Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 36
Yana fita garden ya nufa yana kuma tunanin hali irin na Ayush kuma yana mamakin me yasa be iya d'aukan tsatsauran mataki a kanta Allah ya taimake shi bata tona mishi asiri ba da yau be san yadda ze yi ba sbd kunya hmmm......
Kasan grass carpet me laushi ya samu ya kwanta idonshi na kallon sama, tunani yake yi kala kala har da wadda be yi niyya ba kuma be fatan yayi, motsi yaji a d'an gefenshi kuma yaji numfashin mutum, mikewa yayi a natse ya tunkari inda yake jin motsin kai tsaye......
Dube dube ya fara be ga kowa ba se kuma yaji numfashin kamar a saman bishiya d'aga kai yayi, baki ya sake ganin ta kwance a saman bishiya tana baccinta hankalinta kwance mamaki ne ya kama shi me haka? Se kace ba d'aki a gidan........
wayanshi ya fiddo ya fara d'aukanta photo, fuskanta fayau da shi tana baccinta cikin kwanciyar hankali, se da ya mata kusan kala biyar abunda ba sabon shi ba be ma iya ba gani kawai yakeyi anayi, Wani irin juyi da yaga tayi tayo kasa ne yasa shi sake wayan cikin zafin nama ya taro ta ta fad'a hannunshi........
D'an siririn ihu ta sake tare da amabatar sunan Allah, force da ta taho dashine yasa sukayi kasa baki d'aya suka fad'i shine a kasa ita kuma a saman shi idanun ta a runste ta sadakar yau kam ta gama karyewa ko ma mutuwa gabad'aya se taji an taro ta godiya ta fara yiwa Allah da kuma wadda ya taro tan.......
"Ya salam" ta furta a hankali jin kamshin turarenshi "na shiga uku nayi gudun gara.... Na fad'a a zago, shikennan tawa ta kare" murmushi ne ya su'buce mishi dariya sossai ya kama shi amma se ya danne a hankali ta bud'e idonta da sauri ya sha kunu.....
Idonta ne ya fad'a cikin nashi zaro mata nasa yayi tare da hararar ta, da sauri ta mike daga jikinshi tare da dukar da kanta kasa shima mikewa yayi ya matso dab da ita cikin husky voice d'inshi da son kara tsoratar da ita yace.....
"Wa yace ki fad'o jikina? Tukuna ma me ya kai ki bacci a kan bishiya ba d'akuna a gidan nan ne?" Ya karasa da d'an tsawa, daburcewa tayi tare da zaro manyan idanunta tana d'an juyasu a hankali cikin sanyin muryanta tace "Kayi haa... kuri, bazan sakeeee... ba"......
Sossai ta burge shi ganin yadda take magana kaman da shagwa'ba da d'an sakalci da kuma yadda take zazzare ido kaman an kama 'barawo, shagala yayi da kallonta ita kuma ta d'auka, tunanin hukuncin da ze mata yake tuno Wani abu tayi tace cikin sauri "a gurin fa ina bacci kan bishiya kuma bana fad'uwa kuma shatu da gidado ma sheda ne"........
Ta karasa da turo baki ta'be baki yayi irin I don't care d'in nan se kuma yace "waye shi?" Tace "yayan gidado ne kuma saurayi n......" Kasa karasawa tayi ganin mugun kallon da yake jefan ta da shi, d'aga hannu yayi kaman ze mare ta da sauri ta runtse ido tare da kama kunne alamun ban hakuri a lokaci d'aya kuma hawaye ya gangaro mata.......
Shiru taji ba'a yi dukan ba a hankali ta bud'e ido chan ta hange shi yayi nisa abunshi da tafiya kuma part d'in maami ya nufa, ko me yasa ya fasa dukan? Murmushi tayi ta juya ta nufi part d'in Ammie....
********
Ta bangaren Ammie kuwa maami ta bi d'akinta suka fara tattaunawa akan halin matar d'ansu, sossai hankalin Ammie yake a tashe ta fi kowa sanin waye Aliyu se yarinyar nan ta kashe shi da takaicinta gashi Aliyu be cin komai na maids, kuma tana fitowa ta gansu a waje a tsaitsaye harda namiji.......