Zuhraa❤❤
(The flower)By:fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 35
Bayan sati d'aya
"Maami ta ce ki fara girki daga yau ta gama nata" shiru be ji an amsa ba har na mintuna 3 d'aga ido yayi ya kalle ta tabbas ta ji wato dan ta raina shi, shine yake magana ta manna mishi hauka? Gani yayi ta kara waya a kunnenta tare da cewa.....
"Hello dad ya kk?" Be ji me aka ce mata ba yaji tace cikin 'bata fuska "hmm yana nan daddy nace a turo min maids mana guda uku, am in need of them urgently plz" be ji me aka ce ba yaji tace "ohk thanks dad" tare da kashe wayanta......
Be kara kallonta ba yace "ban da tsarin d'aukan masu aiki a gidana" kafin ya rufe baki ta mike tare da cewa "nan kuma baka isa ba major ai tun kafin ka auro ni baka gayamin haka ba" harara ya zabga mata tare da cewa "ashe ma ni na auro ki?" Ta gane sarai magana ya gayamata ta kau da kai gefe tare da ta'be baki tace......
"Daddy ya ce the maids will be at the next available flight so banga wadda ya isa ya hanasu zuwa ba kuma su shiga gidan nan su min aiki, ai nima gida nane" da tsiwa take maganar be kalle ta yace "koh? Hmm" tare da mikewa ya shige d'akinshi.....
Fad'awa yayi kan gado tare da lumshe idonshi kanshi na sara mishi d'aga waya yayi ya kira Emanuel yana d'auka yace "don't yhu dare let anyone to my house without my consent and don't leave my wife out of the house no matter what"......
"Ohk sir" ema yace tare da hanging off na call d'in, mikewa Aliyu yayi a natse ya fad'a wanka a tsanake yake yin komai ya shirya cikin bakaken kaya, jeans da T-shirt baki ya d'auki agogonshi basaj black ya sa, ya d'auki black facing cap ya sa a kanshi ya hd'a da black timberland boots ya kwashi wayoyinshi ya fice......
Yana fita yaranshi suka taso hannu ya d'aga musu tare da nuna Emanuel karasawa ema yayi tare da sara mishi Aliyu be ce komai ba ya nuna mishi wata sport car baka me shegen kyau da hannu a take ema ya ciro keyn ya mika mishi, kar'ba yayi tare da fad'awa motan a take aka wangale masa get yaja a guje ya bar gidan......
Kai tsaye San hussain ya nufa a parking space d'insu yayi parking ya fito cikin tafiyarshi na issassun maza masu ji da kud'i da kyau ya shige cikin plazan, sayyayya ya fara ni na rasa me yake had'awa komai in ze d'auka guda uku yake d'auka pads packet ya saya se da ya cika basket d'in tab tukun ya juya ya nufi gurin biyan kud'i yaron da yake tura mishi kaya biye a bayanshi......
Atm card d'inshi ya cira ya mika musu ya juya ya nufi mota, zare kud'in su sukayi suka saka mishi kayan a Leda aka yaron shagon d'aya ya kai mishi, yana fita ya hange shi jingine a jikin motanshi yana danna waya, yana ganin yaron ya bud'e mota ya shige tare da bud'e ma yaron back sit na motan saka kayan yaron yayi, yazo dai-dai window d'in ya mikawa Aliyu Atm card d'inshi amsa yayi tare da zaro kud'i 'yan dubu dubu ya mikawa yaron.......
Tare da jan motanshi ya fice daga gurin a guje ko tsawaya jin godiyar yaron be yi ba, gidansu ya nufa tun daga nesa yake danna horn da gudu wani kurtu ya bud'e mishi get yaranshi na gidan su biyar suka taso tare da sara mai, babban cikinsu ya mikawa keyn motar tare da nuna mishi sit d'in baya ya gane me yake nufi da sauri ya kar'ba ya nufi bayan motan....
Shikuwa Aliyu part d'in Ammienshi ya nufa a parlor ya same 'yan matan suna zaune wasu na kallo wasu kuma a aikin danna waya a tare suka ce "a wari na hamma?" Kai ya d'aga musu suka sake gaishe shi hannu ya d'aga musu tare da hayewa sama ya nufi d'akin Ammie gadonta ya fad'a yana jin wayanshi na ringing ko kallon wayan be yi ba....