Page 7

3.6K 258 1
                                    

Zuhraa❤❤
           (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
          ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin


بسم الله الرحمن الرحيم


Page 7

Tafiya suke suna hira cikin farin ciki da niahad'i baza ka ta'ba cewa zuhra na tare da wani matsala ba, dandali suka nufa inda 'yan mata da samari suke tare wasu na gad'a wasu na hira da samarinsu wasu kuma na zazzaune gefen masu tallah suna cin abubuwan tallahn irinsu gyad'a, rake, d'an wake dade sauransu, roban gyad'a ne a hannun zuhra karasawa tayi ta samu dutse ta zauna a kai ta ajiye roban gyad'ar a gabanta tana kallon shatu da ta shige cikin 'yan rawa suna tayi se dariya zuhra keyi, sossai rawa ke burgeta ta iya ba wai bata iya ba kunya takeji tayi rawa a cikin jama'a amma mazari ce ita, "Salamu alaikum" taji Ance a kanta dagowa tayi tare da amsa sallaman da sauri ta tsugunnar da kanta kasa tana Jan gyale ta rufe fuskanta tana murmushi, saurayinta ne yayan shatu "'yan mata ina son gyad'a" ya fad'a yana murmushi, "toh zauna mana hamma na a tsaye zan baka gyad'ar"? Cewar zuhra tana cire dankwalin daga fuskanta.
Zama yayi suka fara hirar su ta masoya yana cin gyad'a har lokaci yaja, dubanta yayi tare da cewa "zuhra dare yayi ya kamata mu tafi gida haka" duban gyad'ar gabanta tayi tayi ciniki sossai amma be kare ba ta ce "uhm uhm hamma na sede in zaku tafi kada baba yayi fad'a amma nikam na koma da gyad'ar nan haka ai kashi na ya bushe" kallon gyad'ar yayi yace "amma naga sauran na hamsin ne guda biyar kenan kinfa yi ciniki ba na d'ari biyu bane kika zo dashi"? Tace "uhm hkne amma har yanzu baka san halin inna bane kasheni zatayi in na koma da wannan" kallonta yake cikin tausayawa yace "daga ganin alamu ma zuhra baki ci abincin dare ba ko"?
Tace "uhm amma in na koma za'a bani", girgiza kai yayi yace "in saya miki d'an wake"? Ta ce "uhm uhm hamma kaima kasan bazan iya cin abinci anan ba", dariya yayi yace "toh sarkin kunya kici gyad'ar in ma zaki iya cinyewa ma ki cinye xe d'an taimaka miki kafin ki koma gida", tace toh tare da bud'e robar ta fara cin gyad'ar da gudu shatu ta karaso tana murmushi tare da cewa "hamma minfu mi nyaman"(nima zanci) gidado yace "na kawarki ne duka ki roketa watakila ta tsammiki ko da shike ita ba marowaciya bace kamanki zata baki" 'bata fuska tayi tace "kai hamma ni d'in ce marowaciya?" Zuhra de murmushi kawai takeyi tana kallon su don burgeta sukeyi se taji ina ma tana da yaya.
Suna gama ci suka mike tare da karkad'e jiki suka nufi hanyar gida har suka isa suna hira suna dariya "jam wala"(mu kwana lafiya) shine abunda zuhra ta fad'a lokacin da suka iso kofar gidansu shatu ita ma kofar gidansu ta nufa tana lalu'ben bakin zaninta 'innalillahi wa innailaihi raji'un' shine abunda zuhra ke ta nanatawa tana dube dube kudin da hamma ya bata na karshe dama d'ari da hamsin na farkon da tayi se ta sa a cikin roban naira hamsin da ya bata daga baya kuma se ta murd'e a kasan zaninta Gashi ya fad'i, "na shiga uku" abunda zuhra ta fad'a kenan ajiye robar tayi waje da gudu ta duba kofar gidansu shatu har sun rufe, tana ta dube dube tana komawa baya ta kama hanyar dandali tayi nisa da tafiya taga inaaa ita kadai baza ta iya bin hanyar nan ba tana tsoro hanyar duhu gashi daji ne, gwara ta koma inma kashe ta inna zatayi ta kashe ta akan tabi hanyar nan wani abu yaje ya sameta, tayi sallama tare da kutsa kai cikin gidan tana sand'a kaman barauniya inna tayi charab ta rike hannunta tare da cewa "munafuka yanzu haka laifi kikayi shine kike tafiya kina sand'a ko?, maza maza bani gyad'a ko kud'i" zuhra ta tsugunna ta bud'e robar gyad'ar ta zuciyar ta na dukan tara tara ta ciro d'ari da hamsin ba mika mata, kar'ba tayi tare da kirgawa ta dubi zuhra tace "ina saura" zuhra tace "inna useni wadu munyel shede mai do'i ha lawol, mi tefi ko hatoi bo mi larai"( inna dan Allah kiyi hakuri kudin ya fad'i a hanya, na dudduba kuma ban gani ba) bata gama rufe baki ba inna ta rufe ta da duka zibgarta take kaman ta kama barawo gashi dare muryar zuhra ya karad'e kab unguwar sbd dare yayi nisa,
Ihu take na neman agaji cikin bacci baffa yaji ihun zuhra da sauri ya farka dama bacci 'barawo ne ya sace shi jira yake ta dawo kafin ya kwanta toh kuma se ihunta ya farkar dashi fita yayi da sauri ya kar'be ta tare da cewa "haba hanse wai ke wace iriyar marar imani ce da tausayi, wai sai yaushe zaki bar yarinyar nan ta sakata ta wala haba kinfa haihu bakya tsoro wata rana ama 'yarki haka, kin tura 'yar mutane tallah naki na kwance bata da aiki sai tara samari da rashin kunya tayi miki aikin gida tayi miki tallah be ishe ki ba ki kamata ki jibga wai se yaushe wannan iskancinnaki ze kare, nafa zuba miki ido ne kawai bafa wai tsoronki nake ji ba hanse ki kiyayi randa zaki gama turani bango fa". sossai hanse ta tsorata tasan malam yana da hakuri amma ka kiyayi zuciyar shi yau taga alamun rashin mutunci yake ji dashi don dazunnan ya kama jainabu ya jibga sbd banzan tara samari se wani cewa yake yarinya bata tafasa ba zata kone shekara tara amma tasan tara samari.
Hanse bata ce komai ba ta shige d'aki tana saka yadda zata ci uban zuhra don wallahi bata hakura ba kud'inta be sha a banza ba, baffa duban zuhra yayi da har yanzu hawaye take yace "kinci abincin dare kuwa"? 'Kad'a mishi kai tayi' yasan da hka shiyasa ya rage mata abincinshi yace "je d'aki na ki dauko kizo kici maza ki kwanta kinga gobe zaki fita kiwo da wuri" tace "toh baffa na gode" taje ta dauko taci ta sha ruwa ta shige d'aki.

Toh asuba ta gari hajiya zuhra 😊😊

Zuhraa❤❤Where stories live. Discover now