Isma'il bai dawo daidai ba har sai da ayana ta yi kwana uku da rasuwa a lokacin ya tambayi matar shi a ka ce mashi tayi tafiya ya tambayi ina ta je ba ta tambaye shi ba.
Hajiya bilki ta ce baka lfy ka huta,
Ya ce "A'a Mammy ina zata je ba tare da ta tambaye niba musanman ta san ban lfy."Hajiya bilki ta ce "Na aike ta egypt ita da Noorie za su min sayyar wasu kaya."
Ya ce "Mammy ay da an fada min ina Mahir?
Hajiya ta ce "Yana chan gidan su nan da sati biyu za su dawo."
Mahir kuma ya gaji da tambayar mummy ya hakura yana jirn ranar dawowarta.
Sati daya da mutuwar ta a ka sallamai shi kuma bai fasa san giya ba ko da ya ce ya daina bai iyawa har ya hakura da tuba dan ko da yayi sai ya koma.
Shiru dai bai ji daga matar shi ba duk da sai yadawo cikin hayyacinsa yake tunawa da ita da dan shi.
Ya tambayi mammy lfy ya ji su shiru Alhaji bilyaminu ya fito yace mashi matar shi ta rasu.
Mumunar dakawa zuciyar shi tayi daga bisani yayi murmiishi ya ce "That should be a joke."
Alhaji bilyaminu ya ce "A na wasa da zancen mutuwa ne?
Ya ce "No dad but that can't be possible dan Allah a ma bar zancen mutuwa."
Mammy ta ce "Gaskiyar ke nan matar ka ta rasu kuma ana zargin ka da kashe ta."
What! Ya furta da sauri.
Alhaji bilyaminu ya lbrt mashi abin da ya faru. Ya mike ba tare da yace masu komi ba ya fita yadau motar shi bai tsaya ko ina ba sai gidan alhaji inuwa ya shiga part din hajiya shafa kasancewa da rana duka matasan gidan su fita Mahir ma yana mkrt.
Hajiya shafa ta fito ya gaishe ta sannan ya bata hkr a kan yayi jinya sai yau suke fada mashi ta rasu.
Har yagama zantukan sa Hajiya ba ta ce mashi komi ba ta mike ta wuce daki ta barshi a parlourn. Bakinci da takaici sun cika mashi zuciya ina ma ace shi ya mutu ba ita ba. Ko gawar matar shi bai gani ba.
Ya mike jikin sa ba kwari ya bar gidan da kar ya mai da kan shi gida ya wuce underground ya shiga parlourn shi ya bude fridge ya dauko beer jar ya balla murfen ya fara sha ko kiftawa babu har sai da ya shanye ta sanna ya zauna zuciyar sa cike ta ke da bakin ciki miyasa duk masoyan shi suke mutuwa yanzu har da matar shi ita ma ta rasu. Da ya tuna da mutuwar iyayen sa da kuma sanadiyar kawun na shi da matar kawun shi rayuwar shi ta lallace dan tabbass dukiyar shi ya ke so ba wai shi ba bai damu da ina yake zuwa ba mike damun sa da sauran su da ya tuna da abin duk sai ya ji ya tsani kan shi ina ma ace iyayen shi na raye ina ma ace mahaifiyar sa ko mahaifin shi na nan wanda zai kai kukan shi wurin shi ko wurin ta ina ma ace yana da masu share mashi yawaye masu yaye mashi damuwar shi giya da Ayana itace mai yin haka yanzu kuma babu ita duk yaji ya tsani rauywar shi dama shi ne ya rasu ya bar duniyar nan da takaicin ta da bakin cikin ta.
Ya mike ya budai friged din ya kara dauko wata ya budai yana sha ya na tuna mutuwar kanen sa da kanwarsa wadda suka riga shi mutuwa sbd sickle cell iyayen shi kuma hatsari sukayi sai ya zamo shi kadai ne.
Yana sheara 13 ya dawo wurin Alhaji Bilyamunu wanda ya bata shi da kudi shi kuma yayi contact da abokan banza suka sa shi a harkar maye har ta kai da ya zamo so addicted in bai sha ba bai jin dadi karshe ma har ranar auran na shi dare kafin ya dawo gida sai da ya bugu.
Bayan auran shi da Ayana ya fara tuba a kan ya daina sai dai ina ta riga da ta bi jikin sa zai yi wuya ya dai na. Ya bugar da kan shi har sai da ya suma.
Alhaji bilyaminu tin da fitar da yayi bai san ina ya je ba wani hali ya ke ba bai damu ba.
Mammy ganin shiru har kwana biyu ta biyo shawu a gidan shi ta iske shi kwance a bige.
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel