Page 46

4.4K 258 28
                                    

Zuhraa❤❤
          (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
         ('Yar mutan Adamawa)


Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 46

Tana shiga wanka tayo ta shirya cikin normal shiganta na gd hk tayi, don tayi alkawarin baza ta ta'ba jan hankalin Aliyu da jikinta ba sbd soyayya na gaskiya take so daga gareshi.........

Half gown ta saka dai-dai gwiwanta, jin motsi a waje yasa ta d'auki hijab d'inta babba har kasa ta saka, fita tayi don taga wanene, tana fita ta ga wani d'an saurayi na shirin shiga d'akin Aliyu ganin ba musulmi bne yasa ta mishi magana cikin harshen turanci "kai me zakayi ne?".......

Cikin ladabi yace "zan share d'akin ne ma'am" zaro ido tayi tukun ta gimtse fuskanta tace "baya bukata sbd da mata ya zo wannan karon, in ba damuwa ka je a chanza maka aiki..........

Godiya ya mata tukun ya fice, kitchen ta shiga nan ma namiji ta gani yana girki shima sallaman shi tayi bayan ya gaya mata za'a ma Oga abincin rana 2pm ake zuwa d'auka wani lokacin kuma yana zuwa da kanshi, tambayan shi tayi "kuma be fad'i abunda za'a dafa ba?" Yace "ai Oga komai kika dafa ze ci in har sunan shi abinci" gyad'a kai tayi shikuma ya fice............

Yana tafiya ta haura sama, "wow ashe saman ma yafi kyau" parlor ne babba shima da d'akuna hud'u da kitchen se dining area, d'akin farko ta fara bud'ewa daga daman ta, a share yake fes amma ba komai ciki wadda yake fuskan tan shi daga hagunta ta bud'e.....

Zaro ido tayi cikin farin ciki ta daka tsalle tare da sake siririn ihu, best colour d'inta, kowa ce mata yake blue colourn maza ne amma ita bata damu ba tana son kayan ta, d'akin irin me angle d'in nan ne komai na cikinshi sky blue da fari, gadon an sashi a angle d'aya se wardrobe d'in gadon shima a angle yake se dressing mirror daga gurin window table ne da kujerun shi guda biyu.......

Daga gefen wardrobe d'in taga lefen ta akwati sha biyu masu kyau su ma sky blue ne da adon fari, sossai d'akin ya burge ta ita kam gaskiya sama zata hauro, don d'akinta na kasa normal room ne ba me angle ba kuma kayan d'akin coffee color ne, fita tayi tana murna wai yanzu gidan nan nata ne cikin jin daad'i ta bude d'akin gefen ta........

"Nan ne kenan asalin d'akin shi" a fili tayi maganan dakin ma sak kaman nata na saman amma se de komai white ne a d'akin har bedsheets da akayi laying white ne, fita tayi ta bud'e wadda yake fuskan tar d'akin shi, nan kuma ta'be baki tayi tana girgiza kai d'akin ya fi ko wanne girma a gidan ko wani lungu da sako na d'akin kayan motsa jiki ne wato gym d'inshi kenan.......

Jawo kofar tayi ta fita zuwa kitchen komai ya mata kyau a gidan data bud'e store kuwa kayan abincin da ta gani se da ya bata tsoro wannan ai se su shekara biyu be kare ba, a fili tace "Allah sarki baffa na ina ma kana raye" hawaye ne ya gangaro mata sharewa tayi ta fito ta sauka kasa.......

D'akin shi na kasa ta bud'e shima normal room ne kuma colourn irin nata na kasan ne, da alamu a ciki ya kwana don gadon ba a shimfid'e ba shiga tayi ta gyare d'akin tsab tayi moping dayake duk d'akunan tiles ne a kasan bayan ta gama ta d'auki akwatinshi ta haura sama dashi bayan ta bud'e wardrobe ba wani kayan kirki tana zuwa saman d'akin shi ta kai tare da bud'e wardrobe d'in d'akin.....

Nan ne taga asalin kayayyakin shi sbd drowern cike yake da kayanshi tab ajiye akwatin tayi da nufin in ta gama abinci se ta cire mishi kayan ciki ta shirya a drowern, sake komawa kasa tayi ta d'auko akwatinta da suka taho dashi ta kawo d'akinta na sama, kitchen d'in kasa ta shiga taga kayan ciki be kai na sama ba fita tayi ta koma saman.........

Babu abunda babu a fridge d'in kitchen d'in, tuwo ta d'aura mishi sbd taji an ce yana son tuwo, tuwon shinkafa tayi da miyan ku'bewa bushashe yaji kifi da nama taso yin d'anye ne amma babu kuma bata tunanin za'a samu a kusa tana gamawa ta had'a mishi zobo ta sa a fridge.....  .

Zuhraa❤❤Où les histoires vivent. Découvrez maintenant