Page 17

3.1K 233 1
                                    

Zuhraa❤❤
(The flower)

By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin




بسم الله الرحمن الرحيم


Page 17

Mintuna 30 ya isar dasu Gurin, don ma Aliyu ya gargad'i Abbas da kar yayi gudu da baffa, da a irin nasu tafiyar ne minti 20 ya kawo su..

Baffa yayi wa Abbas godiya, ze shige kenan Abbas yace "Alhji dama Oga ya bada sako a baka" ya ciro bandir din 1000 ya mika mishi baffa yace "A'a baza ayi hk ba ka mayar mishi da kudinshi"...

Abbas yace "Alhaji idan Oga yayi kyauta be son a maida mishi, wlh yanzu idan baka karba ba ni ze hukunta kayi hkr ka kar'ba plz"....

Baffa ya sa hannu ya kar'ba tare da mishi godiya ya shige gida, Abbas ya bud'e boot ya fara jidan kayan abinci yana ajiyewa a kasa se da ya sauke komai tukun ya kira yara a kofan wani gida ya basu 200 yace su shigar da kayan, shi kuma ya hau motar yaja da gudu, yasan in ya tsaya baffa ze maida mishi kayan ne, shi kuma yasan hukuncin da ze karba matukar ya koma da kayan....

Baffa yayi sallama ya shiga, hanse ce ta amsa mishi tare da fitowa tana cewa "malam sannu da dawowa" yace "yauwa ina yarannan" tace basu dawo daga boko ba" ze kara mgna kenan yaji sallama..

"Wa'alaikassalam ku karaso mana, wa ya aiko ku" yaran suka fara shigowa d'aya bayan d'aya suna ajiye kayan hannunsu, bud'e baki kawai baffa yayi yana kallonsu ya kasa magana...

Seda suka ajiye komai sun juya zasu tafi tukun yace "yara wa ya aiko ku? Ko de ba nan bane, me wayo cikin yaran ne yace "baffa wanda ya sauke ka a mota ne yace mu kawo"..

Da sauri baffa ya fita sede ko kurar motar be gani ba, Murmushi yayi yana mamakin yadda yaran Aliyu suke tsoronshi, dawowa yayi ya sallami yaran.

Yana kallon kayan buhun shinkafa kananan nan guda uku, buhun semovita biyu, spaghetti katon uku, indomie katon biyu, manyan gwangwanin madara da bonvita, macaroni katon biyu.

Adu'a yake yi ma Aliyu a zuciyar shi kafin ya d'aga ido ya kalli hanse da tunda aka fara shigo da kayan take murna, se ta'be ta'be takeyi, ta'ba wannan ta'ba wancan..

Daga baya ma rungume malam d'in tayi tana murna, duk da ba kowa a gurin amma tsakar gida suke, yara zasu iya shigowa ako wani lokaci, ture ta yayi daga jikinshi yana cewa "me haka hanse"..

Tace "malam ina ka samo wannan kayan haka? Eyyeh kace zamu ci dad'i wayyo Allah" wani takaici ne ya kama malam yace "amma banji kin tamabayi zuhra ba"..

Tace "ina ruwana da wata zuhra nasan ko ta shiga duniya, yanda uwarta tayi ta haifo ta" da sauri malam ya katse ta..

"Hanse ki kiyaye ni wlh, toh kayan nan daga wadda ya kad'e ta ne, tana babban asibiti a yola" 'bata fuska tayi tana kunkuni "ita ina ruwanta da zuhra in taga dama ta mutu, kaya de se sunci"..

Malam yace me kika ce? Tace "ba komai" girgiza kai yayi ya shige d'akinshi, ita kuma ta fara shigar da kayan tana murna...

%%%%%%%%%%%%%%

Ta bangaren Aliyu kuma yana ganin tafiyan baffa office din Ammie ya nufa shima zaid office d'inshi ya tafi...

"Salamu alaikum" ya tura kofan ya shiga, ta amsa mishi da "wa'alaikassalam Aljanin zuhra" dakatawa yayi, yayi pouting tare da kwa'be fuska ya shagwa'be fuska tare da cewa..

"Ammie...... Ammie dan Allah ki bari" dariya take tace "naki daga yau sunanka Aljanin zuhra" yace "plz, plz ammie na, kar wasu suji mana a raina ni" tana dariya tace "toh sarkin son girma na dena, baaba rahane tazo ne?"....

Yace "eh, zan je gida, se kin dawo" tace "baka isa ba nan kuma babana ka kad'e yarinya baza ka barmu da aiki ba, kaje ka d'an kara zama da ita se anjima ka tafi, da dare kuma ka dawo dasu Arfah su gaisheta"..

Had'e rai yayi, wai shi me gamin shi da yarinyar nan ne? Ya tambayi kanshi, da kyar ya bud'e baki yace "toh" tare da ficewa daga office din, da Murmushi tabi bayan shi tana girgiza kai....

Da sallama ya turo kofan aciki ciki ba wanda yaji, kawai ganin shi sukayi yaja kujera ya zauna ya fiddo wayanshi ya fara aikin dannawa...

"Sannu da shigowa Alhji karami" inji fad'an baaba rahane yace "yauwa" be ko kalli gefen zuhraa ba, ita ma a hankali tace "sannu" dagowa yayi suka had'a ido a tare gabansu yayi wani mummunan fad'uwa....

Tsaki yaja tare da maida kanshi ga wayarshi ya ci gaba da abunda yake yi, su kuma hirar su suka ci gaba dayi kasa kasa sbd baaba rahane tasan be son hayaniya....

Lallaba zuhra takeyi ta ci abinci ita kuma taki ci se drama suke, tsab yana jinsu dayake shi mutum ne mai kaifin ji, dga kai yayi ya d'an kallesu ya kau da kanshi...

Kaman bazeyi magana ba da ya ga musun su yaki karewa yace "baaba ajiye mata abincin" ta kuwa ajiye a gaban zuhran da se 'bata fuska take kaman zatayi kuka....

Ido kawai ya zuba mata yana mata kallo me kama da harara, ba se yayi magana ba ta san me yake nufi, kau da kai tayi tana cewa a zuciyar ta amma wannan mutumin ya iya hukunci da ido......

Kallon na firgitata yana kad'a mata 'yan hanji amma dan taurin kai irin na fulani da rashin sanin waye shi yasa ko kallon abincin batayi ba se ma kuka data fashe mishi da shi..

Wani uban tsawa ya daka mata da seda hanjin ta ya kad'a "will you shut up my friend, dauki abincin nan ki ci kafin na mike, don wlh in har kika bari na tashi toh se jikin ki ya gayamiki"...

Hannunta na rawa ta fara cin abincin da sauri sauri don ta tsorata sossai, seda ya ga ta gama cinye abincin tukun yaja tsaki tare da ficewa daga dakin....

Kuka ta sama baaba tana cewa ita gida take so bata son nan, da kyar baaba rahane ta shawo kanta tayi shiru tare da kwanciya, bata wani jima ba bacci ya dauke ta.

Yana fita be koma office din Ammie ba bare yabi ta kan zaid mota ya shiga, suka fice kaman masu tashi sama, gida suka nufa suna isa straight part d'inshi ya shige yayi wanka tare da alwala ya shirya cikin kananan kaya bakake wando da riga...

Ya fito da niyan shiga part din maami se aka kira sallah fasa shiga yayi ya juya akalarshi zuwa massallaci, ana idar da sallah ya fito yana tafiyar shi nan na kasaita yana tunani shi badon jikin maami dayake so a fara magani a idonshi ba da ya koma wurin aiki don ya gaji da zaman banza...

Yana cikin tunanin ne yaji an rike hannunshi, waiwayowa yayi se ya ga nasreen ce da uniform a jikinta alamun yanzu suka taso daga school tace "hamma ina ta magana ka yi shiru"..

Yace "yes angel me kika ce?" Da yake haka yake kiranta wani lokacin tace "hamma wannan xuwan naka baka kai mu shopping ba, yaushe zamu je...

Yace "ku shirya da yamma zamu je" tsalle tayi tare da cewa "thanks bro you are the best" ta fice da gudu zata je fad'awa Adda tasan zata bata tukuici sbd Aida na son zuwa shopping da Aliyu, duk irin abunda suka dauka ba ze ce a rage ba haka ze biya ba ruwanshi...

Da gudu ta shiga parlorn Ammie tana cewa "Adda Adda Adda" Aida tace "kayya irin wannan kira, se ka ce makahuwa, wai me?" Nasreen tace "Albishir".

Aida ta ta'be baki tare da cewa "goro" nasreen ta sake cewa "se fa kin bani tam" Aida ta hasala kaman zata make ta "nifa in baza ki fad'a ba zan haura sama, ina da abun yi"..

Arfa na zaune a gefe dama haurawa zatayi ta tsaya tana kallon dramar nasreen da aida, kullum aikinsu fad'a, nasreen neman tsokana, Aida kuma saurin hawa ga son girma..

Nasreen tace "hamma yace mu shirya we are going to shopping da yamma" wani irin ihu Aida tasa tare da tsalle tace "Lil sis gaskiya kin cancanci goro da wannan Albishir, kice gobe akwai iyayi a school"

Murmushi arfa tayi tare da hayewa sama ita ma taji dadin labarin don tana son abubuwa dyawa.



#vote
#share
#comment




























'Yar mutan Adamawa

Zuhraa❤❤Donde viven las historias. Descúbrelo ahora