ta ke waya.

Ya ce "Bari na kashe zan kira in dan sun kwanta dan yanzu zata samin ido. Good night."

Ta ce "Allah kaimu."
Ta aje wayar.

Fira su ka yi har wurin 12 na dare sannan Aunty Salma ta fita parlourn ta san bakin sun tafi, bata iske kowa a wurin ba ta wuce dakin Umma, ta fada mata abinda aunty zulaiha ta yi wa Halimatu.

Umma ta ce ta kira mata Halimatu. Ta fita ta kira Halimatu su ka karaso ciki Jmma ta ce wa aunty salma "Amira zata kwana anan ke da zulaiha sai ku kwana dakin ku."

Salma ba karamin mamaki tayi ba, Umma zata kwana da wani a daki, har ta bar dakin abin ya daure mata kai.

Itama halimatu ga kunya duk ta rufe ta kwana da sirika a daki Umma kuwa ce mata ta ke "Fell free I’m your mom."

Ko da Asim ya kira kin dagawa tayi ta muting din wayar ta.

Salma da ta koma daki bata fadawa zulaiha ga inda Halimatu zata kwana dan ta na shigowa addu'a tayi ta kwanta.

A bangern Asim ya kira har sau uku bata daga ba sai ya kyale ganin 12 tayi shima ya kwanta sai dai kewar ta ta hana shi bacci, da ta na nan da yayi motsi zai rungumi abin sa.

Itama haka duk kewar junan su ya hana su samun ishashen bacci har gari ya waye.

Bayan sun yi sallah asuba Umma ta sa ta ta koma dan yana daga cikin karamin aikin halimatu ta fita ta ce zata yi aiki, su ka koma bacci ba ta tashi ba dai 11 saura.

Kafin ta tashi Asim ya kira bai samai ta ba ya kira Aunty Salma ta ce mashi bacci ta ke, ya ce yauwa Aunty Salam dan Allah a bata kulawa da kyau kin ga ba ita kadai ce ba.

Aunty salma ta ce "Aje ni kayi ko kuma ni na aje ta."

Yayi karamar dariya ya ce "Ba ko daya ni dai da Allah na hada ki."

Ta ce "Shi ke nan in ta tashi zan ce mata ka kira. "

Yayi breakfast ya fita kasuwa shi daman yin girki bai bashi wahala dan ko a gida a ka dafa abinda bai so bai jin gyandar ya shiga kitchen ya dafa abinda ran sa ya ke so.

Halimatu ta na tashi tayi mika ta tashi zaune ta godai wa Allah da ya tasar da ita.

Sai lokacin ta tuna ba a gida ta kwana ba. Ta juya gefen ta ta ga ba umma. Da sauri ta mike ta na ce wa "O ni haliamtu wata irin rishin kunya ce sirika ta riga ki tashi."

Ta sauka daga gadon, cikin sauri ta gyara shi sanan ta fito kasancewa dakin gyara yake dan kafin ta tashi mai aiki ta shiga ta kauda kayan ana jiran halimatu ta tashi a share dakin.

Ta fito nan main parlourn ta iske Umma da wasu mutane.

Ta durkusa ta gaishe su. Su ka amsa umma ta ce "Ki je ki shirya ki zo ki ci abinci in kuma a kai maki chan dakin?

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now