Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 50
A hankali yake dawowa cikin hayyacinshi amma sam be bud'e ido ba sama sama ya fara jin hayaniya a d'akin hira ake da harshen larabci, hakan ya tabbatar mishi da 'yan uwan mahaifiyarshi ne, a hankali ya fara tuna me ya faru dashi last moment d'insu ya tuna yana rike da ita kuma an har'be ta har ta suma ko mutuwa ne ma?..........
A matukar firgice ya mike zaune yana kiran "fateemah" da ita suka fara had'a ido a hankali kuma ya sulale ya kwanta tare da lumshe ido, yana sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciya da numfashi tare da mamakin me ya sa be ganta a kwance ba gashi kaman lafiyanta klau amma kallo d'aya da ya mata ya fahimci ta rame sossai........
Da sauri su Ammie sukayi kanshi dama Abbie da zaid basa d'akin, goshinshi ta dafe tana cewa "son are yhu okey?" A hankali ya bud'e idonshi da ya fad'a sossai yace "am fyn mother" murmushi tayi mishi 'yan d'akin suka fara mishi sannu yana amsawa a hankali yaya Aasim da suke cewa uncle Aasim yace.........
"Lallai son ka cika me karfin zuciya ya naga ka tashi garau kai da aka cire hope a kanka?" Shiru yayi kakanshi ummi tace "hmmm kaji min d'an renin wayo wato a gadon asibitin ma se kayi wa mutane miskilanci nikam Allah ya had'a ni da gamo na, bayan na gama da kakanka, na dawo kan Aadil se kuma kai.......
Mtseww Allah ka taimake ni kar 'ya'yanka su gada don ban san ya zanyi ba" ta karasa maganan da dafe kunci tare da fuskan tausayi dariya 'yan d'akin suka saka kallonsu take yi ita a ganinta bata ga abun dariya ba, kallon Ammie Aliyu yayi da ido ya mata alaman abunda yake so........
Har ta mike idonta ya fad'i akan zuhraa da tayi shiru tana kallon guri d'aya da alama tunani take yi se taji zuhraan ta bata tausayi haka kawai komawa tayi ta zauna tace "daughter tashi ki d'auko abunda mijinki ze wanke bakinshi don yanzu ba iya tafiya ze yi ba", mikewa tayi ba tare da tace komai ba ta shiga toilet d'in ta samo abu ta fito.......
Gurinshi ta nufa a hankali cikin natsuwa da taka tsan tsan ya mike zaune don ba karamin ciwo yake ji a jikinshi ba dauriya ce kawai da sauri Ammie ta sa pillow a bayanshi ya jingina, had'a ido sukayi da uncle Aadil shi be zata ma yana d'akin ba don duk abunda ake yin nan be ji muryanshi ba.....
Murmushi suka sakar wa juna da alamomi kala kala da su kawai suka san me ke nufi, sossai suka shaku da uncle Aadil ba wai suna hira bane a'a kawai in suka had'u haka zasuyi ta zman kurame se alamomi da su kad'ai suka san me suke cewa, brush zuhraan ta mika mishi da marcline a jiki kar'ba yayi ba tare da ya kalle ta ba........
Bayan ya gama brush d'in ne ya mika mata silvern kar'ba tayi ta shige toilet, kafin ta fito Ammie ta sa mishi abinci mikawa zuhraa plate d'in Ammie tayi a kunyace ta kar'ba ta zauna bakin gadon ta fara bashi a baki duk da ze iya ci da kanshi, har ta gama bashi magana be had'a su ba ita ta d'auka rashin mishi magana ne yasa shima be mata ba......
A hankali yadda ba me ji tace "ya jiki?" Shiru yayi kaman be jita ba bayan sarai ya ji ta sake maimaitawa tayi nan ma shiru yayi ranta ne ya 'baci hararanshi tayi charab a idonshi had'e rai yayi ita ma ta had'e gabas da yamma kamar yadda yayi.......
Dariya ma ta bashi amma be yi ba se satar kallonta yake yi mikewa tayi ta koma gefe tayi zamanta murmushi yayi a dai-dai lokacin da su zaid da Abbie suka shigo farin ciki ne fal a fuskansu ganin Aliyu a zaune da sauri zaid ya karasa ya rungume Aliyun farin ciki fal kaman yayi rawa.....
Murmushi Aliyu yayi tare da buga bayanshi kad'an sukayi breaking hug d'in, murmushi ya ma Abbie shima ya mayar mishi tare da mishi sannu da jiki, Ammie tace "se kayi wanka ko?" Da ido ya mata alamun tazo matsawa kusa da shi tayi a hankali yace "what happen to me?" Ita ma cikin kasa da murya ta bashi labarin abunda ya faru........